Wannan kashi na shida kenan cikin fadakarwar da muka faro a makon jiya kan hanyoyin da mai karatu zai iya kwarewa a fannin kimiyya da fasahar sadarwa na zamani. A yau mun dubi fannin "Web Design and Maintenance" ne.
Wannan mako za mu leko gidan yanar sadarwa na Gumel.com ne, wanda Malam Salisu Hashim Gumel ya dauki nauyin ginawa da tafiyar dashi. A sha karatu lafiya.
Daga wannan mako za mu fara kai ziyara ne zuwa wasu gidajen yanar sadarwa na harshen Hausa, don baiwa masu karatu daman ganin yadda suke, da irin tsarin dake cikinsu, da kuma fa'idar dake tattare da ire-iren wadannan shafuka.
Kamar yadda nayi alƙawari makon da ya gabata, yau ga ni ɗauke da bayani kan Gina Gidan Yanar Sadarwa. Sai dai wani hanzari ba gudu ba. . .masu karatu za su ji dandanon wannan ƙasida ta canza, sabanin yadda aka saba jin bayani…