Sakonnin Masu Karatu (2015) (1)

A yau za mu amsa wasu daga cikin sakonnin da kuka aiko mana ne ta Tes da Imel.  Masu bukatar kasidu na aika musu. Sai su duba akwatin Imel dinsu.  Akwai wadanda suka aiko sakonni da jimawa kuma ban samu daukansu ba sai wannan karo.  Ina neman afuwa kan tsaiko da aka samu.  Ina mana fatan alheri a cikin dukkan al’amuranmu, kuma da fatan zamu yi sallah lafiya.  Allah karbi ayyukanmu kyawawa, ya yafe mana kura-kuranmu baki daya, amin.  Barka da Sallah!

170

Salamun alaikum Baban Sadiq, da fatar kana cikin koshin lafiya. Shin,
Windows 10 tana aiki akan kowace Android?   Tambayata ta biyu ita ce, Kwamfuta ta wallahi tana yawan daukewa.   Sannan akan nuna mini: “Windows is not genuine.”  Ko na je anyi “Activating” din.   Na gode kwarai.  –  Hafizu Balarabe – hafizubalarabe@yahoo.com

Wa alaikumus salam Malam Hafizu, ai babbar manhajar “Windows 10” da aka kaddamar ana dora ta a kan kwamfuta ce, ba kan wayar salula ba.  Duk da cewa akwai nau’in Windows dake wayar salula, wanda kamfanin Microsoft ya kera a wayoyin salula nau’in Lumia, wato “Windows Phone” kenan.  Amma dangane da sauran nau’ukan wayoyin salula masu dauke da wata manhaja daban ba ta Windows Phone ba, ba za su iya daukan babbar manhajar Windows 10 ba.  Kai hatta su kansu nau’ukan Lumia din, sai nan gaba ne kamfanin Microsoft zai fitar da nasu nau’in Windows 10 din.

Dangane da matsalar da kake samu da babbar manhajar Windows dake kwamfutarka a halin yanzu kuma, ga dukkan alamu babbar manhajar ba orijina bace, ma’ana ba ta asali bace, ta bogi ce, wato “Pirated.”  Wannan ke nuna cewa a asali ba ita ce hakikanin babbar manhajar dake kwamfutarka ba, daga baya ne aka dora maka ita.  In kuwa haka ne, duk sadda ka hau Intanet da ita, kamfanin Microsoft za su iya gane cewa wannan ba ta asali bace, ta bogi ce.  Wannan shi ne babban dalilin da yasa kake ganin wannan sako dake cewa: “Windows is not genuine.”

A duk sadda ka sayi sabuwar kwamfuta, da zarar ka hau Intanet da ita, tana yin musayar bayanai tsakaninta da kwamfutocin kamfanin Microsoft, don karin tagomashi.  Wannan shi ake kira “Windows Update.”  Daga cikin bayanan da take saukarwa daga kamfanin akwai wata karamar manhaja mai suna: “Windows Genuine Advantage Validation Tool,”  ko “WGA” a gajarce.  Wannan ita ce manhajar dake da alhakin gano gangariyar Windows daga jabunta.

Don haka, idan Windows dinka ba gangariya bace, orijina, nan take wannan manhaja za ta motsar da bayanan da kake gani a shafin farko da zarar ka kunna kwamfutar, wato: “Windows is not genuine,” ko wani zance makamancin haka.  Idan har kwamfutarka ta fara nuna maka wannan sako, to, sai dai kayi hakuri dashi sai sadda ya dauke sannan ka samu shiga kwamfutar.  Galibi yakan yi dakiku 15 ne (15 seconds).  Da fatan ka gamsu.


- Adv -

Assalamu alaikum Baban Sadik, ina da tambayoyi kamar haka: 1) Ka taimaka ka gaya mana abubuwa uku kacal da Najeriya ta samar a fannin kimayya da kere-kere, wadanda yanzu haka ake cin kasuwarsu a kasuwannin duniya.  2) A ganinka wasu matakai ne na gaggawa Najeriya za ta dauka domin tarar da sa’anninta wurin samun ‘yanci, da suka yi mata  fintinkau a fannin kimiyya da kere-kere?  3) Ko kimiyya ta tabbatar da samuwar aljannu a wannan duniya tamu?  Daga Ashiru Dan’Azumi Gwarzo.  alasheerd@gmail.com

Wa alaikumus salam Malam Dan’Azumi, da fatan kana lafiya.  Bayani kan kirkirarrun hajojin fasaha da Najeriya ta samar kuma ake cin gajiyarsu a duniya a fannin kimiyya da kere-kere abu ne dake bukatar bincike na musamman.  Idan Allah ya kaddaremu zan ribaci lokaci don aiwatar da bincike kan haka, saboda karuwarmu.  Amma kafin nan, ina son ka san cewa akwai tsari da gwamnatin tarayya karkashin ministan kimiyya da fasahar sadarwa da kere-kere, wanda ake wa take da: “National Technology Incubation,” inda kwararru ‘yan Najeriya ke aiwatar da bincike da samar da hajoji a wannan fanni don amfanin ‘yan kasa baki daya.  Shiri ne wanda na san bai yadu ta ko ina ba, amma dai akwai shi.

Dangane da tambayarka ta biyu, mun riga mun gabatar da gamsasshen bayani kan yadda Najeriya za ta zage dantse don cinma sauran kasashen da suke tsararta ne a baya, amma suka shallake ta a yanzu saboda kalubalen dake fuskantarmu.  Wadannan bayanai sun zo ne cikin shahararriyar kasidarmu mai take: “Ciyar da Najeriya Gaba a Fannin Kimiyya da Kere-kere,” wadda muka gabatar a shekarar 2010.  Shafukan kasidar sun kai 14!  A ciki mun bayyana halin da kasar nan ke ciki, da manyan matsalolin dake dakile ci gabanmu baki daya.  A karshe kuma na kawo shawarwari kan hanyoyin ci gaba.  Wadannan hanyoyi dai su ne:  samar da shugabanci na gari, da lura da bukatun kasa/al’umma don yi musu abin da zai amfane su, da samar da makamashi na hakika (kamar wutar lantarki ta dukkan hanyoyin zamani misali), da bayar da tallafi ga Cibiyoyin Binciken Ilmi (Research Centers), da samar da yanayin karatu mai kyau a makarantu, wato samar da ingantaccen ilimi dai kenan a takaice.

Abu na gaba shi ne aiwatar da tsarin da ake kira “Satar Fasaha” ko  “Industrial Espionage” a harshen turanci, sai kuma yin nazarin kirkirarrun hajojin fasaha da kere-kere daga Wasu kasashe.  Wadannan dunkulallun shawarwari ne da sai ka karanta kasidar za ka ga abubuwan da suka kunsa.

Tambayarka ta karshe kan ko fannin kimiyya ya tabbatar da duniyar aljanu, wani fage ne dake bukatar fadadawa.  Babu amsa kwaya daya.  Akwai wadanda suka tabbatar akwai wadanda suka kore samuwar aljannu da duniyarsu gaba daya.  Sannan akwai wadanda basu tabbatar ba kuma basu kore ba, daga cikin kwararrun malaman kimiyya na duniya, amma suna kan gudanar da bincike na kwakwaf, don kokarin tabbatar da gaskiya ko rashin gaskiyar hakan.  Wannan ma, kamar tambayarka ta farko, na cikin abin da nake bincike a kai don kawo mana wadannan bangarori guda uku, bayan mun gama bukukuwan sallah, in Allah ya yarda.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.