Wuraren da Za a Fara Kaddamar da e-Naira (4)

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 22 ga watan Oktoba, 2021.

923

Wannan shi ne kashi na karshe a jerin makalolinmu kan e-Naira.

——————–

Me Yasa Aka Dage Ranar Kaddamar da e-Naira?

Asali dai bankin CBN ya tsara matakai hudu ne mahimmai, wadanda da zarar an gama su za a kaddaramar, kamar yadda sanarwa ta gabata a baya.  Matakin farko shi ne yin nazari mai zurfi kan yadda tsarin zai gudana daga tunani har zuwa samarwa, ta la’akari da tsarin kasarmu, da kuma tsarawa tare da zana nau’in kudin na e-Naira da irin manhaja ko magudar da za ayi amfani dashi.  Mataki na biyu kuma ya kunshi kintsa nau’in kudin ne don dacewar da manufar da ta sa aka kirkiro tsarin.  Sai mataki na uku da ya kunshi horas da ma’aikatan da za su tafiyar da tsarin – tsakanin ma’aikatan babban bankin da kuma bankunan kasuwa, da wayar da kan jama’a kan dangane da dukkan abin da ya shafi sabon tsarin.  Sai mataki na karshe, wanda shi ne kaddamar da wannan nau’in kudi, wanda a farko bankin CBN ya sanar da ranar 1 ga watan Oktoba ne, don dacewa da bikin murnar samun ‘yancin kasa a karo na 61.  To amma, ‘yan sa’o’i kafin wayewar gari sai ya dage wannan biki na kaddamarwa.

Dalilin hakan na dauke ne cikin sanarwar da bankin ya fitar, cewa, bayan sakin shafin yanar sadarwa na e-Naira (e-Naira Website) da bankin yayi a ranar, cikin sa’o’i shida an samu mutane kusan miliyan biyu da suka ziyarceshi, nan take.  Wannan yasa shafin ya fara saibi; alamar cewa jama’a sun masa yawa.  Bayyanar hakan matsala ce, domin idan a farkon lamari an fara samun hakan, to, me zai faru idan tsarin ya game kasa?  Wannan yasa aka dage bikin, don kara inganta wannan shafi da dukkan tsare-tsaren dake dauke dashi, don samun sakamako mai inganci a gaba.

Don tabbatar da cin nasarar wannan tsari gaba dayansa, bankin CBN ya kebance ma’aikata sama da saba’in a wani mahalli a babbar birnin tarayya, Abuja, inda suke aiki dare da rana safe da yamma, don tabbatar da cewa komai ya gudana yadda aka tsara.  Kuma da zarar y agama kintsawa, zai sanar da ranar da za a kaddaramar da wannan tsari in Allah Ya yarda.

Da Wasu Jihohi ko Bangaren Najeriya Za a Fara Wannan Tsari?

- Adv -

Kamar kowane tsari mai gamewar tasiri, akan zabi wurare ne na musamman don fara kaddamar dashi a matsayin gwaji.  Daga baya kuma, bayan la’akari da nasara ko kalubalen da aka samu marhalar gwaji, sai a kaddamar da tsarin a kasa baki daya.  Dangane da sabon tsarin e-Naira, bankin CBN zai fara gudanar da tsarin ne a manyan birane hudu dake jihohi hudu a kasar nan.  Wadannan birane dai su ne: birnin Legas, dake Jihar Legas.  Da birnin Kano, dake Kanon Dabo.  Sai birnin Fatakwal dake jihar Rivers.  Sai birni na karshe, wato babban birnin tarayya, Abuja kenan.  Daga baya tsarin zai game kasar baki daya, in Allah Yaso.

Su Waye Masu Ruwa da Tsaki Cikin Lamarin Ne?

Masu ruwa da tsaki, wadanda dasu ne tsarin zai gudana dai su biyar ne.  Bangaren farko shi ne babban bankin Najeriya, wato “Central Bank of Nigeria” ko CBN a gajarce.  Shi ne wanda ya kirkiri tsarin, kuma zai buga nau’in kudin, ya samar da hanyar yada shi, da kuma tantance wadanda zasu gudanar da hada-hadarsa a kasa.  Kuma shi ne har wa yau wanda hako, ya adana, ya kuma lura da rayuwar e-Naira.  Shi ne ya gina manhajar da za a rika amfani da ita wajen aiwatar da dukkan wadancan tsare-tsare, wanda ya kira: “CBN Digital Currency Management System” ko .  A karshe, shi ne wanda zai baiwa bankunan kasuwanci daman bude wa kwastomominsu taskar e-Naira Wallet, bayan ya bude musu nasu a bangarensa.

Bangare na biyu su ne bankunan kasuwanci, wato: “Commercial Banks”.  Su ne wadanda zasu taimaka wa sauran mutane dake da ajiya dasu wajen bude taskar e-Naira Wallet, kuma su ne zasu mika bukatar neman e-Naira ga CBN a madadin masu ajiya dasu, sannan su sake basu damar iya aika kudi daga taskar ajiyarsu ta banki zuwa taskarsu ta e-Naira.  Bayan haka, yana ckin aikinsu lura da adadin kudin e-Naira dake taskarsu a wasu rassan jihohi, da tantance masu aiwatar da hada-hadar kudi ta hanyarsu da dai sauran tsare-tsare.

Bangare na uku su ne hukumomin gwamnati, daga fedara zuwa kananan hukumomi; musamman wadanda suke da taskar ajiya a babban bankin Najeriya ta hanyar gamamman taskar TSA.  Su ma CBN zai basu damar iya karba da kuma aika e-Naira tsakaninsu da juna, da kuma tsakaninsu da sauran kamfanoni ko daidaikun mutane.

Sai bangare na hudu, wato kamfanoni da masana’antu da masu aiwatar da kasuwanci.  A tsarin e-Naira ya zuwa yanzu babu nau’in “Corporate Account”, wato nau’in taskar ajiya na kamfanoni da masana’antu, kamar yadda ake dashi a tsarin banki na Zahiri.  Su ma dama ce za a basu don bude taskar e-Naira, tare da hanyoyin karba da aikawa wanda babu caji a tattare dashi.  Daga cikin hanyoyin akwai amfani da na’urar POS, da hanyar karbar kudade ta amfani da hanyoyin sadarwa na zamani.

Bangaren karshe su ne daidaikun mutane, masu taskar ajiya a banki da wadanda ba su da taskar ajiya.  Wadanda ke da taskar ajiya a banki cikin sauki za su iya bude taskar e-Naira Wallet ta taimakon bankinsu.  Marasa taskar ajiya a banki kuma suna iya amfani da wayarsu ta salula, da layin da suka yi rajistan katin zama dan kasa, wato: “National Identity Number” ko “NIN” a gajarce, wajen tantance kansu.

- Adv -

You might also like
6 Comments
    1. Baban Sadik says

      Mun gode.

  1. Salisu Yusuf Abdullahi says

    Jazakallahu khairan baban Sadiq sannu da kokari

    1. Baban Sadik says

      Yauwa barka dai. Mun gode sosai.

      1. MUHAMMAD HAMZA says

        Good morning Baban Sadiq, a prolific writer. I have gone through your write ups on enaira. It is highly informative, enlightened and sensitizing. May Allah out of His infinite bounties increase you in beneficial knowledge

        1. Baban Sadik says

          Morning. Thanks hearing that. And thank you for the prayers.

Leave A Reply

Your email address will not be published.