Ziyarar Gidajen Yanar Sadarwa (3)

Wannan mako za mu leko gidan yanar sadarwa na Gumel.com ne, wanda Malam Salisu Hashim Gumel ya dauki nauyin ginawa da tafiyar dashi. A sha karatu lafiya.

244

GUMEL.COM (http://www.gumel.com)

Cikin yawace-yawacen da muke yi a gidajen yanar sadarwa a matsayin ziyara, a yau za mu bakonci Zauren Gumel.com ne; gidan yanar sadarwa ta farko da aka fara dorawa a giza-gizan sadarwa ta duniya.  Kafin mu ci gaba, zan so sanar da masu karatu cewa wannan ita ce makala ta karshe a wannan silsila da muka dauko na ziyara.  Zuwa mako mai zuwa za mu juya akala zuwa wani bangaren kuma, don dada fadada sanayyarmu ga hanyoyin sadarwa ta zamani, in Allah Ya yarda.

Gidan Yanar, Kacokan

 

 

Wannan gidan yanar sadarwa ta Gumel.com, ginanniyar gida ne da aka gino daga kwarangwal (template) din manhajar gina gidan yanar sadarwa ta Dreamweaver, wanda kamfani da gidan yanar Macromedia (http://www.macromedia.com) ta kirkira.  Duk da yake kamfanin Adobe (http://www.adobe.com) ta saye wannan manhaja na Dreamweaver, har yanzu akan masa lakabi da sunan kamfanin Macromedia din.  To da daya daga cikin kwarangwal dinsa ne aka gino gidan yanar.  Kuma shi ma maginin yayi amfani ne da fasahar Java Script wajen kawata hotuna da haruffan da ke dakunan gidan yanar gaba daya.  Duk tambarin da ka matsa da dan manunin kwamfutarka (mouse pointer), za ka ga ya canza, ko kuma ya motsa zuwa wani abu daban.  Har wa yau, maginin yayi amfani da gajeren fasahan tsara hafuffa da kasidu a dakin gidan yanar sadarwa, wato Cascading Style Sheets, ko CSS a takaice.   Da zarar ka shigo zauren gidan yanar, za ka fara cin karo ne da wani babban tambari (Banner) a saman zauren, mai dauke da hotunan Hausawa a zaune a tabarma.

A bangaren dama kuma wata baiwar Allah ce cikin lullubi irin na matan Hausawa.  A tsakiya ga wani babban tambarin GUMEL, wanda aka masa dogarawa da sunayen wasu daga cikin biranen kasan Hausa; Kano, Zaria, Maiduguri, Abuja.  Ga alama dai wannan tambari na kwance ne a kan wani taswira (map) mai dauke da sunayen garuruwan Hausa.  Kasa da wannan tambari kuma za ka ci karo da matakalan shiga sauran dakunan gidan gaba daya, wato Navigational Links.  Daga nan sai maginin ya raba gidan zuwa bangarori uku, kamar irin tsarin da maginin Kanoonline yayi; bangaren tsakiya, sai hagu da kuma dama. Bangaren tsakiyan a rabe yake daga kwance.  Hakan ya bayar da daman sake raba bangaren zuwa kashi uku, sama da kasa.

Abin da ke Ciki

Kamar sauran gidajen yanar sadarwa a Intanet, gidan yanar Gumel.com na dauke ne da bayanai na sauti da hotuna masu motsi da marasa motsi da kuma tarin bayanai (texts).  A tsagin hagu na zauren gidan yanar, za ka samu mashigi ne zuwa wasu dakuna da gidajen yanar sadarwa.  A sama akwai rariyar likau zuwa Majalisar Hira (Chat Room) na Gumel.com, wanda ba a gama ginawa ko ba.  Kasa dashi kuma sai rariyar likau zuwa gidajen yanar sadarwa na wasu mujallu da jaridun Nijeriya irinsu: African News, Daily Trust, Daily Independent, Daily Champion, Guardian, This Day, Vanguard, The Sun, Punch, Triumph, da Nigerian Tribune.   Kasa da wadannan kuma sai kafofin da zasu riskar da kai majalisun tattaunawa na Finafinan_Hausa (wanda Farfesa Abdallah Uba Adamu ya kirkira kuma Malam Magaji Galadima ke shugabanta), da kuma na Gamji.com.   

- Adv -

A bangaren tsakiya kuma a sama, za ka cin ma BARKA DA ZUWA GUMEL, wanda aka rubuta da manyan haruffa.  Kasa dashi kuma za ka ci karo da rariya guda uku, masu dauke da hotuna, da zasu sadar da kai in da za ka samu bayanai kan Kasar Hausa da Tarihinta, da Wakokin Hausa da kuma Littafan Hausa.  tsagin da ke biye da wannan kuma zai riskar da kai ne zuwa bangaren Koyon Hausa, da bangaren Tallace-tallace, sai kuma shafin da zai kai ka gidajen rediyon Hausa, irinsu BBC Hausa, da Muryar Amurka (Voice of America), da Jamus (Deustchewelle) sai kuma Sashen Hausa na Rediyon Kasar Sin (China Radion International).  Sai bangaren karshe, wanda zai sake riskar da kai ne zuwa Sashen Littafan Hausa da Giajen Rediyo da kuma Wakokin Hausa.  A wadannan bangarori, za ka samu wakoki ne na zube, irin wakokin su Marigayi Mamman Shata da sauransu.  Har way au, akwai wasu shafukan daban, wadanda basu cikin jerin wadanda na zayyana.  Idan mai karatu ya koma kasan tambarin gidan yanar gaba daya, zai ga Shafin Farko, Trihin Hausa, Ma’aikatanmu, Wakokin Hausa, Bayaninmu, Saduwa Da Mu.  Wadannan, a takaice, su ne aubuwan da ke cikin wannan gidan yanar sadarwa.

Manufa

Manufar kafa wannan gida ko shafi a bayyane take; ilimantar da duniya kan kasar Hausa, musamman ma kasar Gumel (ko Lautai, kamar yadda mai gidan ya kira garin) da masarautar Gumel din gaba daya.  Sai manufa ta biyu, wanda it ace koyar da harshen Hausa.  wannan shafi ba a gama gina shi ko ba.  Alal hakika idan ka shiga wannan gida, za ka amfana da abubuwa da dama, daga littafai zuwa kasidu da wakoki.  Don haka wannan ke nuna cewa babban manufar assasa wannan gida shi ne ilmantar da duniya kan kasar Hausa.   Na tabbata wannan na daga cikin abin da tasa aka gina gidan da harshe biyu; Husa da Turancin Ingilishi.

Uban Gidan Yanar (Webmaster)

Mai wannan gidan yanar sadarwa shi ne Malam Muhammad Hashim Gumel, dan kasar Gumel ne, kamar yadda ya nuna a fili; daga sunan gidan yanar zuwa dukkan abin da ke ciki.  Mutum ne mai sha’awar tarihi da al’adu, kuma a halin yanzu yana zaune ne a kasar Amurka.  Ya dade a can, a gaskiya.  Kuma shi ne wanda ya fara gina gidan yanar sadarwa da harshen hausa a giza-gizan sadarwa ta duniya (a iya sani na), kafin zuwan su Dandali  da Kanoonline.   Shi yake tafiyar da wannan gidan yanar sadarwa tare da wani bawan Allah mai suna Abba Dauda Abba.  Allah Ya saka musu da alheri, amin.

Shawarwari

Yana da kyau a yi kokarin hanzarta karasa gina Zauren Hira (Chat Room), wannan na daga cikin abin da ke kara ma gidan yanar sadarwa shahara da yawan maziyarta.  Sai kuma wasu ‘yan kurakuran rubutu (typographical errors) da nai ta cin karo dasu cikin shafuka daban-daban.  Misali, a shafin Tarihin Hausawa, an rubuta “arewacin Nijeriya” da “arewancin Nijeriya”, wato an kara harafin “n”, wanda bai kamata a shigar ba.  Bayan haka, akwai matsalar lahaja (dialect);  misali, an yi amfani da kalmar “tarishi”, maimakon “tarihi”, kamar yadda yake a daidaitacciyar Hausa.  Allah sa mu dace gaba daya, amin.

Kammalawa

Daga karshe, za mu dakata a nan, sai wani mako in Allah Ya kai mu.  Kamar yadda na sanar, mako mai zuwa za mu koma wani banganren, don fadada fahimtarmu kan hanyoyin fasahar sadarwa ta zamani.  Kada a mance a kai ziyara zuwa Mudawwanarmu da ke: http://fasahar-intanet.blogspot.com.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.