Sakonnin Masu Karatu (2019) (7)

Shawarwari Kan Abubuwan La'akari Yayin Sayan Kwamfuta

Ci gaban sakonnin masu karatu da na samu a wannan shekara. An buga wannan bayani ne a jaridar AMINIYA na watan Maris, 2019.

227

Assalamu alaikum, da fatan Baban Sadik yana lafiya. Don  Allah  Baban  Sadik ina  son  amin  bayani  kan abin  da  zanyi  la’akari  dashi  in  zan  sayi  kwamfuta (Laptop  ko  Desktop). Kuma  wace  kirar  Kwamfuta  ta  kamata  in  saya (hp , Dell, Acer etc)?  Hassan Abdul:  08033390046

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Hassan.  Da fatan kana lafiya.  Bayani kan me ya kamata kayi la’akari dashi wajen sayan kwamfuta sabuwa, wannan ya danganci abubuwa da dama.  Na farko nawa ka tanada?  Na biyu, me kake son yi da kwamfutar?  Akwai kwamfutoci nau’uka daban-daban, daga kamfanonin kwamfuta daban-daban.  Wasu masu dan Karen tsada, wasu kuma masu araha.  Wasu kuma sun hada tsakanin masu tsada da masu araha.  Kamar masu son sayen kwamfutocinsu, kamfanonin kera kwamfuta su ma suna da nasu manufofin na kasuwanci da suke la’akari dasu yayin kera kwamfutocin da kake gani a shaguna ko a hannun mutane ana amfani dasu.

Amma duk da haka, akwai wasu kebantattun siffofi da suka kamata ayi la’akari dasu wajen sayen kowace irin kwamfuta ce ma.  Na farko kuma wanda yafi kowanne mahimanci, shi ne na’urar sarrafa bayanai ko umarnin da ake baiwa kwamfuta lokacin da ake amfani da ita.  Wannan shi ake kira: “System Processor”.  A duk sadda ka latsa wani abu a jikin kwamfuta wanda ya danganci ba da umarnin tayi wani abu, za ka so nan take kaga ta aiwatar maka dashi.  Idan ka latsa wata manhaja, kana son nan take kaga manhajar ta budo ba bata lokaci.  Idan ka kunna kwamfutar, nan ma kana son kafin kiftawa da bisimillah, ta farka firgigi.  Haka idan ka tashi zuba mata bayanai daga wata ma’adanar, zaka so nan take kaga ta karbesu ba da jinkiri ba.  Abin da ke sanya kwamfuta ta zama hakan kuwa shi ne wannan na’ura na Processor.

Wannan na’ura na Processor dai yana nan mizani mizani ne.  Akwai babba akwai karami.  Kwamfutoci masu dan Karen araha kan zo da mafi karancin mizanin Processor ne.  Galibi bai wuce 1.4Ghzt.  Ko kuma 1.6Ghzt.  Processor mai irin wannan mizanin dai zai maka aiki, amma ba cikin kazar kazar da kuzari ba.  Akwai kuma mizani babba wanda ke farawa galibi daga 2.4Ghzt, har zuwa 3.2Ghzt.  kwamfutoci masu dauke da irin wannan mizani ba su da matsala.  Kuma za ka same su a guje, sai kace an koro su, da zarar ka basu umarni.  Wannan na’ura ta Processor dai a gine take a kan kwarangwal din kwamfuta, wato: “Motherboard”, muddin kana son canza shi, sai dai ka canza “Motherboard” din gaba daya.  Wannan bai cika faruwa ba sosai.

- Adv -

Abu na biyu mai mahimmanci kuma su ne masarrafar bidiyo (Video Card) da masarrafar nuna hotuna da rubutu da zane (Graphics Card), da Ma’adanarta (Memory).  Na biyun farko su ne ke taimaka maka wajen mu’amala da bidiyo – ka ganshi rau-rau – da hotuna ko rubutun da talabijin da kwamfutar ke nuna maka.  Shi kuma ma’adana ko kwakwalwarta shi ne ke taskance dukkan manhajojin da kwamfutar tazo dasu da wadanda nan gaba zaka zuba mata, sannan ya baka damar mu’amala dasu a duk sadda ka budo su, ta hanyar tanada musu wurin da zasu zauna na wucin gadi.  Aikin farko na faruwa ne a babbar ma’adana, wato “System Hard Drive”, na biyu kuma a wata ma’adana ta wucin gadi da ake kira: “Random Access Memory”, wato: “RAM” kenan a takaice.  Su ma, kamar masarrafar “Processor”, suna da nasu mizanin daban-daban.  Amma bambancin shi ne, su ana iya canza su cikin sauki.  Kamar RAM, idan ka sayi kwamfuta mai dauke da 2GB RAM, kana iya kara mata wani 2GB RAM din.  Haka idan 4GB RAM ne, kana iya kara mata ko dai 2GB ko wani 4GB din, ya danganci girma da mizanin “Motherboard” dinta.  Haka a bangaren bidiyo da masarrafar sarrafa hotuna da rubutu, duk kana iya sayen wani ka dora mata.

Sauran abubuwan da ake la’akari dasu sun hada da girman fuskar kwamfutar (Screen Size), da mizanin batirinta wajen rike caji, da inganci sinadaran da aka kera kwarangwal dinta dasu da dai sauransu.  Kari a kan haka, yana da kyau kayi la’akari da yaduwar irin kwamfutar da za ka saya.  Akwai wasu kwamfutocin da basu yadu ba sosai, kamar mota ce, idan ka saye ta kuma daga baya ta samu matsalar da ake da bukatar canza wani bangarenta, ba a samu cikin sauki.

A karshe dai, kwamfutocin da suka shahara a nan sosai su ne HP, da Dell, da Acer.  Akwai wasu nau’ukan daban, irin su Samsung, da Toshiba, da MacBook na kamfanin Apple da sauransu.  In da hali ka sayi HP, don ta fi saukin kudi, ko da babba ce, idan aka kwatanta ta da Dell.  Dell kuma tana da inganci amma tana da tsada matuka.  Daga HP sai Acer wajen saukin kudi.  In kuma kana da hali sosai sai ka yi Dell din.

Allah sa a dace, amin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.