Me Yasa Hukumomin Kasashen Duniya Ke Kayyade Tsarin Ma’amala da Kafafen Sadarwa Na Zamani?

A halin yanzu akwai adadi mai yawa na mutane dake ta’ammali da wadannan kafafe na sadarwa a duniya.  Misali, Dandalin Facebook na da adadin masu rajista sama da biliyan biyu da miliyan dari bakwai (2.7 billion), a kididdigar shekarar 2021. – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 22 ga watan Yuli, 2022.

245

Matashiya

Wannan shi ne kashi na hudu cikin jerangiyar makalolin da muka faro cikin makonni uku da suka gabata, duk da canjin taken, maudu’in duka daya ne.  Bayan koro bayanai a takaice kan abin da wancan sabuwar doka da hukumar NITDA ke gab da fitarwa ya kunsa, na sanar damu cewa ba kasarmu kadai ba, akwai kasashe da dama da suka fitar ko suke gab da fitar da dokoki makamantan wannan.  Tambayar ita ce:  meye dalilin da yasa hakan ke faruwa?

Amsar wannan tambaya ce za ta taimaka mana wajen fahimtar dalilan da suka sa gwamnatin Najeriya ke kokarin samar da wannan doka.  Daga nan ne za mu yi sharhi na karshe kan abubuwan da suka kamata a gyatta su a dokar, ko abubuwan da suka kamata a kara ko cire daga ciki, da abubuwan da suka kamata ayi Karin haske a kansu.  Kafin nan, me yasa kowace kasa ke kokarin kayyade wadannan kafafe na sada zumunta ne?

Yawa da Bunkasa

Dalili na farko shi ne, wadannan kafafen sadarwa sun yi yawa, kuma a kullum kara bunkasa suke da sauyawa wajen hada mutane a tsarin sadarwa na gamayya. Tun ana aiwatar da sadarwa ta hanyar rubutu kadai, yanzu bayan rubutu, ana aika hotuna, da bidiyo, da kuma sauti.  Sannan kai tsaye ana aiwatar da kira, irin wanda a baya sai ta amfani da tsarin sadarwar wayar salula kadai ake yi.  Bayan haka, hatta tarurruka na kai tsaye (Live meetings) ana yi a wadannan kafafe na sadarwa.  Wannan ya sauya tsarin alakoki tsakanin mutane dake duniya, ba ma Najeriya kadai ba.  Daga madarar zumunci zuwa kasuwanci, da siyasa, da shugabanci, da samartaka, da karatu da karantarwa, da addini da tunatarwa, da dukkan abin da mutane keyi a zahirin rayuwa na neman maslaha.

- Adv -

A halin yanzu akwai adadi mai yawa na mutane dake ta’ammali da wadannan kafafe na sadarwa a duniya.  Misali, Dandalin Facebook na da adadin masu rajista sama da biliyan biyu da miliyan dari bakwai (2.7 billion), a kididdigar shekarar 2021.  A daya bangaren kuma, shafin bidiyo na Youtube, mallakin kamfanin Google, yana da masu rajista biliyan biyu da miliyan dari uku (2.3 billion), shi ma.  Sai manhajar WhatsApp wanda na kamfanin Facebook ne (ko Meta), mai adadin masu rajista sama da biliyan biyu (2 billion).  Sai manhajar Facebook Messenger, mai adadin masu rajista biliyan daya da  miliyan dari uku (1.3 billion).

Daga cikin manhajoji masu tarin jama’a har wa yau akwai manhajar Instagram, wanda mallakin kamfanin Meta ne.  Wannan dandali na da masu rajista sama da biliyan biyu da miliyan dari biyu (1.2 billion).  Daga nan sai manhajar wayar salula mallakin kamfanin kasar Sin mai suna “WeChat”, wanda ke da adadin masu rajista biliyan daya da miliyan dari biyu (1.2 billion) shi ma.  Sai manhajar wayar salula na TikTok, mai adadin masu rajista sama da biliyan daya (1 billion) a halin yanzu.  Sai kafa ta karshe, wato: Twitter, mai adadin masu rajista sama da miliyan dari hudu (400k).

Idan muka dawo gida Najeriya kuma, a bayyane yake cewa adadin ‘yan Najeriya dake ta’ammali da wadannan kafafen sadarwa na zamani na dada karuwa ne a kullum, musamman ta la’akari da adadin jama’ar dake kasar.  Daga cikin mutum miliyan dari biyu da ‘yan doriya dake rayuwa a wannan kasa tamu, akwai mutane sama da miliyan dari da arba’in da biyar (145 million) dake ta’ammali da fasahar Intanet a Najeriya.  Kuma kaso mafi tsoka na wannan adadi duk suna yin hakan ne ta hanyar wayar salula.  Dangane da alaka da kafafen sada zumunta kuwa, akwai ‘yan Najeriya sama da miliyan talatin da biyar (35 million) dake da rajista a Dandalin Facebook.  A bangaren manhajar WhatsApp kuwa, akwai ‘yan Najeriya sama da miliyan casa’in (90 million) dake da rajista.  Wannan a bayyane yake, idan muka yi la’akari da cewa galibin ‘yan Najeriya na ta’ammali da fasahar Intanet ne ta hanyar wayar salula.  Sai Dandalin Twitter mai dauke da adadin ‘yan Najeriya sama da miliyan uku (3 million) kacal, sabanin miliyan talatin da a baya ake ta yayatawa, musamman sadda aka samu sabanin tsakanin Gwamnatin Najeriya da kamfanin.

Munanan Tasiri da Illoli

Bayan wadancan fa’idoji da jama’a ke samu sanadiyyar wannan sadarwa ta gamayya, akwai matsaloli da illoli kuma, wadanda ba sa misaltuwa. Wadannan matsaloli ko illoli suna cutar da jama’a nesa ba kusa ba.  Wannan yasa galibin kasashe ke kokarin ganin sun samar da daidaito tsakanin wadannan fa’idoji da cutarwa da tsarin sadarwa na zamani ya samar.

A makon gobe in Allah Yaso za mu yi bayani kan ko, shin, wadannan kafafe na sadarwa, akwai wani yunkuri da suke yi ne wajen kayyade ma’amalar jama’a dake ta’ammali da kafafensu?

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.