Shahararren Dan Dandatsa, “Alan Ralsky” Ya Shiga Hannu

Labaru da dumi-duminsu na tabbatar da cewa shahararren dan dandatsan nan mai suna Alan Ralsky, ya shiga hannun hukuma. A yau za mu dubi irin laifuffukan da yayi ne a baya, da yadda aka yi hukuma ta samu nasara a kansa, da kuma abin da ke jiransa na hukunci. A sha karatu lafiya.

167

Bayan tsawon shekaru uku tana kai masa farmaki a boye, a karshe dai hukumar binciken cikin gida na kasar Amurka, wato FBI tayi nasara wajen cafke shahararren dan Dandatson nan mai suna Alan Ralsky tare da ‘yan kungiyarsa masu aika wa mutane sakonnin bogi (Spam and Junk Mails) don zamba-cikin-aminci ta hanyar fasahar Intanet.  Mr. Ralsky, dan shekaru 64, yayi ikirari ne kan zargin da ake masa a ranar litinin da ta gabata a wata kotu da ke kasar Amurka, inda yace lallai gaskiya ne, sun kwashe shekaru suna aikata wannan mummunar ta’ada da ake tuhumarsu a kai.  Wannan mummunar sana’a da hukumar ke tuhumarsu a kanta dai ita ce wacce a turance ake kira Pump-and-dump stock spam scam.  Masu kara suka ce wannan gungu na ‘yan dandatsa da Alan Ralsky ke shugabanta sun yi suna ne wajen tallata wasu hannayen jarin wasu kamfanoni da ke kasar Sin da Hong Kong, wadanda asali masu arahan farashi ne.  Ba wanda ya damu da sayensu.

Wannan gungu na ‘yan Dandatsa dai sun sayi hannayen jarin wasu kamfanoni ne da ke kasar Sin da Hong Kong, masu araha, wadanda ba wanda ya damu dasu, kamar yadda bayanai suka gabata a sama.  Daga nan suka tsara wasikar karya da suka yi ta watsawa cikin jakunkunan Imel din mutane, musamman masu sayen hannayen jari a duniya, suna sanar dasu cewa lallai wadannan hannayen jari nan gaba kamfanoninsu zasu kara tagomashi, kuma akwai tabbacin cewa farashin su zai yi sama nan take, abin da hakan ke nuna riba ne ga masu sayensu a halin da ake ciki.  Sun dauki tsawon lokaci suna aikin aikawa da wadannan sakonni na bogi, wanda a zahiri sai kace gaskiya ne.  Hakan kuwa yayi tasiri, inda nan take farashin wadannan hannayen jari yayi sama, ana ta saye don tsammanin cin riba da samun ladan zubin jari a cikinsu.  Da wadannan ‘yan dandatsa suka lura cewa farashin ya haura fiye da kima, sai kawai suka sayar da nasu, wadanda suka saya a farashi mai karanci.  An kiyasta cewa sun ci riban a kalla dalar Amurka miliyan uku ($3M), cikin watanni goma sha takwas.

- Adv -

Hukumar FBI na tuhumar wadannan ‘yan dandatsa ne karkashin dokar haramta zamba-cikin-aminci mai suna CAN-SPAM Act da ke kasar Amurka.  Kuma kotu ta yanke musu hukunci iya gwargwadon aikin kowanne cikin wannan badakala.  Shugabansu, wato Mr. Ralsky, ya samu zaman kurkuru na tsawon watanni tamanin da bakwai a gidan yari, ko ya biya taran dalar Amurka miliyan daya ($1M).  Wannan hukunci ya shafe shi ne, tare da wani surukinsa mai suna Scott Bradley, dan shekaru 38.   Har wa yau, akwai John S. Bown mai shekaru 45, wanda shahararre ne kan sarrafa kwamfuta, kuma yana da kwarewa irin ta bai wa kwamfuta da ke wata uwa duniya umarni ta aika wa wasu sakonni  ko kuma yayi amfani da ita a matsayin bola ko matattarar bayanai daga ko ina ne a duniya.  Wannan tsari, wanda a Turancin kwamfuta ake kira Botnet, da shi ne wannan gungu na ‘yan Dandatsa suka yi amfani wajen aika bayanai na karya cikin jakunnkunan Imel din mutane tsawon wannan lokaci, don tallata hannayen jarin wadannan kamfanoni.  Shi John S. Bown, ya samu shekaru biyar a gidan yari sanadiyyar samunsa da hannu dumu-dumu cikin wannan ta’asa.  Sai kuma James E. Fite, dan shekaru 36, wanda ke jiran yanke masa hukunci a wata kotu da ke jihar Detroit, ranar ashirin da tara ga watan Oktobar wannan shekara.  Bayan James, akwai wasu guda uku a kasar Sin da ke jiran hukuncin karshe su ma, kan wannan badakala.

Mr. Ralsky dai shahararren dan Dandatsa ne kafin ruwa ya kare wa kada, inda ya shahara wajen amfani da kwarewarsa ta kwamfuta kan kowane irin ta’addinci ne, muddin zai samu abin hasafi.  Shi ne dan dandatsa guda daya da yayi fice a jihar Detroit, inda har ya taba fitowa fili, cikin shekarar 2002, ya sanar da cewa shi dan dandatsa ne, kuma duk mai son shi da wani aiki kan wannan harka ya zo, ya samu.  Wannan hira da jaridar Detroit Times tayi dashi, ta jawo masa jaraba, inda da dama cikin kamfanonin Amurka suka yi ta daukansa a boye yana musu aikin ta’addanci kan aikawa da sakonnin bogi, wato Spam Mails, don tallata hajojinsu ko kuma darkake gidajen yanar sadarwar kamfanonin abokan hamayyarsu, ta hanyar tsarin Robot Network.  Wannan tasa har buya yake yi, saboda aiyukan sun masa yawa.  Ba a jihar Detroit kadai ba, hatta a kasar Amurka da duniyar Intanet, yana cikin shahararrun wadanda ake nema ruwa a jallo kan wannan ta’ada.  A gidan yanar sadarwar SpamHaus, wacce matattarar bayanai ce kan ‘yan dandatsa shahararru da ake nema, labarai kan miyagun ta’adunsa sun bayyana har sau dari da shida (106).

Su dai ‘yan Dandatsa (ko “Hackers” a turance) mutane ne masu amfani da tsabar kwarewarsu wajen cutar da kwamfuta ta kowace irin hanya da nahiya – kai tsaye ne, ko ta wata hanya daban.  Mr. Ralsky na cikin masu alfahari da wannan sana’a a duniyar Intanet, kafin ruwa ya kafe masa a tsakiyar teku, sa’adda yake jin dadin ninkaya.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.