Sakonnin Masu Karatu (2013) (10)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

99

Assalaamu Alaikum Baban Sadik, da fatan alheri mai yawa a gare ka. Me yasa iska da ruwa mai iska da ake yi suke da sunannaki.  Kuma yaya ake bambance su, misali: Tornado, Katrina, Rita, Wilma, da sauransu?  Don Allah ina bukatar bayani.  –  Ummu Haidar, Gombe

Wa alaikumus salam, a gaida Ummu Haidar, da fatan ana lafiya.  Wadannan sunaye da kike ji da gani, sunaye ne da Malaman kimiyya masu bincike suke bai wa nau’ukan guguwa ko mahaukaciyar iska da ta taba samu a wasu sasannin duniya.  Kalmar “Tornado” dai wata irin mahaukaciyar guguwa ce mai da’ira daga fuskar kasa har ta kere zuwa gira-gizai, da karfi.  Sauran sunayen da kika ambata kuma nau’ukan irin wannan iska ne da suka taba faruwa a wurare daban.  Malaman kimiyy kan basu sunaye ne don tantancewa a bangaren kasa, ko jiha, ko zamani, ko kuma yanayin iskar da irin barnar da tayi.  Da fatan kin gamsu.


Assalaamu alaikum, barka da warhaka. Allah ya taimaka ya kuma kara fahimta.  Don Allah ina so ka turo mini rubutun da kayi mai take: “Tsakanin Kwakwalwa da Zuciya wa ke Samar da Tunani,” ta adireshin Imel di na da ke kasa.  Sannan kuma ina neman izninka akan zan dora wannan kasida a shafina da ke Intanet, domin sake yada ta.  – Ahmad Abdulnasir Shuaib, Dorayi, Kano: 08182788350 – ahmadabdulnasir9@gmail.com

Wa alakumus salaam Malam Ahmad. Da farko dai na tura maka wannan kasida da ka bukata ta adireshinka na Imel da ka turo. Bayan haka na amince har abada, cewa ka sanya wannan kasida a shafinka da ke Intanet. Illa dai kamar yadda ka’idar nakalto bayanai na ilmi ta nuna, ka bayar da hakkin mallaka. Ma’ana ka tabbatar da sunan wanda ya rubuta. Allah sa a dace, amin.


Assalamu Alaikum Baban Sadik, barka da warhaka.  Me ake nufi da “Server” da kuma “Client”?  Shin, akwai bambanci a tsakanin wadannan kalmomi ne ko dai duk abu daya ne ake nufi?  Domin a wani lokaci sai inji an ambacesu a lokaci daya.  Ka huta lafiya.  –  Uncle Bash, Jimeta-Yola: 0703713338

Wa alaikumus salaam Uncle Bash.  Wadannan kalmomi dai suna da alaka mai girman gaske a tsakaninsu, duk da cewa sun sha bamban wajen ma’ana.  Da farko dai, Kalmar “Server” a ilimin sadarwa ta kwamfuta na nufin wata masarrafa ce ko na’urar kwamfuta ko sadarwa mai dauke da tsarin mika bayanai tsakaninta da wata na’ura ‘yar uwarta.  A daya bangaren kuma, Kalmar “Client” na ishara ne ga wata masarrafar kwamfuta ko na’urar sadarwa mai iya nemowa ko karbo bayanai daga wata masarrafar kwamfuta ko na’urar sadarwa mai dauke da masarrafar mika bayanai mai suna “Server” da ma’anarta ta gabata.  Kalmar farko ita ce muke kira da suna “Uwar-garke” a hausar zamani na bangaren sadarwa.  Mun kira ta “Uwar-garke” ne saboda yanayin aikinta. Kamar yadda ka san saniya uwar-garke ke baiwa ‘ya’yanta mama, a duk sadda suka bukata.  Haka wannan masarrafa ta “Server” ke bai wa duk kwamfuta ko masarrafar da ta bukaci wani bayani daga gare ta.

- Adv -

Asali, “Uwar-garke” kwamfuta ce da ke dauke da shafukan Intanet (Web Pages) ko bayanai a gajere ko dogon zangon sadarwa, wadda ke iya fahimtar sakon bukatar bayanai (Requests) daga wata masarrafa ko kwamfuta ‘yar uwarta.  Ita wannan kwamfuta ba ta bukata sai dai kawai a bukata daga gare ta.

Duk sadda sakon bukata ya iso gare ta, takan yi amfani da wasu ka’idojin sadarwa (Communication Protocols) wajen tantance ingancin sakon, da kuma tambayar wadda ta turo sakon harshe irin na sadarwa.  Da zarar ta gamsu da jawaban da ta samu, nan take sai ta bayar da bayanan da aka bukata daga gare ta.  Ita kuma mai nema, ita ce “Client.” Tana iya zama kwamfuta ce ko wayar salula, ko na’urar sarrafa bayanai (irin iPaid, ko Samsung Galaxy Note, ko Galaxy Tab, ko Google Nexus).  Har wa yau, ana iya samun kwamfutoci masu bukatar bayanai (Clients) sama da goma su diro kan Uwar-garke guda daya a lokaci daya, kuma duk tana iya amsa musu nan take.  Dukkan wannan al’amari kan faru ne cikin kankanin lokacin da bai wuce dakiku (seconds) goma ko ashirin ba, iya gwargwadon ingancin yanayin sadarwar da ke tsakanin mai nema da wadda ake nema daga gare ta.   Wannan yanayi ko tsari shi ake kira “Client-Server Model” a ilimin kimiyyar sadarwar zamani.


Assalaamu alaikum Baban Sadik, barka da warhaka, ina fatan kana lafiya tare da daukacin masu karatu.  Tambayata ita ce: shin, me yasa idan mutane suka mutum da babbar wayar, sai ka ji suna tambayar cewa, “Shin Android ce?” Abin da nake son sani a nan shi ne: Mene ne Android?  Kuma wani abu ne yasa wannan wayar da ke dauke da Android ta fi tasiri a tsakanin wayoyin salula na zamanin yau da yasa har mutane ke rubibin sayenta?  Sannan kuma ko akwai kwamfutar Android?  In akwai, shin, mene ne ya bambanta wayoyin Android da kwamfutar?  –  Uncle Bash, Jimeta-Yola: 0703713338

Wa alaikumus salam Uncle Bash, da fatan kana lafiya kai ma. Da farko dai kamar yadda ka tambaya, kalmar “Android” na ishara ne zuwa ga babbar manhajar wayar salula da galibin wayoyin salular kamfanin Samsung, da LG, da Motorola, da SonyEricsson, da kuma HTC.  A baya-bayan nan kamfanin wayoyin salula na kasar Sin mai suna TECNO ya shigo cikin harkar shi ma, inda ya fito da wayoyin salula masu kima, masu zafi, masu inganci, dauke da wannan babbar manhaja ta Android.  Babbar manhajar Android na kamfanin Google Incorporated ne da ke kasar Amurka, ta hadin gwiwa da wasu kamfanonin waya da harkar sadarwa kusan goma.  Tana daga cikin shahararrun manyan manhajojin wayar salula da ake ji dasu a duniya a yau.  Sadda kamfanin Nokia ya saye kamfanin Symbian da ke bai wa sauran kamfanonin waya irin su Samsung da LG da Motorola lasisi, sai suka koma kan wannan babbar manhaja ta Android. Ga dukkan alamu, wannan na daga cikin abin da ya daga su, har a karshe suka shallake kamfanin Nokia a kasuwar wayar duniya baki daya. Nau’in wannan babbar manhajar waya dai ita ce Android Jelly Bean 4.3.

Daga cikin dalilan da suka haddasa mata shahara da karbuwa a tsakanin jama’a a duniya akwai saukin mu’amala, da hanyoyin samar da masarrafan wayar salula masu sawwake mu’amala da bayanai ko ita kanta wayar, a sawwake kuma na kyauta.  Bayan haka, wannan babbar manhaja ta Android tana da ingantacciyar hanyar sadarwa ta Intanet ba tare da matsala ba, da hanyoyin ta’ammali da bayanai daga waje ko cikin wayar masu inganci; ta hanyar masarrafan na’urorin daukan hoto, da na’urar daukan bidiyo, da fasahar Bluetooth da dai sauransu.  Sannan akwai kwamfuta mai dauke da wannan babbar manhaja ta Android. Kamfanin kera kwamfutoci da wayar salula mai suna Dell ne ya fara kera kwamfutocin tafi-da-gidanka (Laptops) masu wannan babbar manhaja.  Cikin makonni uku da suka gabata ya fitar da wasu nau’ukan kwamfutocin tafi-da-gidanka jerin nau’in Dell XPS, guda uku: wato Dell XPS 11, da 12, da kuma 13.

Wadannan siffofi ne suka bambanta babbar manhajar wayar salula ta Android (wanda kamfanonin Samsung, da LG, da Motorola, da HTC, da SonyEricsson ke kerawa) da wayoyin salula masu dauke da babbar manhajar Windows Mobile (wadanda kamfanin Nokia, misali, yake kerawa).  Babbar manhajar Windows Mobile wacce ke dauke cikin nau’ukan wayar Nokia Lumia da dukkan rabe-rabenta, ta sha bamban.  Na farko dai ta fi wahalar sarrafawa ga mai dan karamin sani, wanda bai saba mu’amala da kayayyakin sadarwa na zamani ba, sannan ba ka iya sarrafa bayanan da ka taskance cikin karamar ma’adanar MMC dinka, sabanin Android.  Abin da kamfanin Microsoft ya fi damuwa da shi a wannan babbar manhaja shi ne tsaron bayanai, da tsaron ita kanta babbar manhajar, wato: “User and Applications Data Security.”

A daya bangaren kuma, ban taba amfani da kwamfuta mai dauke da babbar manhajar Android ba, domin basu yadu sosai ba. Kamfani daya ne na sani yake kera su, kuma basu yadu ba.  Amma dole za a samu bambanci wajen masarrafai, da yawan abubuwa masu taimaka wa kwamfuta aiwatar da ayyukanta, wadanda wayar salula ba ta da irinsu. Amma idan ka kebe wannan, duk dabi’ar sauri, da saukin mu’amala duk daya ne.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.