Tsarin Fasahar Faifan DVD (3)

Kashi na 3 cikin jerin kasidun dake bincike kan tsarin fasahar faifan DVD. A sha karatu lafiya.

290

Na’urar Sarrafa Faifan DVD

Faifan DVD da CD, da ma na garmaho da bayanansu suka gabata a makonnin baya, suna xauke ne da rubutattun bayanai ko sauti ko hotuna daskararru (Still Images), ko kuma hotuna masu motsi, wato bidiyo kenan.  Waxannan bayanan dai ba a iya ganinsu sai an tsofa faifan a cikin wata na’ura wacce ke sarrafa su don su bayyana ga mai kallo ko mu’amala dasu ya gansu, ko samu damar yin mu’amala dasu.  Na’urar dake da alhakin sarrafawa tare da bayyana waxannan bayanai na CD da DVD dai ita ake kira: “CD Player” idan na faifan DVD ce, ko kuma “DVD Player”, idan na faifan DVD ce.  Kowanne daga cikin waxannan aikinsa daban, duk da cewa na’urar CD Player aka fara qirqira a farko.

Kafin nan, yana da kyau mai karatu ya fahimci cewa ita fasahar Faifan DVD, kamar yadda qasidar makon jiya da na shekaranjiya suka tabbatar, mizaninta ya xara na fasahar faifan CD wajen girma da armashi, da kuma yalwa wajen sarrafa bayanai.  Kowane faifan DVD na taskance bayanai ne a wasu ramuka ko kogo dake fuskar faifan, qanana, waxanda na’urar sarrafa faifan ne ce kaxai ke iya hanga da riskar abin da ke xauke cikinsu.  Waxannan ramuka ko kogo su ake kira: “Tracks” a harshen fasahar sadarwa na zamani.  Fuskar faifan DVD na xauke da waxannan ramuka ne masu ximbin yawa, iya gwargwadon girma da mizanin faifan.  Kowane rami ko kogo daga cikin waxannan ramuka na iya xaukan bayanai miliyan biyu ne da dubu xari huxu da goma sha takwas, wato: 2,418 bytes, ko 2.4MB kenan.  Da zarar wannan rami ko kogo ya toshe sanadiyyar qura ko datti ko wani karta da ya samu faifan, to, na’urar ba ta iya sarrafa bayanan dake wannan kogo.  Shi yasa za ka hotuna ko sautin na kakkaryewa, ba ya bayyana daidai, wato: “Cracking” kenan.

A jumlace dai, an qirqiri na’urar sarrafa faifan CD da DVD nau’i biyu ne, kuma kowanne daga cikin waxannan nau’uka na da wasu na’uka da na musamman da ake amfani dasu ta wasu na’urorin sadarwa daban.  Ga taqaitaccen bayani nan kan kowanne daga cikinsu.

- Adv -

Na’urar CD Player

Ta farko daga cikin nau’ukan na’urar dake sarrafa waxannan fasahohi dai ita ce ake kira: “CD Player”.  Wannan na’ura ce aka qirqira tun farkon bayyanar fasahar CD, don sarrafawa da kuma bayyana bayanan dake xauke cikin faifan, ga masu amfani dashi.   Na’urar CD Player na’ura ce ta musamman da aka qera, wato: “Standalone Device”, kuma ake sayarwa ga masu buqatar mu’amala da faifan CD a wancan lokaci.  Kuma kamfanoni da dama sun qera wannan na’urar, musamman kamfanonin dake da ruwa da tsaki wajen samar da asalin fasahar CD xin, irin su: Toshiba, da Sony, da Philips da ma wasu kamfanoni da suka shiga harkar daga baya.

Na’urar sarrafa faifan CD dai ta kasu kashi-kashi, ta la’akari da inda ake amfani da ita.  Kamar yadda bayani ya gabata a sama, ta farko ita ce wacce aka qera mai zaman kanta, wacce za ka je kasuwa ka saya, don amfani da ita kai tsaye a jikin talabijin xinka.  Sai nau’i na biyu wacce ke zuwa a jikin kwamfuta.  Wannan ita ake kira: “CD ROM”.  Ita kam ko ka saya, muddin ba a kwamfuta ka sanya ba, ba ka iya amfani da ita.  A taqaice dai, ta kevanci kwamfuta ce kaxai.  Akwai kafa ta musamman da aka tanada a jikin kwamfuta, wanda a nan ake tsofa ta.  Wannan nau’i na na’urar CD dai ta sha bamban da ta asalin, domin fasaharta daban yake.  Bayan nuna bidiyo da sarrafa sauti, na’urar CD ROM tana iya sarrafa hotuna, da rubutattun bayanai, da kuma manhajar kwamfuta.  Amma na’urar CD da za ka iya saya a kasuwa ka jona da talabijin gidanka ba ta iya sarrafa faifan CD mai xauke da rubutattun bayanai ko manhajar kwamfuta.

Sai nau’in na’urar CD dake zuwa a jikin mota, shi ma dai kamar na asalin na’urar CD ne; tana iya sarrafa sauti ne da bidiyo, amma ba ta iya sarrafa faifan CD mai xauke da rubutattun bayanai ko manhajar kwamfuta.  Wannan na’ura dai an girka ta ne a jikin motocin da aka qera a lokacin da wannan fasaha na faifan CD ke yayi.  Don haka, ko da ka je kasuwa ka sayo, idan ba a mota ka xora ba, ba a iya amfani da ita a talabijin.

Sai nau’in na’urar CD na qarshe wacce ita ma mai zaman kanta ce, amma ta sha bamban da asalin na’urar da aka fara qerawa.  Wannan na’urar dai tana xauke ne da mahallin xora faifan CD, da kuma wasu ‘yan qare-qare masu qayatarwa, irin su rediyo da sauransu.  Duk da cewa bata shahara ba sosai a wannan vangaren qasashen namu, amma tana cikin jerin nau’ukan na’urar da suka shahara a qasashen turai da amurka.  Kuma ita ake kira: “Portable CD Player”.  Kamfanoni da yawa sun qera wannan nau’i na na’urar CD sosai, kuma har yanzu ana amfani dasu.  Ba su da girma sosai; kana iya sanya su cikin jaka, kuma suna xauke da talabijin dinsu (Display Screen), wanda hakan ke nufin ba ka buqatar talabijin don amfani dasu.  Sai dai su ma, kamar nau’in na’urar CD na mota ne, sauti da bidiyo kaxai suke iya sarrafawa, ban da rubutattun bayanai da manhajar kwamfuta.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.