Shafin Kimiyya Da Fasaha Ya Sauya Take

Na tabbata masu karatu sun lura da sauyin take da aka samu a wannan shafi, daga “Kimiyya da Fasaha” zuwa “Kimiyya da Kere-kere”.  Hakan ba kuskure bane na mashin, lokaci ne yayi da ya kamata wannan sauyi ya samu. A takaice ma dai, har wasu cikin masu karatu sun bugo waya don nuna farin cikinsu da wannan canji da aka samu. Duk da haka mun ga dacewar gabatar da fadakarwa da kuma dalilan da suka haddasa hakan.

505

Tuna Baya

Wannan shafi dai ya dade yana daukan taken “Kimiyya da Fasaha”.  To amma idan mai karatu ya yi la’akari da nau’ukan bayanai ko kasidun da ake bugawa a shafin, zai ga cewa: ko dai bayanai ne kan yadda tsarin kimiyya yake – musamman kimiyyar sararin samaniya (astronomy) – ko kuma bayani kan tsarin kerarrun kayayyakin kimiyya ko fasaha.  Ire-iren wadannan kerarrun kayayyaki sun hada da kwamfuta da wayoyin salula, da fasahar Intanet, da tsararrun hanyoyin sana’antawa tare da yada bayanai da dai sauransu.  Kamar yadda muka sanar kuma mai karatu zai ci gaba da gani nan ba da dadewa ba, wannan shafi yana kan fadada fannonin bincike ne don dacewa da taken da tun farko aka bashi.  Don haka kasidu kan kere-kere a fannin ababen hawa (automobile technology), da jiragen sama da dukkan nau’ukansu, da fannin kimiyyar sinadarai da na sararin samaniya, da kuma bangaren lantarki, duk za a ta cin karo dasu a wannan shafi.

Haka ma abin da ya shafi fannin kimiyyar halittu.  Fannin da muka yi kokarin kauce masa da gangan dai shi ne bangaren abin da ya shafi kimiyyar magunguna da yadda ake shansu.  Wasu cikin masu karatu sun rubuto tambayoyi don neman shawara kan wasu kwayoyi da yadda ake shansu.  Ban basu amsa ba saboda ina tunanin samun lokaci makamancin wannan don fadakarwa, da kuma nuna wa masu karatu iya haddin da wannan shafi ya takaita a kai.  Shawarwari kan yadda ake shan magunguna ko tsarin da ya kamata a sha su, ko nau’ukan da suka kamata a sha, duk ba ya cikin hurumin wannan shafi.  Akwai shafin Dakta Auwal Bala kan Kiwon Lafiya, wanda kuma ke amsa tambayoyi kan ire-iren wadannan al’amura, cikin ilmi da kwarewa.  Sai a doshe shi don samun gamsuwa, tunda a kan haka ya kware.

A takaice dai, idan muka dubi dukkan wadannan kerarrun kayayyakin kimiyya da bayaninsu ya gabata, za mu ga cewa ba su bane “Fasahar”, a a, “sakamakon fasahar ne” – ko kace Technology a turancin zamani.  Wannan tasa wasu ke fassara kalmar Technology da “Fasahar Kere-kere”, duk da cewa hakan ma kuskure ne. Abin da yafi dacewa da kalmar shi ne “kere-kere” kawai.  Domin idan muka ce “fasahar kere-kere”, muna siffata nau’in fasahar da aka kera abin ne, ba wai abin da aka kera ba.  Wanda mu kuma a wannan shafi muna nufin “wannan shafi ne don fa’idantuwa da bayanan da ke bayyana tsari da kimtsin kere-kere” – wato abin da aka kera su da fasahar kere-kere.  Don haka muka canja taken wannan shafi zuwa “Kimiyya da Kere-kere”, kuma dai shi ne “Science and Technology” din, a harshen turancin zamani.  Sai mu bibiyi wadannan kalmomi daya-bayan-daya don fa’idantuwa da sakon da suke bayarwa, a da, da ma wannan zamani da muke ciki.

Kalmar “Kimiyya” asalinta kalmar Larabci ce – daga “Al-Keemiya” –  kuma tana da ma’anoni guda biyu, inji Mu’ujamul Waseet, wato daya daga cikin Kamus din Larabci na zamani.  Kamus din yace: “Malaman da, ko magabata, suna amfani da wannan kalma ne don nufin canza nau’in ma’adanai daga wani nau’in zuwa wani.”  Idan kuma suka ce “Ilmin Kimiyya”, suna nufin “…ilmin sanin yadda ake zagwanyar da sinadaran karkashin kasa ne, don samar da wani nau’in daban (musamman don mayar da su zinare).”  Amma a wajen Malaman Zamani, a Larabce idan aka ce “Kimiyya”, in ji wannan Kamus, yana nufin: “…ilmin binciken wani fanni (musamman na karkashin kasa) mai dauke da dokoki (ko ka’idojin) da ke taimakawa wajen fahimtar tsarinsa.” (Mu’ujamul Waseet, shafi na 844). Wannan kalma ce Hausawa suka aro ta, kuma suke fassara ma’anar “Science” da ita, kamar yadda Neil Skinner ya tabbatar a cikin Kamus na Turanci da Hausa, shafi na 156, inda ya kawo kalmar Science, yace: “ilmi irin na zamani (kamar su Kimiyya).”  Wannan ke nuna cewa kalmar “Kimiyya” da Hausawa ke nufi, shi ne ma’anar da kalmar turanci ta Science ke bayarwa, ba wacce ma’anar kalmar Larabci ke bayarwa ba.  Wannan kenan.

A daya bangaren kuma, kalmar “Fasaha”, ita ma daga Larabci muka aro ta – asalinta shi ne: “Al-fasaahatu”, wadda ke nufin “bayyanawa…ko kubutar harshe ko lafuzza daga sarkakiyar zance ko rubutu, mai haddasa wahalar fahimta”, inji Mu’ujamul Waseet, a shafi na 723.  A hausance idan aka ce “fasaha”, (dangane da wannan ma’ana da Kamus din ya bayar), ana nufin “bayyanannen abu, wanda babu sarkakiya a ciki ko wahalar fahimta a tare da shi”.  A daya bangaren kuma, Kamus din yaci gaba: “Faseehi shi ne mutum mai kyautata zance, mai bambance kyakkyawa daga mummuna wajen zance.”  A nashi bangaren, Al Imam Ibnul Atheer ma haka ya tabbatar a littafinsa mai suna An-Nihaayah fee Gareebil Hadeeth wal Athar, mujalladi na 3, shafi na 403.  Ga abin da yace kan kalmar “Faseehi”, siffar mai “Fasaha”: “…(mutum) mai sakakkiyar harshe wajen zance, wanda ya san kyakkyawa daga mummuna.”  Dukkan wadannan ma’anoni a Larabce kenan.

- Adv -

Amma a harshen Hausa, kamar yadda ma’anar kalmar “’Kimiyya” a Larabce ta sha bamban da ma’anarta a Hausa, to haka ma ma’anar kalmar “Fasaha” ta sha bamban da ma’anarta na Larabci.  A cikin Kamus dinsa mai suna Hausa-English Dictionary, shafi na 309, wanda kuma aka buga tun shekarar 1934, Likita Bergery ya kawo ma’anar kalmar “Fasaha” da abin da take nufi a Hausance da kuma Larabce, inda yace: “Fasaha: Cleverness, whether of brain or hand. (But in Arabic = Eloquence).”   Kamar yadda sunan Kamus din ya nuna, marubucin kan kawo kalmar Hausa ce, sannan ya fassara ma’anarta a turance.  Ya kuma tabbatar da cewa a Hausa kalmar “Fasaha” na nufin “haza ka” ne, wajen tunani ko iya tsara abu da hannu.  Amma a Larabce, kamar yadda ya nuna cikin baka biyu, abin da kalmar ke nufi shi ne “iya tsara zance”, ko “hikima wajen iya magana, ta yadda kowa zai iya fahimta, komai karancin ilminsa.”  Wannan kuwa shi ne abin da ake kira Eloquence a harshen Turanci.  Kuma shi ne ma’anar da dukkan Kamus din Larabci ke bayarwa.

Daga bayanan da suka gabata, a tabbace yake cewa yin amfani da “Kimiyya da Kere-kere” shi ne abin da yafi dacewa da shafinmu, fiye da kalmar “Kimiyya da Fasaha”.  Duk da yake na san masu karatu sun fi sabawa da kalmar “Kimiyya da Fasaha”, saboda saukin fada.  Amma a yi hakuri.  Daga yanzu taken wannan shafi shi ne “Kimiyya da Kere-kere”.  Mun yi hakan ne don tabbatar da abin da shafin ke tabbatarwa.  Na kuma tabbata nan ba da dadewa ba masu karatu zasu saba da wannan sauyi da aka samu.


Mudawwanan Shafin

Kwanakin baya na sanar da masu karatu cewa akwai Mudawwana (Blog) na musamman da na bude don taskance ko adana kasidun da suka shafi Kere-kere, da kuma Ilmin Sararin Samaniya, don amfanin dukkan masu sha’awan wadannan fannoni.  Nayi hakan ne don baiwa masu sha’awa samun saukin isa ga kasidun a killace, ba tare da sai an ta jigilar nemansu a wancan Mudawwana ba.  Don haka duk  mai bukatar kasidun da suka shafi Sararin Samaniya, da fannin Kere-kere, to yaje Zauren Kimiyya da Kere-kere, wanda ke: http://kimiyyah.blogspot.com.

Masu neman bayanai kan abin da ya shafi Fasahar Intanet da Kimiyyar Sadarwa kuma, wato Information Technology, sai su je shafin Makarantar Kimiyya da Fasahar Sadarwa, wanda ke: http://fasahar-intanet.blogspot.com. Idan akwai karin bayani da ake nema, sai a tuntubemu ta hanyoyin da aka saba. Kuma zanyi kokarin ganin cewa na rika sanya adireshin Mudawwanar da ta danganci kasida ko makalar da aka buga a dukkan mako.  Don fadakarwa ga masu neman kasidun a Intanet.

Shafin Kimiyya da Kere-kere na mika dubun gaisuwarsa ga dukkan masu karatu, da masu bugo waya don neman karin bayani ko godiya, musamman irinsu Malam Sani Abubakar ‘Yankatsare da ke Jas, da Aliyu Muktar Sa’idu (IT) da ke Kano, da Malam Munzali Jibril da ke Gumel, da Malam (Uncle) Bash da ke Jimeta, da Malam Abbass Ameen, da Malam Khaleel Nasir Kuriwa, Kiru, Kano, da sauran masu karatu da ke Legas da Patakwal da sauran wurare.  Allah albarkace ku, ya  kuma bar zumunci, amin.

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. Nura Shehu says

    Alhamdulillah, Gaskiya muna godiya da irin wannan dinbin ilimi da kuke bamu muke amfana dashi a koda yaushe. Allah Ubangiji ya kara basira. Ameen thumma Ameen

Leave A Reply

Your email address will not be published.