Bincike Kan Bacci da Mafarki a Mahangar Kimiyya (3)

Wannan shi ne kashi na uku na kasidarmu kan bacci da mafarki a mahangar kimiyya. A sha karatu lafiya.

305

Madaidaicin Bacci

Wannan shi ne nau’in bacci na biyu.  Na kira shi da suna “Madaidaicin Bacci” ne don bambance shi da “Bacci mara nauyi,” wato matakin bacci na daya da na biyu a karkashin nau’in bacci mai nauyi.  Wannan nau’in bacci na dauke da mataki daya ne kacal.  Kuma shi ne matakin da mai bacci ke afkawa cikinsa, mintuna 70 zuwa 90 da fara baccinsa.  Idan mai karatu na tare da ni, na sanar da shi cewa matakin farko a bacci mai nauyi kan dauki mintuna 10 ne. Mataki na biyu kuma kan dauki mintuna 20.  Mataki na uku kuma kan dauki mintuna 30.  Sai kuma mataki na hudu, wanda ke daukan mintuna 25 zuwa 30.  Idan aka tara wadannan mintuna, za a samu 85 zuwa 90.  Da zarar mai bacci ya kai tsawon wannan lokaci, sai ya shiga yanayin bacci madaidaici.

A cikin wannan yanayi, kwayan idon mai bacci kan jujjuya, su rika motsawa daga nan zuwa can.  Wannan shi ake kira Rapid Eye Movement (REM).  Kuma shi ne abin da masu bincike suka hango tun cikin karni na 20, ta hanyar wancan na’ura mai suna Electroencephalograph (EEG).  A cikin wannan yanayi ne kwakwalwarsa ke zama kar, ta ci gaba da aiki sama da yanayin farko.  A cikin wannan yanayi ne jijiyoyin gabobin jikinsa ke sandarewa gaba daya, ya kasa motsi.  A cikin wannan yanayi ne har wa yau, mai bacci ke yin mafarke-mafarke nau’uka daban-daban. An kuma gano hakan ne ta hanyar tambayar masu baccin da aka sa a karkashin wannan na’ura ana lura da su a halin baccinsu.  Duk wanda yace ya yi mafarki, da zarar an duba sai a ga a sadda kwayan idanunsa ke jujjuyawa ne a halin baccinsa.

Masana sun kasa tantance dalilin da ke sa kwakwalwar dan adam zama a farke sosai, da yin aiki sama da yadda take yi a farko, da jujjuyawan kwayan idanunsa, da kuma yin mafarki.  Har yanzu babu wanda ya dace da wani amsa karbabbe ga kowa.  Sai dai hasashe.  Wasu sukan ce kwakwalwa kan kama aiki ne sosai a lokacin saboda taimaka wa sauraron gabobin jikin dan adam samun kuzari idan ya farka.  Wasu suka ce dan adam kan yi mafarki ne saboda kwakwalwarsa na tattauna al’amuran da suka faru ne a rayuwarsa sadda yake farke lokacin yini. Yana daga cikin dalilan da ke sa kwayan idanunsa ke jujjuyawa sadda yake bacci, don hangar abubuwa a cikin mafarkinsa.  Wasu kuma suka ce a a, kwayan idanun na jujjuyawa ne don gyatta mahallin zamansu, da kuma kara giris a wuraren da ba su samun giris sadda mai jikin yake farke.  Har yanzu dai lalube ne ake yi a cikin gaibu.   Kuma ya zuwa wannan lokaci da nake rubutu, bincike na ci gaba da gudanuwa don kokarin gano dalilan da ke haddasa wadannan al’amura.

Matakan Bacci

Baya bayani ya gabata cewa akwai nau’ukan bacci guda biyu; da bacci mai nauyi, da mara nauyi.  Mai nauyin, wanda Malaman Kimiyya ke kira Non-Rapid Eye Movement (NREM) Sleep, yana dauke ne da matakai guda hudu. Da gajeren bacci ko gyangyadi, kamar yadda na kira shi, da mataki na biyu wanda ke dauke da bacci na hakika.   Wannan shi ne matakin da malaman kimiyya ke kira True Sleep.  Har dai zuwa mataki na hudun.  Nau’i na biyu kuma shi ne madaidaicin bacci, wanda suka kira Rapid Eye Movement (REM) Sleep. A wannan mataki ne kwayan idanun mai bacci ke jujjuya a sadda yake bacci.  Sai dai kuma, sabanin yadda bayanai suka zo, idan dan adam ya shiga bacci, matakan da yake bi cikin baccin sun sha bamban.  Ba wai daga gyangyadi yake farawa, daga nan ya wuce matakan nau’i na farko, ya shiga na biyu, daga nan ya farka ba.  Abin ya wuce haka.

Da zarar mutum ya kwanta bacci zai bi matakin farko na bacci mai nauyi, zuwa matakin bacci na biyu, da mataki na uku, da mataki na hudu.  Wannan kan faru har na tsawon mintuna 90, kafin mai bacci ya shiga nau’in bacci na biyu, wato madaidaicin bacci kenan.  Idan ya shiga madaidaicin bacci, zai ci gaba da yin bacci, kafin wani lokaci sai kuma ya sake dawowa  matakin bacci mai nauyi na uku, wato Delta Sleep kenan, kamar yadda bayani ya gabata a baya. Daga nan ya sake gangarowa matakin bacci na biyu, wato True Sleep.  Da zarar ya kwashi mintuna 20 a wannan mataki na bacci, sai kuma ya sake komawa nau’in bacci na biyu, wato nau’in baccin da kwayar idanunsa za su rika jujjuyawa a ciki.  Bincike ya nuna cewa masu bacci kan maimaita wannan yanayi sau uku zuwa hudu a kowane lokacin baccinsu, daga nan kuma sai su farka.  Wannan ke nuna mana cewa, bayan mai bacci ya wuce mataki na farko har zuwa na hudu, zai shiga yanayin bacci madaidaici, daga nan sai baccinsa ya sake nauyaya, sanadiyyar komawa mataki ba uku, daga nan kuma ya saukaka, sanadiyyar shiga mataki ba biyu, sai ya sake komawa yanayi madaidaici.  Wannan zai maimaitu kamar sau uku ko hudu kafin farkawa.  To me ke haddasa bacci ne?

Me Ke Haddasa Bacci?

Wannan tambaya ce da galibin masana suka ta kokarin amsa ta tsawon shekaru, amma har zuwa wannan lokaci samun amsa gamsasshiya ya gagara.  Wani mai tambaya a yanar sadarwa ta duniya ya jera wasu tambayoyi kan asali da samuwar bacci ga dukkan masu binciken kimiyya a duniya, wanda a cawarsa har yanzu sun kasa amsawa.  Yace me yasa, duk kwarewarsu a fannin kimiyya, da samuwar hanyoyi da na’urorin sadarwa da binciken kimiyya a duniya, amma sun kasa gano abin da ke haddasa bacci?  Yace idan har da gaske suke yi a fanninsu na bincike wanda a kanshi suka kware kuma aka sansu, me yasa har yanzu suka kasa gano dalilin da yasa dan adam da sauran halittu ke bacci?  Ta yaya aka yi suka kera kumbo har suka je duniyar wata, suka jefa wasu kumbon nazari da bincike zuwa wasu duniyoyin, suka gano cututtuka da yadda ake tiyata har ma a cire zuciya a dasa wata, a cire koda a dasa wata, amma ga bacci, wanda dabi’a ce da dan adam ya sifatu da ita, kuma shi ne abin da dan adam yafi yi cikin kashi biyu na ukun rayuwarsa, amma sun kasa gano dalili da abin da ke haddasa shi?

- Adv -

A hakikanin gaskiya akwai alamar cewa lallai malaman kimiyya sun gaza a wannan janibi.  Farfesa Allan Rechtschaffin, babban malami a fannin bincike kan bacci da yadda yake samuwa, wanda farfesa ne a Jami’ar Chicago da ke kasar Amurka, ya kwashe shekaru 50 yana gudanar da bincike kan bacci yadda yake samuwa da dukkan alamunsa.  Amma da kansa ya sanar da mujallar New York Times cewa, sadda aka masa tambaya kan dalilin da ke sa dan adam ya shiga yanayin bacci, yace: “Wannan wani kalubale ne mai girma ga malaman ilmin halitta (Biologists).”  A wani wuri kuma da tambaya makamanciyar wannan ta sake maimaituwa, sai ya sake cewa: “A takaice dai, har yanzu babu wani bayani kan me yasa muke bacci; kawai muna yi ne a duk sadda baccin ya dauke mu.”  Wannan kamar alamar gazawa ce, to amma akwai da yawa cikin malaman kimiyya da ke ganin har yanzu bincike ake yi, kuma ba a fid da rai ba.A hakikanin gaskiya dai gano hakikanin abin da ke haddasa bacci abu ne mai wahala, domin alakar da ke tsakanin bacci da ruhin dan adam.

Agogon Dabi’a (Biological Clock)

Duk da cewa ba a gano hakikanin abin da ke haddasa dan adam bacci ba, cikin bincike da ake yi an gano lallai akwai wani yanayi na dabi’a da ke cikin jikin dan adam, wanda ke la’akari da yanayin mahalli, don tilasta wa jiki shiga yanayin bacci.  Wannan yanayin dabi’a kuwa shi ne abin da a turancin kimiyya suke kira Biological Clock, ko Circadian Rhythm.  Wannan yanayi tun cikin shekarar 1960 malaman kimiyya suka tabbatar da samuwarsa a jikin dan adam.  Wasu malamai kan kira shi Cibiyar Bacci, wato Sleep Center, amma babu wanda ya san a ina yake a jikin dan adam.  Wasu na ganin a kwakwalwa yake.  Sai dai wannan hasashe ne.  yanayi ne kawai gamamme, wanda ke amfani da mahallin da dan adam ke rayuwa a ciki.

Malaman kimiyya suka ce idan dan adam yana rayuwa a wuri, sai dare ko yamma ya shiga, nan take dabi’ar halittar jikinsa zai fahimci canjin yanayi a muhalli. Daga nan  sai wannan agogon dabi’a ya tilasta wa jikin dan adam samar da wani sinadari mai suna Melatonin wanda ke haddasa bacci nan take.  Da zarar gari ya fara wayewa kuma, jikin adam zai sinsini irin canjin da ke faruwa a lokacin da gari ya fara wayewa, sai wannan sinadari na Melatonin ya fara narkewa ko zagwanyewa, sai bacci ya kaura daga idanun mai bacci, ya farka. Da zarar rana ta fito, ko an shiga lokacin yini kuma, sai hasken rana ya hana wannan sinadari na Melatonin zuba. Wannan abu ne mai kamar saukin fahimta, amma yiwuwarsa ya sha bamban da yadda mai karatu ke karantawa ko hankaltarsa a zuciyarsa daga abin da yake karantawa a yanzu.  Domin na san yanzu haka wani zai ce ya aka yi wasu ke yin bacci da rana?  Wannan tambayar ma dai har yanzu tana jiran amsa.

Sabubban Samuwar Bacci

Duk da cewa malamai basu gano hakikanin abin da ke haddasa bacci ba, amma sun gano sabubba da dama, wadanda ke da alaka na kut-da-kut wajen jefa dan adam cikin yanayin bacci.  Daga cikinsu akwai yawan gajiya. Kamar yadda masu karatu suka sani, yawan gajiya kan sabbaba bacci.  Abu na biyu shi ne cin bashin bacci.  Ma’ana, a rashin kwanciya a lokacin da ya kamata mutum ya kwanta, wato lokacin da bacci ya bijiro masa kenan.  Galibi mukan sha shayin kahwa ko mu tauna goro don hana bacci zuwa, ko mu sha wasu kwayoyi ko a mana allura.  Duk wadannan kan hana bacci ne na wani dan gajeren lokaci, amma ba har abada ba.  Binciken malamai ya nuna cewa cin wani abu ko shan wani abu da manufar hana bacci zuwa a lokacin da ya kamata a yi shi, yana da cutarwa mai girma, sannan hakan kan canza dabi’ar jikinsa (ma’ana agogon dabi’arsa) wanda ke bayuwa zuwa ga canza masa lokacin bacci.

Cin bashin bacci, abin da malamai ke kira Sleep Debt, yana da illa sosai, kuma kwashe tsawon yini ana bacci ba ya sa mutum ya biya bashin baccin da ake binsa.  Domin kuwa lokacin baccinsa ya riga ya canza, dole sai ya sake tarbiyyar dabi’ar jikinsa wajen tilasta mata yin bacci a lokacin da ya kamata yayi.  Galibin masu gadi a lokutan dare kan samu matsalar bashin bacci, musamman idan aka sake canza musu lokacin aiki zuwa rana.

Daga cikin dalilan da ke haddasa bacci akwai yanayin mahalli, kamar yadda bayani ya gabata.  Da zarar yamma ya gabato, akan samu sauyin yanayin dabi’ar jiki (Biological Clock), wanda hakan ke haddasa samuwar sinadarin Melatonin, nan take sai jiki ya fara canza yanayinsa, daga farkawa zuwa kasalar da ke kai mutum ga bacci.  Daga cikin abin da ke canza yanayin zuban wannan sinadari dai akwai yawan zama cikin duhu a kullum, da yawan zama cikin haske a lokacin dare; duk suna canza yanayin zubansa.

Rashin Bacci

Rashin bacci matsala ne mai girman gaske ga dan adam.  Domin yana rage kaifin fahimta.  Sannan dan adam kan shiga wani yanayi na rashin daidaituwar kwakwalwa da fahimtar abubuwa.  Rashin bacci kan taimaka wajen yawan zuban sinadaran insulin a jikin dan adam, wanda hakan ke taimakawa wajen haddasa yawan kiba a jiki  Rashin bacci na haddasa yawan mantuwa, domin kwakwalwa kan samu kanta ne cikin halin rudu.  Bincike ya nuna cewa rashin bacci na tsawon awanni 17 na iya haddasa nakasar darajar fahimta a kwakwalwar dan adam da kashi 0.05%, iya gwargwadon abin da zai iya sa mutum ya shiga halin maye idan ya sha barasa cikin moda biyu.  Rashin bacci na haddasa hauhawan jini ga dan adam, da kuma yawan kiba, kamar yadda bayani ya gabata.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.