Tsarin Amfani da Wayar Salula (6)

Kashi na 31 cikin jerin kasidun dake nazari na musamman kan wayar salula da dukkan abin da ya shafeta. A sha karatu lafiya.

220

Mu’amala da Fasahar Infra-red

Kafin bayyanar fasahar sadarwa ta Bluetooth tsakanin shekarar 1998 zuwa 1999, galibin wayoyin salula na amfani ne da fasahar sadarwa ta Infra-red, wadda ita ma mun gabatar da kasida guda tun shekaru 4 da suka gabata a wannan shafi.  Duk da cewa a yau an daina kera wayoyin salula masu fasahar Infra-red, amma har yanzu akwai wasu da ke dauke da masarrafar, wadanda aka kera a baya.  Ko da ma babu su, ilimi dai ba ya tsufa.

Kalmar Infra-red dai kalma ce mai tagwayen bangarori biyu da aka kago daga harshen Latin da Turancin Ingilishi.  Kalmar Infra, Latin ce, kuma tana nufin “Kasa da…”, kalmar Red kuma kamar yadda muka sani, harshen Turanci ce da ke nufin “Launin Ja…”.  Abin da wannan ke nufi shi ne, Infra-red fasahar sadarwa ce da ake amfani da ita wajen aiwatar da sadarwa ta hanyar launi kasa da launin ja.  Wannan launi kuwa na samuwa ne a jerin launuka bakwai da ke tsarin maimaituwan haske da ake kira Electromagnetic Wave, a harshen kimiyyar Fiziya na zamani.

An fara amfani da wannan nau’in sadarwa ne a kayayyakin fasahar sadarwa cikin  shekarar 1994, amma kafin nan, ana amfani da ita ne wajen kera na’urar hangen nesa, da wajen magance cututtuka da kuma daukan hotuna daga sararin samaniya. Haka ma na’urar Remote Control da muke amfani da ita wajen sarrafa akwatin talabijinmu, duk da makamashin Infra-red aka gina ta.  A takaice ma dai, bayanai sun nuna cewa an yi amfani da makamashin Infra-red cikin yake-yaken da aka yi ta gwabzawa a yakin duniya na biyu. Hukumar da ta kirkiro wannan tsari na kayan fasahar sadarwa kuma ita ce Infra-red Development Association (IrDA).  An shigar da nau’in fasahar Infra-red cikin kayayyakin fasahar sadarwa irin su wayar salula; kana iya aikawa da sakonnin lambobin waya da katittika daga wayarka zuwa wayar abokinka; kana iya aikawa da hotuna, da kuma jakunkunan sauti na wakoki ko karatuttuka da sauran bayanai.  Haka ma an shigar da wannan nau’in sadarwa cikin na’urar daukan hoto ta zamani (Digital Camera).

Bayan ka dauki hotuna, kana iya aikawa da su ta wannan hanya; kana iya aikawa dasu cikin kwamfutarka, ko kuma na’urar sawwara hotuna ko bayanai, wato Scanning Machine, don ta bugo maka su waje ka gani.  Haka na’urar sawwara hotuna daga ma’adanansu ta asali zuwa bayanai na haske, wato Scanning Machine, tana dauke da wannan fasaha, kuma kana iya shirya alaka tsakaninta da kwamfutarka, don aika mata da hotuna ko bayanai ta sawwara maka su nan take.

Sabanin fasahar Bluetooth, sadarwa a tsakanin kayayyakin fasahar sadarwa masu dauke da makamashin Infra-red ya sha banban.  Ba a bukatar doguwar tazarar da ta  gota taku uku, ko kuma mita guda.  Wannan shi yayi daidai da digiri talatin (30 Degrees).  Har wa yau, fasahar Infra-red na iya aiwatar da sadarwa ne idan ya zama babu wani shamaki komai kankantarsa tsakanin kayayyakin sadarwa biyu.  Idan akwai shamaki, ko da na kaurin silin gashi ne, sadarwa  ba ta yiwuwa.  Amma sabanin yadda muka dauka, cewa sai an hada wayar salula jiki-jiki kafin a iya aikawa da sako ta Infra-red, ba haka abin yake ba.  Idan an yi haka ba komai, amma ba ka’ida bace cewa  dole sai ta haka za a iya sadarwa.

Har wa yau, fasahar sadarwa ta Infra-red ta dara Bluetooth a wurare da dama; ba ka bukatar sai  ka nemi abokin huldanka ta hanyar barbaran wayar salularsa, a a.  Da zarar ya kunna tasa shi kenan. Amma fasahar Bluetooth dole ne ka bata lokaci wajen neman abokin hulda da kuma barbaran wayarsa.  Haka na’urar Infra-red ta fi gaugawa wajen sadar da bayanai, wannan tasa za ka iya aikawa da mizanin bayanai mai yawa cikin kankanin lokaci, sabanin Bluetooth uwar saibi da nawa; duk kwaskwariman da ake ta mata shekara-shekara.  Wannan ya faru ne saboda ka’idar da ke taimaka wa Infra-red sadarwa, wato “Very Fast Infra-red Protocol” (VIFR Protocol) ta shallake wacce ke isar ma Bluetooth, nesa ba kusa ba.

A daya bangaren kuma, wannan bai sa Bluetoth ta gaza ba kwata-kwata;  sadarwa ta Bluetooth ba ta bukatar dole sai masu sadarwa na tsaye cif, ba motsi.  Kana iya kunna Bluetooth dinka, ka sa wayarka cikin aljihu, ka ci gaba da harkokinka alhali wani na karban sako daga gareka.  Haka fasahar Bluetooth ba ta saurara wa shamaki; ko da shamaki ko babu, kana iya aiwatar da sadarwa kai tsaye.  Ka ga kowa da nashi ranar kenan.  A cewar masana ci gaban fasahar sadarwa ta zamani a lokutan baya, zai yi wahala wani ya doke wani daga kasuwa.  Domin kowanne daga cikinsu na da nashi siffa wacce abokin mukabalarsa ba shi da ita.

A takaice dai kowanne na da fagensa, kuma za su ci gaba da habaka lokaci-lokaci, iya gwargwadon yadda  bincike ko mu’amala da su ya kama. To amma, ga dukkan alamu, fasahar Bluetooth ta ci nasara kan Infra-red, domin a yanzu an daina kera wayoyin salula masu dauke da Infra-red sai Bluetooth.  Akwai alamar dai kungiyar da ke lura da habaka fasahar Bluetooth ta fi tasiri wajen samar da kirkire-kirkiren ci gaba a fannin sadarwa.

Mu’amala da Fasahar GPRS

- Adv -

Daga cikin hanyoyin aiwatar da sadarwa wajen karba da aikawa akwai tsarin General Packet Radio Service, ko GPRS a gajarce.  Sai dai sabanin sauran fasahohin sadarwar da suka gabata (Bluetooth da Infra-red), fasahar GPRS ba a iya gani. Wani tsari ne ko kintsin hanyar sadarwa da ke cikin ruhin wayar salula da aka tsofa mata, tun ran gini.

Tsarin sadarwa ta fasahar GPRS ita ce hanyar da ta kunshi aikawa da kuma karbar sakonnin da ba na sauti ko murya ba, tsakanin wayar salula da wata waya ‘yar uwarta.  Wadannan sakonni da ake iya aikawa ta hanyar GPRS dai su ne rubutattun sakonnin tes (SMS) ko Imel ko mu’amala da fasahar Intanet ta hanyar wayar salula ko kuma tsarin kira ta hanyar bidiyo (video call).  Wannan tsari na sadarwa na cikin sababbin tsare-tsaren da wayoyin salular da aka kera cikin zamani na biyu (2nd Generation Phones) suke dauke dasu.  Kuma ita ce hanya ta farko da ta fara bayyana wacce ke sawwake sadarwar da ta shafi rubutattun sakonni da na bidiyo da kuma mu’amala da fasahar Intanet.

Amma kafin nan, tsofaffin wayoyin salula na amfani ne da hanya kwaya daya wajen aikawa ko karbar dukkan nau’ukan sakonni.  Idan kana magana da wani, to, ko da an aiko maka rubutacciyar sako, baza ta shigo ba sai ka gama magana sannan ta iso.  Idan kana son aikawa da rubutacciyar sako kuwa, ta hanyar aikawa da murya za ka aika, kuma da zarar ka fara aikawa, layin zai toshe babu wanda zai iya samunka, sai lokacin da wayar ta gama aikawa sannan za a iya samunka.  Wannan ya faru ne saboda wayoyin salula na zamanin farko (1st Generation Phones) na amfani ne da layin sadarwa guda daya rak.  Wannan tsari shi ake kira Circuit Switched Data (CSD).  Karkashin wannan tsari, kamfanin sadarwarka zai caje ka ne iya tsawon lokacin da sakonka ya dauka kafin ya isa, wanda kuma mafi karancin lokaci shi ne dakiku talatin (3o seconds).

To, amma da tsarin sadarwa ta wayar iska na GSM ta bayyana, sai aka samu fasahar GPRS, wacce ke amfani da layin aikawa da karbar rubutattun sakonni kai tsaye tsakaninta da wata wayar.  Hakan kuma na samuwa ne musamman idan wayar na dauke da fasahar Wireless Application Protocol, wato WAP, wacce ita ce ka’idar da ke tsara sadarwa a tsakanin kwamfuta da wayar salula, ta hanyar wayar iska.  Karbar sakonnin text ko Imel ko kuma mu’amala da fasahar Intanet ta hanyar GPRS shi yafi sauki da kuma sauri wajen mu’amala.   Sai dai kuma wannan tsari na GPRS na cikin nau’ukan hanyar sadarwa da kamfanin sadarwa ne ke bayar dasu, wato Network Service.  Wannan ke nufin idan wayarka na da WAP, ko kuma tsarin mu’amala da fasahar Intanet, to kana iya amfani da ita kai tsaye wajen shiga Intanet.   Kuma da zarar ka yi haka, kamfanin sadarwarka zai caje ka kudin zama a kan layi.

Tsarin sadarwa ta GPRS na amfani ne da wasu hanyoyi masu zaman kansu wajen aikawa da sakonni.  Wannan tsari shi ake kira Multiple Access Method a harshen kimiyyar sadarwar zamani.  Ta amfani da wannan tsari, wayarka na iya karban sakonnin Imel ko tes, a yayin da kake magana da wani.  Sai dai kawai ka gansu sun shigo.  Kana iya karbar rubutattun sakonni fiye da daya a lokaci guda.  Hakan ya faru ne saboda tsarin na amfani ne da hanyoyi fiye da daya wajen karba ko aikawa da wadannan sakonni.  Ba ruwansa da layin da kake karbar sakonnin kira na sauti, sam.  Sai dai kuma, mu a nan galibi, kamfanonin sadarwarmu na amfani da ita ne kawai don bayar da damar shiga ko mu’amala da fasahar Intanet.

Idan ka fara mu’amala da fasahar Intanet a wayarka, za ka an rubuta kalmar “GPRS” a sama daga hannun dama.  Idan kana cikin lilo a duniyar Intanet sai aka kira ka, layin zai dakata, har sai ka gama tukun. Kamfanonin sadarwar tarho dinmu duk suna da wannan tsari na GPRS, amma kamar yadda na zayyana a sama, idan ba wayoyin salula na musamman irinsu BlackBerry ba, ba a iya amfani da ita sai wajen shiga Intanet kadai.   Amma a sauran kasashe ana amfani da wannan tsari wajen karba da aikawa da sakonnin tes, da sakonnin Imel da kuma yin hira da abokinka ta hanyar gajerun sakonni, wato Instant Chat. 

Dangane da nau’in wayar salula, akwai yanayin sadarwa iri uku ta amfani da fasahar GPRS.  Akwai wayoyin salula masu karfin karbar kira na sauti ko murya da kuma karba ko aikawa da sakonnin tes, duk a lokaci guda.  Ma’ana, kana magana sannan kana rubuta sakon tes, idan ka gama rubutawa, ka aika da shi nan take, ba tare da layin da kake magana da abokinka ya yanke ba.  Wadannan wayoyin salula sune ke martaba na farko, a sahun wayoyin salula masu amfani da fasahar GPRS, wato Class A kenan.  Har wa yau su ne nau’ukan wayoyin salula masu amfani da babbar manhajar wayar salula ta Symbian, ko Windows Phone, ko Android, ko kuma iOS na kamfanin Apple.  Su ne nau’ukan da ke iya bayar da daman mu’amala da masarrafar waya sama da guda daya a lokaci daya, wato Multitasking kenan.

Sai kuma wadanda ke biye dasu, wato Class B, wadanda idan kana amfani da fasahar GPRS, ta amfani da Intanet ko sakonnin tes, sai kira ya shigo, to wayar za ta tsayar da wancan layin da kake karbar sako ko kake mu’amala da Intanet, don baiwa layin da ke karbar kira damar sadar da kai da wanda ke kiranka.   Wadannan sune kusan kashi hamsin cikin dari na ire-iren wayoyin da ake amfani dasu a yanzu.  Sai nau’i na karshe, wato Classs C, wadanda idan kana son amfani da fasahar GPRS, to dole sai ka shiga cikin wayar, ka saita ta da kanka.  Da zarar ka saita ta, to, ba wanda zai iya samunka, sai in ka gama abin da kake yi, ka sake saita ta zuwa layin karbar kira na sauti ko murya (Voice Call).

Wannan fasahar sadarwa ta GPRS dai na cikin fasahohin da suka kara wa wayar salula tagomashi da kuma karbuwa a duniya. Domin ta sawwake hanyoyin yadawa da karbar sakonni ba tare da mushkila ba. Kana iya mu’mala da fasahar Intanet.  Kana iya aikawa da sakonnin hotuna ko bidiyo ko sauti ta tsarin Multimedia Message Service, wato MMS.  Sai dai kuma a lura, duk sakon da ka aika, za a caje ka.  Haka duk lokacin da ka shiga giza-gizan sadarwa ta duniya don yin lilo, za a caje ka.  Iya dadewarka, iya yawan kudin da za a diba daga layin wayarka.

Bayan haka, har yanzu kamfanonin waya basu gama daidaitawa ba a tsakaninsu wajen aikawa da karbar hotuna ko sakonnin Imel ko sauti ko bidiyo ta hanyar fasahar GPRS.  Ma’ana, a yanzu za ka iya aikawa da hoto ta tsarin MMS mai amfani da fasahar GPRS daga layin MTN ne kadai zuwa wani layin MTN din. Amma ba za ka iya aikawa zuwa layin Etisalat ko Glo ko Airtel ba. Haka yake a sauran layukan.  Kowa ba ya iya karba daga wani, sai tsakanin layukansa.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.