Za a Samar da Intanet a Duniyar Wata

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 29 ga watan Oktoba, 2021.

798

Shekaru kusan 50 kenan da dan adam ya fara taka kafarsa a duniyar wata, sadda mahaya Kumbon Apoll 11 suka ziyarci duniyar.  Daga wancan lokaci zuwa yanzu dai an samu ci gaba a fannin kimiyyar sararin samaniya da dama.  Wannan yasa a halin yanzu hukumar binciken sararin samaniya ta kasar Amurka, wato NASA, ta kuduri aniyar sake komawa duniyar wata a shekarar 2024.  Sai dai a wannan karon, ziyarar za ta sha bamban da ziyarar farko.  A karon farko mace za ta kasance cikin tawagar.  Sannan za a hada da bakin fata, cikin masu tafiya.  Bayan dukkan wannan, za a samar da Intanet mai zaman kansa, wanda zai dace da yanayin wancan mahalli, don taimakawa wajen sawwake sadarwa tsakanin maziyarta.

Wannan nau’in Intanet da za a samar a duniyar wata dai an kira shi da suna: “LunaNet”, wanda ke nufin nau’in Intanet din da ya dace da sararin samaniya.  Wannan shi ne abin da shafin Autoevolution ya tabbatar, daga hukumar NASA dake kasar Amurka.  Wannan nau’in Intanet mai suna “LunaNet” dai zai taimaka wajen hada alakar sadarwa tsakanin masu lura da cibiyar tauraron dan adam ne a wannan duniyar tamu, da wadanda ke can duniyar wata a cikin kumbo.

Wannan shiri na samar da Intanet a duniyar wata dai ya faro ne tun shekarar 2019, daga cibiyar binciken NASA dake Goddard (Goddard Space Flight Center), a jihar Maryland ta kasar Amurka.  Asalin manufar shirin dai shi ne samar da tsarin sadarwa tsakanin kananan taurarin dan adam dake shawagi a harabar wata dake sararin samaniya.  Sabanin tsarin Intanet irin wanda muke amfani dashi, wanda kana iya aika sako amma ya kasa isa inda aka aika saboda matsalar yanayin sadarwa, LunaNet na dauke ne da wani tsari mai suna: “Delay/Disruption Tolerant Networking”, wato: “DTN” a gajarce.  Aikin wannan tsari shi ne, duk sakon da aka aika sai ya isa adireshin da aka aike shi.  Idan ma ya samu matsala a hanyarsa, tsarin na iya taskance shi, yaci gaba da neman hanya ingantacciya mara matsala. Da zarar ya samu sai ya saki sakon, har ya isa inda ake shi.

Bayan haka, wannan nau’in Intanet zai rika taimaka wa masu shawagi a duniyar wata wajen gano bigiren da suke a taswirar duniya, tare da samun hanyar mafi sauki wajen zirga-zirga a mahallin da suke.  Hakan kuwa zai yiwu ne ta hanyar siginar sadarwa da tsarin zai rika aika musu a iya kadadar sadarwa da suke.

- Adv -

Daga cikin siffofin LunaNet har wa yau, tsarin zai rika amfani da hanyar karban siginar yanayi a sararin samaniya wajen sanar da masu shawagi a duniyar wata duk wani abu mai hadari dake tafe ko yake kusa dasu, musamman tastsatsin yular wuta dake fetsowa lokaci-lokaci daga jikin rana, ko harshen tururin wuta dake yawo a sararin samaniya.  Sannan akwai tsarin nemowa da ceton wanda ya fada cikin wani hadari, wato: “Search and rescue.”

Bayan haka, abu na karshe mai kayatarwa game da LunaNet shi ne, an gina masa tsarin nemo sigina mai dauke da bayanan wasu duniyoyi dake makwabtaka da duniyarmu, musamman duniyoyin dake nesa damu ainun.  Wannan tsari, a cewar masana, zai baiwa malaman sararin samaniya aiwatar da bincike a aikace, don gwajin ka’idojin kimiyyar sararin samaniya da aka dade da rubuta su a nazarce.  Kuma sakamakon da za a samu zai taimaka matuka wajen kara gano yadda tsarin halittar duniyar take ne gaba daya ma, ba wannan duniyar tamu ba kadai.

Sai dai, wannan nau’i na Intanet da ake kan ginawa, ba irin wanda muke amfani dashi bane a wannan duniya tamu, wanda zaka hau shafin Google, ko Youtube ko Facebook.  A a, yanayi ne na sadarwa dake bai wa na’urorin sadarwar dake mahallin da suke damar ganin juna, da sanin bigiren da kowanne yake, ta hanyar shafi na musamman da tsarin zai samar.  Kuma idan ba a mance ba, a makalar farko da aka fara bugawa a wannan shafi mai albarka, na mana bayanin ma’anar Intanet da cewa, tsari dake “baiwa kwamfutoci da sauran na’urorin sadarwa damar Magana da juna wajen aikawa da karbar sakonni a iya zango ko kadadar sadarwa na musamman.”  Ka’idar dake taimaka wa kwamfutoci aiwatar da irin wannan nau’i na sadarwa dai ita ce ginanniyar ka’idar sadarwa mai suna: “Internet Protocol” (IP).  Wanda ke amfani da adireshin kowace kwamfuta ko na’urar sadarwa a tsarin lambobi, don aiwatar da sadarwa a tsakaninsu.

Irin wannan tsari na sadarwa shi ne LunaNet ke amfani dashi don taimaka wa masu shawagi a duniyar wata.  Ana kuma sa ran fara amfani da shi a shekarar 2024, sadda hukumar NASA za ta koma duniyar wata dauke da mahaya na musamman.

- Adv -

You might also like
2 Comments
  1. Muhammad sambo Usman says

    Gaskiya inajin dadin wannan shafi sosai matuka.Muna godiya

    1. Baban Sadik says

      Mun ji dadin ganin ka samu gamsuwa da rubuce-rubucenmu. Muna godiya matuka.

Leave A Reply

Your email address will not be published.