Ku Inganta Mana Makarantunmu Na Kimiyya da Kere-Kere (1)

A yau zamu fara duba yadda tsarin ilimi yake a Najeriya, da tasirinsa ko rashin tasirinsa wajen ciyar da al’umma gaba a kimiyyance. Wannan ci gaba ne a jerin kasidun da muka faro a baya. Na farko mai taken: “Ciyar da Najeriya Gaba a Fannin Kimiyya da Kere-kere.” Na biyun kuma: “Hanyoyin Ciyar da Al’umma gaba a Kimiyyance.” A sha karatu lafiya.

261

Mabudin Kunnuwa

Cikin makon da ya gabata ne hukumar JAMB ta gudanar da jarabawar shiga makarantun gaba da sakandare, inda dalibai miliyan daya da dubu dari bakwai suka rubuta wannan jarabawa.  Daidai wannan lokaci, manema labaru sun tattauna da Ministan Ilimi ta kasa Hajiya Rukayyatu Rafa’i, inda ta musu bayanin kalubale da hukumar ke fuskanta a kokarinta na inganta ilimi a kasar nan.  Daga cikin kalubalen da ke fuskantar ilimin gaba da sakandare a kasar nan, a cewar Ministan, akwai karancin jami’o’i.  Tace daga cikin mutum miliyan daya da dubu dari bakwai da suka rubuta wannan jarabawa ta JAMB, mutum dubu dari biyar da ashirin ne kacal suke da gurbi a makarantun!  Tirkashi! Duk da cewa ba dukkan masu wannan jarabawa bane suka fito daga sakandare cikin shekarar da ta gabata, amma galibinsu duk yayayyun daliban sakandare ne masu neman ci gaba.  Don haka, idan mutum dubu dari biyar da ashirin ne kacal suke da gurbin karatu cikin miliyan daya da dubu dari bakwai, sauran kuma ina za su nufa?

Tare da haka, daga cikin abin da suke yi da sunan inganta ilimi a jihohinmu musamman na arewa, Gwamnoninmu na can suna ta kara gina makarantun sakandare da firamare, ba tare da la’akarin halin da ingancin ilimi ke ciki ba.  A wasu jihohin Arewa har yanzu akwai malaman da ba a biya su albashi ba na tsawon watanni uku zuwa hudu.  A jihar da wannan lamari ya shafa, Gwamnati ta gina makarantun firamare da sakandare da dama.  Ban sani ba ko yawan makarantu shi ne kadai hanyar inganta ilimi a kasarmu.  Shin, ina makarantunmu na kimiyya da kere-kere (Science Secondary Schools), ina makarantunmu na koyon sana’o’i (Vocational Schools/Technical Colleges)?  Ashe ba su ne suka kamaci a dada inganta su ba?  Ba su ne suka kamaci a dada yawaita su ba?  Cikin kashi 100, kashi 90 na masu aikin hannu, ko sana’ar hannu (walda, da kanikancin motoci da babura, da aikin lantarki, da aikin gine-gine, da fasahar kere-kere) duk a kan titi suka koya.  Hakan ya faru ne saboda karancin ingancin karatu a makarantunmu, da karancin su kansu makarantun na sakandare, sannan da sauran matsaloli da suka shafi tsarin tafiyar da ilimi a kasar baki daya.

A yau za mu dubi halin da makarantunmu na sakandare suke ciki ne. Da babbar manufar kafa makarantun sakandare, sannan mu duba mu gani; shin, an cin ma wannan buri kuwa a Najeriya, musamman a fannin samar da kimiyya da kere-kere da sana’a?  Domin wannan shi ne damuwarmu a wannan shafi.  Sai dai kafin wannan, za mu yi tsokaci takaitacce kan halin da makarantunmu na sakandare ke ciki, musamman wajen samar da ingantaccen ilimi kan kimiyya da kere-kere da kuma sana’ar hannu.

Kafin Mu Kara Yawan Jami’o’i

Kafin amsa kiran babban Ministan Ilimi wato Hajiya Rukayyatu Rufa’i wajen kara yawan jami’o’i don samun gurabun karatu a makarantun gaba da sakandare, zai dace Gwamnatin tarayya tayi dogon nazari kan halin da makarantun sakandare suke ciki, musamman wajen cinma manufar babban kundin tsarin ilimi na kasa, wato National Policy on Education.  Ga duk wanda ke zaune a wannan kasa ya san halin da makarantunmu ke ciki, musamman na sakandare. Wadannan makarantu suna cike ne da matsaloli, kuma galibinsu a rikice suke, ta kowane fanni.  Wanda kuma na san duk mun yarda cewa sai da ingantattun sakandare ilimi zai ci gaba a kasar nan.

Daga cikin manyan matsalolin da ke addabar makarantunmu na sakandare akwai rashin isasshen kudin tafiyar da ayyuka, da samar da kayayyakin da za su taimaka wajen inganta ilimi.  Kamar yadda rahoton babban bankin Najeriya (CBN) ya nuna: tun daga shekara ta 2000 zuwa 2010, kason da Gwamnatin Tarayya ke baiwa bangaren ilimi bai shige kashi 14 cikin dari ba.  Wannan kaso bai taka kara ba balle ya karya. Domin kason da kasashe irin su Kenya, da Malawi, da Bostwana, da Angola, da Seraliyon, da Afirka ta Kudu ke baiwa ilimi ya shige namu, nesa ba kusa ba.  Wannan mitsitsin kaso da gwamnati ke baiwa ilimi bai yi la’akari da yawan daliban da ke makarantu ba, balle kokarin tabbatar da ingancin da ake bukata wajen samar da sana’o’in hannu da inganta fannin kimiyya.  Tare da haka ma, kaso ne da ya shafi bangarori uku; makarantun firamare, da makarantun sakandare, sannan da jami’o’i ko makarantun gaba da sakandare.

- Adv -

Matsala ta biyu da makarantunmu na sakandare ke fuskanta shi ne karancin kayayyakin aiki, da karancin azuzuwa, da karancin littattafai ko ma rashinsu, da karancin ingantattun malamai, ko ince kwararru, sannan da uwa uba, karancin dakunan bincike da gwaje-gwajen kimiyya da ayyukan hannu (Science and Technical Laboratories).  Ba wannan kadai ba, akwai makarantu yanzu haka a kasar nan, daliban a kasa suke zama, wasu kuma a gindin bishiyoyi ake karatun.  Duk wannan na faruwa ne a yanzu, cikin karni na ashirin da daya.

Daga cikin manyan matsalolinmu akwai rashin kwararrun malamai, sannan wadanda ake dasu ma dai lallabawa ake yi. Akwai masu kokari matuka, wadanda suka sadaukar da kansu wajen tarbiyyantar da dalibai, tare da basu ilimi mai nagarta, sannan akwai ‘yan dagaji masu shiririta. Babbar matsalar ita ce, ba kasafai ake samun kyakkyawar lura da malamai ba musamman na sakandarare.  A ka’idar karantarwa na zamani, kowane malami bai kamata daliban da zai karantar su wuce talatin zuwa talatin da biyar ba a aji.  Sadda nake sakandare shekaru 17 da suka gabata, a makarantarmu (wadda makaranta ce ta gwamnati a Abuja) kowane aji dalibai talatin da biyar ne zuwa arba’in.  Amma a yanzu kowa ya san ba haka lamarin yake ba. A sharhin bayan labaru na tashar Rediyon Tarayya (Radio Nigeria Network News) cikin makon da ya gabata, inda sharhin yayi tsokaci kan matsalolin ilimi musamman a makarantun sakandare a Najeriya, kididdiga ya nuna cewa, maimakon kowane malami a takaita shi ga dalibai talatin da biyar a aji (1:35) kamar yadda tsarin karantarwa ya nuna, a Najeriya yanzu kowane malami na daukan dalibai dari da hamsin ne (1:150). Dankari!

A cikin rahoton hukumar Ilimi na kasa na shekarar 2009 ma wannan matsala ta bayyana, wato karancin malamai ingantattu.  Haka ma Obanya ya hakaito cikin binciken da Wasagu ya gudanar (2006), sadda yake gudanar da bincike kan halin da makarantun sakandare na kasa suke ciki.  Bincikensa ya gano cewa: akwai karancin malamai ingantattu a manyan jihohin kasar nan hudu – jihar Legas, da Inugu, da Kaduna, da kuma Ribas. Yace wannan karancin malamai ya shafi dukkan fannonin ilimin da ake karantarwa, musamman bangaren addini da kasuwanci (Religious Studies & Commerce).  Binciken ya sake nuna cewa babu isassun malamai kwararru kan harsunan gida (Hausa, da Yarbanci, da yaren Ibo).  Wannan yasa a yanzu za ka ga dalibin sakandare, ko ma wanda ya gama sakandare, ba ya sha’awar harshen Hausa.  Idan kace ya rubuta maka wasika da harshen Hausa sai ka sha mamaki.  Ka’idojin rubutu na shan wahala a wajensu.  Sai kadan daga cikinsu.  Sakamakon wannan bincike har wa yau ya nuna cewa fannonin ilimin da suka fi kowanne karancin kwararrun malamai a makarantunmu na sakandare su ne fannin Lissafi (Mathematics) da fannin koyon sana’o’in hannu (Vocational Studies). Sannan, bincike ya nuna a karshe, jihar Legas ta fi kowace jiha karancin malamai a fannonin karatun sakandare.

A wani bincike na musamman da Ndefo ya gudanar (2006), matsalar karancin kwararrun malamai a makarantunmu ta dada fitowa fili karara.  A nasa binciken, sakamako ya nuna cewa kashi 36.8 daga cikin dari na malaman sakandaren kasan nan ne kwararru a fannin Ingilishi.  A fannin lissafi kuma ya gano cewa kashi 27.4 kacal ne kwararru. Duk sauran ‘yan abi yarima a sha kidi ne.  A bangaren fannin kimiyya kuma, ya gano cewa kashi 32.4 ne kwararru masu karantar da ilimin Fiziya (Physics), a yayin da aka samu kashi 40.4 kwararru a fannin kimiyyar sinadarai (Chemistry).  Sauran dai ana lallabawa ne.

Daga cikin manyan matsalolin da ke dakushe ilimi a matakin sakandare, akwai matsalar halin ko-in-kula daga malamai.  Da zuwa aji latti, ko ma rashin zuwa gaba daya, da taimakawa wajen magudin jarabawa, da kuma mummunar alaka da dalibai mata.  Wannan na cikin sakamakon binciken da Adeyemi da Ige suka gudanar (2002).  Wadannan matsaloli a fili suke, musamman dai abin da ya shafi taimaka wa dalibai wajen magudin jarabawa; kafin jarabawar ne, ko sadda ake yi, ko kuma bayan an gama. Magudin jarabawa na cikin manyan matsalolin da ke dakushe ingancin ilimi a matakin sakandare.  Jaridar Daily Sun ta ranar 29 ga watan Agusta, 2006 ta tabbatar da cewa, tsakanin shekarar 1995 zuwa 2006, dalibai sama da miliyan 14.4 ne suka rubuta jarabawar kammala matakin sakandare (SSCE).  Daga cikin wannan adadi, hukumar WAEC ta gano cewa dalibai miliyan daya da dubu dari uku da sittin da bakwai da dari bakwai da ashirin da shida sun tafka magudi a jarabawar da suka rubuta.

Shekara guda bayan wannan rahoto (2007) kuma sai ga labarai cewa babban Ministan Ilimi ya soke makarantu 324, an rufe su, duk sanadiyyar magudin jarabawa.  Abin da ke faruwa kuwa shi ne, akwai galibin makarantun da hukumar makarantar ce da kanta ke taimaka wa dalibai wajen magudi, bayan an hada kudade don wannan hidima.  A wasu lokuta kuma malaman ne ke rufe tagogin azuzuwa, su baiwa dalibai amsa, bayan an gansu.  A wasu lokuta mafiya muni kuma, wasu ne ke zuwa su rubuta wa wasu jarabawa.  Kai, abin ya kai a yanzu ma wasu babu maganar jarabawa, sai dai a yi “hannu kasa” don samun shedar jarabawa.  Duk wannan na faruwa karara a kasarmu.  Ta yaya ilimi zai yi inganci a matakin sakandare?

Bayan matsalar kwararru da isassun malamai, akwai matsalar rashin ingantaccen tsarin karantarwa, wato Curriculum. Tsarin karatu da muke amfani dashi a kasar (National Curriculum) ya tsufa. Domin tun 1969 aka rubuta shi. Duk da cewa ya zuwa yanzu anyi ta masa kwaskwarima, amma duk da haka da sauran rina a kaba.  Har yanzu masana basu gushe ba wajen sukan wannan kundi.  Daga cikin nakasun da ke cikinsa akwai rashin dacewa da zamani, sanadiyyar tsufa da yayi.  Akwai rashin baiwa ilimin koyon sana’a muhimmanci wajen karantarwa.  Akwai yawan damuwa ko himmatuwa da tsantsar karatu (Theory) maimakon kwatanta ilimin da aka koya.  Sannan ya cika fadi, ya cika yawa. Bai damu da abin da ya shafi horas da malamai ba, balle jin dadinsu.  Wannan shi ma wani babban nakasu ne wajen ci gaban ilimi a Najeriya.  Al’amura irin wadannan suna da bakanta rai, domin wannan kundi dai ba wani bane ya rubuta shi face mu, don  me ba za mu iya gyara shi ba?

Za mu ci gaba!

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.