Web 3.0: Fasahar “EDGE Computing” (1)

Abin da wannan sabuwar fasaha ta kunsa shi ne, kusantar da cibiyoyin sarrafa bayanai zuwa ga masu amfani da na’urorin sadarwa na zamani.  Ma’ana, gina wuraren da ke dauke da kwamfutoci da na’urorin da za su rika sarrafa bayanan da mutane ke aikawa a tsakaninsu, a kusa da inda suke, saboda sawwake adadin lokacin da bayanan za su rika dauka kafin su isa inda za a sarrafa su, har a samu sakamako cikin lokacin da ake bukata.  – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 3 ga watan Yuni, 2022.

216

Matashiya

Makonni uku da suka gabata na ci gaba ne da tsokaci kan turakun sabuwar fasahar giza-gizan sadarwa ta marhala ta uku, wato: “Web 3.0” kenan, inda mai karatu yaji bayani dalla-dalla kan Fasahar “Blockckain”, wacce nan gaba ake sa ran ta habaka fanni da tsarin hada-hadar kudade ta amfani da hanyoyi da na’urorin sadarwa na zamani.  A baya kuma mun gabatar da bayani kan Fasahar “Artificial Intelligence” (AI), wacce ta kunshi tsarin da zai kara habakawa tare da inganta tsarin sarrafa bayanai ta amfani da manhajoji da na’urorin sadarwa na zamani, yadda za su zama masu tunani da kansu, don hasashe da kirdadon abin da ya dace.

A wannan mako ga mu dauke da bayani kan rukuni na uku na wannan sabuwar marhalar giza-gizan sadarwa na duniya zubi na 3.

Fasahar “EDGE Computing”

Fasahar “EDGE Computing” dai tsari ne na kusantar da hanyoyin sarrafa bayanai da muke musayarsu a tsakaninmu ta hanyar wayoyin salula ko kwamfuta ko sauran na’urorin sadarwa, don rage lokacin aikawa, da sarrafawa, da kuma karbansu, da kuma inganta tsarin ma’amala dasu.  Abin da wannan zance ke nufi shi ne, a tsarin da muke gudanar da sadarwa a halin yanzu, idan ka aika sako daga wayar salularka, ko kwamfuta, ta amfani da kwamfuta dake jone da siginar Intanet, sakon zai bar wayarka ne, ya zarce cikin kwamfutocin kamfanin da kayi amfani da manhaja ko masarrafa ko shafinsu na Intanet, wanda ke can kasar da kamfanin yake, ko wata cibiya da kamfanin ya samar a wata nahiya daban, daga can kuma a sarrafa bayanan, kafin aika su zuwa kwamfuta ko na’urar da wanda ka aika masa sakon yake amfani da ita.

- Adv -

Misali, idan ka aika sakon Imel daga wayar salularka a yau Jumma’a, 3 ga watan Yuni, 2022, zuwa adireshin Imel dina mai suna: wasiku@babansadik.com, wannan sakon zai fita daga wayar salularka ne, ya wuce zuwa kwamfutar dake sarrafa sakonnin Imel na kamfanin Google (idan Gmail ne) dake kasar Amurka.  Yana isa can, za a sarrafa sakon, sannan a cillo shi zuwa adireshin Imel dina mai suna: wasiku@babansadik.com, wanda kuma yake dauke cikin kwamfutar kamfanin dake adana shafukan gidan yanar sadarwana na Taskar Baban Sadik dake: https://babansadik.com.  Kamfanin na kasar Amurka ne.  Sakon na isa akwatin Imel din, nan take sai manhajar Imel dake wayar salulata kuma ta dauko mini shi kai tsaye zuwa kan wayata, duk cikin lokacin da bai wuce minti 1 zuwa 5.

Wannan, a takaice, shi ne fayyataccen misali kan yadda sakonni ke fita, a sarrafa su, sannan a aika su zuwa ga wanda ake son ya samesu, ta amfani da na’urori da hanyoyin sadarwa na zamani.

Wadannan na’urori su ne: kwamfuta da dukkan nau’ukanta, da wayar salula da dukkan nau’ukanta, da kuma na’urorin sarrafa bayanai da aika su a zangon sadarwa, irin su: “Router”, da “Server”, da “Switch”, da kuma wasu kananan na’urorin sadarwa wadanda ake amfani dasu a asibitoci, ko dakunan binciken kimiyya, ko kuma motoci masu amfani da na’ururi masu basira (Smart Devices) wajen gano bigire da sauransu.  Wadannan na’urori kenan.  Bangare na biyu shi ne hanyoyi da manhajojin sadarwa.  Su kuma sun hada da fasahr Imel da dukkan nau’ukanta, da fasahar Intanet da dukkan nau’ukanta, da sauran manhojin karba da aika sakonni, da kuma shafukan Intanet masu dauke da fasahohin sadarwa na zamani.

Wannan misalin yadda tsarin yake kenan, a galibin wurare da lokuta a halin yanzu.  Amma, ta la’akari da tsarin da ake hasashen samunwansa nan da ‘yan shekaru kadan, wanda sabon tsarin giza-gizan sadarwa na duniya mai suna: “Web 3.0”, akwai saibi a ciki.  Musamman idan bayanan da ake aikawa ana bukatar samakonsu ne cikin gaggawa, wato: “Real time data”.  Shi yasa a halin yanzu ake gina wannan sabuwar fasahar musayar bayanai da sarrafa cikin dan kankakin lokaci, don inganta harkokin rayuwa gaba daya a Intanet, a duniya.

Abin da wannan sabuwar fasaha ta kunsa shi ne, kusantar da cibiyoyin sarrafa bayanai zuwa ga masu amfani da na’urorin sadarwa na zamani.  Ma’ana, gina wuraren da ke dauke da kwamfutoci da na’urorin da za su rika sarrafa bayanan da mutane ke aikawa a tsakaninsu, a kusa da inda suke, saboda sawwake adadin lokacin da bayanan za su rika dauka kafin su isa inda za a sarrafa su, har a samu sakamako cikin lokacin da ake bukata.  Abu ne sananne cewa, a wannan zamani na ci gaban kimiyya da fasahar sadarwa na zamani, daga cikin abin da ke taimakawa wajen inganta kasuwanci, da sadarwa, da harkar kiwon lafiya, da ceton rayuka, da inganta tsarin shugabanci a wurare ko kasashen da ake amfani da hanyoyin sadarwa na zamani wajen ayyukan gwanmati ko kamfanoni da kungiyoyi.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.