Tsarin Manhajar WhatsApp (1)

Manhajar WhatsApp na cikin sababbin manhajojin wayar salula (Mobile Application) da suke tashe a yanzu, kuma ana hasashen nan gaba sai ta kere sauran manhajoji. A yau za mu dubi yadda tsari da kintsin wannan manhaja yake ne. A sha karatu lafiya.

350

Kafuwa da Tasiri

Cikin shekarar 2009 ne wasu matasa biyu – BRIAN ACTON da JAN KOUN – tsofaffin ma’aikatan kamfanin Yahoo! suka kirkiri masarrafar da a halin yanzu ta rikide zuwa Whatsapp, don aiwatar da sadarwa a tsakaninsu a gajeren zangon sadarwa – LAN.  Zuwa watan Nuwamba na shekarar (2009), Brian ya gayyaci wasu abokansa 5, su ma tsoffin ma’aikatan Yahoo! don zuba jari, da manufar sana’ar ta ci gaba. Wadannan abokai sun zuba dalar amurka 250,000 ($250,000). Cikin watan har wa yau aka fitar da zubin farko na masarrafar Whatsapp, wanda ke aiki a kan wayar iPhone kuma ta hanyar App Store na kamfanin Apple kadai ake iya samu.

Ana shiga shekarar 2010, sai Jan ya gayyaci wani abokinsa mai suna Chris Peiffer, masani kan masarrafar kwamfuta, ya shigo cikinsu, kuma shi ne ya gina manhajar Whatsapp dake aiki a kan wayar Blackberry. Daga nan aka ci gaba da samar da nau’ukan manhajar Whatsapp a wasu wayoyin, irin su Nokia, da Android, da dai sauransu. Wayoyi masu dauke da babbar manhajar Symbian ba su iya daukan manhajar Whatsapp, sai nau’in Nokia N9 kadai. Nau’in manhajar whatsapp na Android ne na karshe wajen samarwa.

A halin yanzu kamfanin na dauke da ma’iakata 55 ne, kuma cikin watan Fabrairun wannan shekara ne kamfanin Facebook ya saye manhajar da kamfanin gaba daya, a zunzurutun kudi dalar amurka biliyan 19 ($19 billion), wajen naira tiriliyon 3.2 (N3.2tr) kenan a kudin Najeriya. Ana kan tsara yadda za a mika wannan kamfani ne ga hukumar Facebook a halin yanzu.

A watan Disamba na shekarar 2013, kamfanin Whatsapp ya sanar da cewa akwai mutane masu amfani da wannan manhaja sama da miliyan 400 a kowane wata. Bayan wasu watanni kuma (April 2014), ya sake fitar da sanarwa cewa masu amfani da manhajar sun kai miliyan 500 a duk wata. Sannan a duk yini, masu amfani da manhajar na aika hotuna sama da miliyan 700, da bidiyo sama da miliyan 100, sannan a duk yini, ana musayar sakonni (messages) sama da biliyan 10 a wannan manhaja ta Whatsapp!  Dankari!!!

- Adv -

Madaukai (Platform)

Manhajar Whatsapp da ake samu a nau’ukan wayoyin salula dake amfani da babbar manhaja daban-daban, ba iri daya bace, ko kadan.  Akwai manhajar Whatsapp nau’in Android da ake samu a cibiyar “Play Store” (ko “Google Store”) kadai.  Akwai nau’in iOS da ake samu a cibiyar “App Store” kadai.  Akwai nau’in Symbian da ake samu a cibiyar “Ovi Store” kadai.  Akwai nau’in Blackberry da ake samu a cibiyar “App World” kadai.  Sannan akwai nau’in Windows Phone da ake samu a cibiyar “Store” kadai.  Kowanne daga cikinsu daban yake, kuma muddin ba nau’in babbar manhajar wayar da aka gina don ita bane, ko an saukar, wayar ba za ta iya lodawa ba.

Nau’in da aka fara ginawa shi ne na iOS, a shekarar 2009.  Shi ne wayoyin salular iPhone masu dauke da babbar manhajar iOS zubi na 4.3 suke iya amfani dashi.  Sai nau’in Blackberry da aka gina a watan Janairu, shekarar 2010.  Shi ne wanda wayoyin Blackberry masu dauke da babbar manhajar Blackberry 4.6 ke iya amfani dashi (har zuwa Blackberry 10 – kamar su Z10 da Z30).  Sai nau’in Android da ke aiki a kan babbar manhajar Android zubi na 2.1 zuwa sama.  A watan Satumba na shekarar 2011 din dai har wa yau aka fitar da nau’in WindowS Phone, wanda wayoyin salula masu dauke da babbar manhajar Windows ke iya amfani dashi.  Daga nan aka samar da nau’i guda wanda ke taimaka wa wayoyin salula kanana na kamfanin Nokia masu amfani da babbar manhajar Nokia Series 40 (Nokia S40).

Su wadannan wayoyin salula dai ba nau’ukan “Smartphones” bane, amma an agaza musu ne ta la’akari da yawan jama’a dake amfani dasu musamman a kasashe masu tasowa, a tunani na.  Wadannan wayoyi dai ne: Nokia C3-00, da Nokia C3-01, da Nokia X2-01, da Nokia X3-02, da Nokia X3-02.5 (Refresh), da Nokia X2-00.  Sai Nokia Asha: 201, da 205 Chat Edition, da 206, da 208, da 210, da 300, da 301, da 302, da 303, da 305, da 306, da 308, da 309, da 310, da 311, da 515, da 500, da 501, da 502, da 503, da kuma Asha 230.  Bayan wadannan kananan wayoyi, akwai Nokia N95, wadda ita ce nau’in Smartphone mafi dadewa da ke iya amfani da manhajar Whatsapp.  An kera ta ne a shekarar 2007, tun kafin a kirkiri manhajar ma kenan.

A makon da ya gabata masu karatu da dama sun ta tambayar da wani irin dabarun gina manhajar kwamfuta ne aka gina manhajar Whatsapp, wato “Programming language” kenan?  Wannan tambaya ce mai kyau.  Sai dai kamar yadda na sanar a kasidar da nake rubutawa mai take: “Yadda Tsarin Dandalin Facebook Yake,” manhajoji irin wadannan ba su ginuwa ta amfani da dabaran gina manhaja kwaya daya.  Akwai nau’ukan dabarun gina manhajar kwamfuta da dama da aka yi amfani dasu wajen gina manhajar Whatsapp. Wadannan dabaru dai su ne: Erlang, JQGrid, da LibPhoneNumber, da LightOpenID, da LightTPD, da PHP, da kuma YAWS.  Dukkan wadanann dabarun gina manhajar kwamfuta ne; da kanana da manya.  Babbar manhajar kwamfuta da suke amfani da ita kuma, wato “Operating System,” ita ce: FreeBSD.  Nau’in LINUX ce, wacce ke jure wahala, da dawainiya, da tsawon zamani tana kunne.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.