Me Ka Sani Kan Motoci Masu Amfani da Makamashin Lantarki? (1)

A yau mun dauko kasidar daya daga cikin masana harkar sadarwa da kere-kere ne dake shafin Endgadget.com, wato: Steve Dent, wanda yayi kan motoci masu amfani da makamashin lantarki (Electric Cars). Wannan shi ne kashi na daya. Mako mai zuwa kashi na biyu na tafe.

346

Marubuci: Steve Dent, engadget.com

Mai fassara: Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadik)


Kusan shekaru dari da suka shude ne wata yarjejeniya kan kera motoci masu amfani da makamashin lantarki (Electric cars) ta ruguje tsakanin Henry Ford da Thomas Edison.  Babban dalili shi ne rashin ingancin fasahar batir mai iya taskance makamashin lantarki da zai iya tafiyar da motar.  Tun daga wancan lokaci motoci ke amfani da makamashin gas da fetur, wanda hakan ne ya jefa mu cikin zamani mai cike da dumamar yanayi.  Sai dai kuma, wani abin farin ciki shi ne a halin yanzu kamfanin Ford ya hada kai da kamfanonin kera motoci irin su Tesla da Chevrolet don kera motoci masu amfani da makamashin lantarki masu dimbin yawa.

Kamfanin Toyota ne ya jagoranci wannan sabon zamani, inda ya kera nau’in Prius mai amfani da makamashin gas da lantarki (Gas-Electric Hybrid).  A yayin da kamfanin Tesla ya samar da nau’in Elon Musk da Model S, wadanda ke amfani da zallan makamashin lantarki.  Nau’ukan motoci masu amfani da makamashin gas da lantarki su suka fi shahara, duk da bambancin da ke tsakaninsu.  Misali, nau’in Toyota Prius ta sha bamban nesa ba kusa ba da nau’in Volt na kamfanin Chevy; duk da cewa dukkansu suna amfani da makamashin gas da lantarki ne.  To me yasa ake samun wannan bambacin fasaha waje kerawa?  Bari mu kutsa duniyar sababbin nau’ukan da aka kera masu amfani da ko dai makamashin lantarki zalla ko na lantarki da makamashin gas, mu gani.

- Adv -

Meye Haka Kuma?

Tarihin motoci masu amfani da makamashin lantarki na farowa ne daga farkon shekarar 1880, amma wacce aka kera ta hakika a farko, ita ce wadda hamshakin mai kudin kasar Ingilan nan wato Thomas Parker ya kera a shekarar 1884.  Fasahar motoci masu amfani da makamashin ta kasaita iya gwargwado a karni na 19, musamman cikin shekarar 1912, sadda aka kera wajen 34,000 a kasar Amurka kadai.  Wannan adadi kusan shi ne  adadin nau’ukan masu amfani da lantarki da gas da aka kera a shekarar 2002.  Ire-iren wadannan nau’ukan motoci na nan birjik a cikin birane suna shawagi, saboda saukin mu’amalarsu.  Kari a kan haka, motoci ne da aka yi masu cin gajeren zango, kuma galibin masu saye da hawansu mata ne.  Amma bayan ci gaba da aka samu wajen inganta tituna da kuma ma’adanar man fetur mai dimbin yawa da aka gano, sai motoci masu amfani da man fetur suka yawaita fiye da masu amfani da lantarki da gas.  Zuwa tsakiyan shekarar 1910 sai galibin kamfanoni suka daina kera motoci masu amfani da makamashin lantarki tsantsa, sai ‘yan kadan hana rantsuwa da suka ci gaba da kera kananan motoci na musamman da ake amfani dasu wajen dauko abubuwa a filayen kwallon gof ko wuraren gine-ginen gidaje.

Daga nan aka daina kera ire-iren wadannan motoci, in ka debe wani gajeren yunkuri da aka yi wajen kera nau’in Henney Kilowatt tsakanin shekarar 1959 da 1960, wacce bata yi kasuwa ba a karshe.  An ci gaba da gudanar da bincike don fadada wannan fasaha ta nau’in abin hawa, har zuwa shekarar 1967 lokacin da aka kera nau’in Amitron da kamfanin American Motors ya kera.  Wannan nau’in mota mai amfani da hadakar makamashin lantarki da gas ita ce kuma nau’in farko har wa yau da aka kera wadda ke iya rage karfin makamashin lantarki a duk sadda aka taka birki, don baiwa na’urar rike makamakin motar damar alkinta makamashin da ke cikinta.  Wannan yasa motar ke iya daukan dogon zango sanadiyyar maimaituwar karfi da makamashinta ke samu a duk sadda aka taka birki.  An ci gaba da amfani da wannan dabara na fasahar Amitron a nau’ukan motocin kamfanin Audi da Volvo da ma wasunsu da dama.

Zan ci gaba mako mai zuwa.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.