Kasar Sin ta Kera Makamin Tsaron Teku

Kasar Sin ta samu ci gaba a fannin kimiyyar makami, inda ta kera wani makamin yaki da zai bata kariya ta kafar teku. Me ye tasirin hakan a siyasar duniya da kuma kere-kere? Shi ne abin da makalarmu ta wannan mako za ta duba.

325

Ranar 5 ga watan Maris da ya gabata ne kasar Sin ta cilla gungun tauraron dan Adam mai suna “Yaogan-IX Naval Ocean Surveillance System (NOSS)” zuwa sararin samaniya, wanda kuma shi ne ayarin taurarin dan Adam na musamman kashi na uku da kasar ta tanada don taimaka wa sabon makami mai linzami na kariyar hari daga teku da ma sararin samaniya (Anti Ship Ballistic Missile – ASBM) da ta kera don kare kasarta.  Wannan sabon makami mai linzami da ta sanya wa suna “DengFeng 21D”, ko kuma “DF-21” a gajarce, makami ne mai linzami (missile) mai cin matsaikacin zango, kuma mai karfin darkake duk abin da yake hari a ko ina ne yake cikin kadadar tazararsa.  Makamin DengFeng 21D, wanda a Hausance yake nufin “Iskar Gabas”, shi ne irinsa na farko a duniya baki daya.  Makamin, wanda aka yi masa gwajin farko a shekarar 1985-6, an gama kera shi ne a shekarar 1991.  Gwajin baya-bayan nan da aka yi na wannan makami ya faru ne cikin shekarar 2005.  Kuma idan aka gama tsara makamin, an kiyasta cewa zai iya daukan kawunan nukiliya guda 60 zuwa 80 a cikin kowane makami mai linzami guda daya.  A halin yanzu ana gab da gama kintsa shi don fara aiki.

Asali

Cikin shekarar 1960 ne dai kasar Sin ta fara tunanin kirkiro wani makami da zai bata kariya daga irin barazanar da makamai masu linzami da kasar Amurka ta tanada a farfajiyarta cikin teku, suke mata.  Hukumar da gwamnatin kasar ta dora wa nauyin kera wannan makami mai linzami dai ita ce “China Changfeng Mechanics Electronics Technology Academy”, watau Cibiyar Kimiyyar Kere-kere ta kasar kenan.  Cibiyar ta fara ne da kera makami mai linzami nau’in DF-21 mai cin gajeren zango, mai dauke da kawunan nukiliya (Nuclear War Head) guda 500 (watau 500Kt), kuma zai iya tafiyar tazarar kilomita 1,700 (1,700km) daga inda aka harba shi.  Sai dai kuma, a lokacin ba a yi amfani da shi ba.

A shekarar 1996 sai wannan Cibiya ta Kimiyya ta kara masa tagomashi, inda ta samar da nau’in DF-21A, mai cin tazarar kilomita 2,700 (2,700km), amma kawunan nukiliya guda 90 kadai yake iya daukawa a cikin kwansonsa.  Ana shiga shekarar 2006 sai wannan hukuma, a bisa umarni da tsarin hukumar kasar, ta kara ingantawa tare da kayatar da wannan nau’in makami mai linzami zuwa nau’in DF-21C, amma mai cin gajeren zango, kuma duk tazararsa bata wuce kilomita 1,700 ba.  Sai dai kuma, Cibiyar ta shirya shi ne ta yadda zai rika amfani da fasahar GPS (Global Positioning System) wajen ganowa tare da kai hari kan abokan gaba a daidai tazarar da aka haddade masa.  Bayan haka, wannan nau’in makami na DF-21C na iya riskar duk abin da ya hango kuma yake hari, kai tsaye ba tare da ya kuskure shi ba.

Bayan ‘yan shekaru sai Cibiyar kuma ta kara wa wannan makami tagomashi har wa yau, don samun inganci.  Bayan dacewa wajen riskar duk abin da ya hango kuma yake hari, ana iya harba shi ne a kan na’urar harba makami mai linzami na musamman da aka tanada masa, mai tafiya – watau  “Mobile Antiship Ballistic Missile Launcher” – maimakon amfani da kananan jiragen sama kamar yadda sauran makamai masu linzami ke yi kafin riskar abin da suke hari.  Kari kan haka, wannan ingantaccen nau’i da Cibiyar ta canza wa suna daga DF-21C zuwa DF-21D na iya tarwatsa jiragen saman yaki da suka taso daga teku, ko sararin samaniya, ko kuma darkake jiragen ruwan yaki na musamman masu buya a karkashin teku – watau “Submarine War Ships”.  Bayan haka, wannan makami mai linzami da kasar ta kera, duk da cewa mai cin matsakaicin zango ne, yana iya kai hari daga nahiyar Asiya har zuwa nahiyoyin da ke makwabtaka da ita.

Bayan dukkan wannan kudura da karfi, wannan makami mai linzami na DF-21D zai rika karban umarnin kai hari ne daga tashar da aka cilla shi, ba wai daga wani tauraron dan Adam da ke shawagi a sararin samaniya ba, sabanin sauran makamai masu linzami irin na da.  Wannan zai ba shi damar tashi cikin tsari, da tafiya cikin natsuwa, da kai hari a daidai inda ake son ya kai, sannan ya kamo hanyar dawowarsa tiryan-tiryan zuwa tasharsa ba tare da wata na’ura ta kawo masa cikas ba wajen karban umarnin da ake bashi daga tashar da ya baro.  Kari a kan wannan, akwai gungun taurarin dan Adam masu taimaka masa wajen hango abokan gaba a ko ina suke, amma ba su suke sarrafa tafiya ko dawowarsa tasharsa ba.  Wannan irin kudura da makamin DF-21D ya samu shi ya kebance shi daga sauran makamai masu linzami masu amfani da kawunan nukiliya wajen kai hari a duniya.  Duk abin da ya dosa, sai ya darkake shi, kuma duk abin da aka harbo zuwa bigirensa, to yana iya mukabalantarsa, ya kuma tarwatsa shi nan take. Wannan ne ma yasa galibin masana ke masa lakabi da “makamin kariya daga teku”, watau “Anti Ship Ballistic Missile” ko “ASBM” a gajarce.

- Adv -

Kafin wannan makami ya fara aikinsa, akwai ayarin na’urorin tauraron dan Adam da yake bukata masu taimaka masa wajen aiwatar da aikinsa ba tare da wata matsala ba.  Kuma tuni kasar Sin ta gama cilla su zuwa sararin samaniya don su kama wajen zamansu.  Ayarin farko an cilla su ne ranar 9 ga watan Disamba, cikin shekarar 2009.  Kwanaki biyar bayan wannan, sai aka aika ayari na biyu: ranar 14 ga watan Disamba din shekarar dai har wa yau.  Ayari na karshe kuma an aika su ne ranar 5 ga watan Maris na wannan shekara.  Ayarin farko dai su ne: “Yaogan-VII Electro-optical Satellite”, ayari na biyu kuma kasar ta kira su “Yaogan-VIII Synthetic Aperture Radar”, sai kuma ayari na karshe, wanda ta kira “Yaogan-IX Naval Ocean Surveillance System (NOSS) Constellation.”  Ana sa ran gabatar da gwajin wannan makami a karo na karshe a karshen wannan shekara.  Dukkan sauran gwaje-gwajen da aka gudanar a baya an samu cin nasara kansu; babu matsala.

Tasiri a Siyasar Duniya

A bayyane yake cewa mallakar wannan makami ga kasar Sin zai canza tsarin siyasar duniya da na zaman lafiya da kuma kawancen da ke tsakanin kasashen Asiya da kasar Amurka; musamman ma kasashen Jafan, da Koriya ta Kudu, da Filifins, da kuma kasar Taiwan.  Kusan kashi sittin cikin dari na labarun da ke fitowa kan kera wannan makami da kasar Sin ke yi, na samuwa ne daga Hukumar Sojin Ruwa na Kasar Amurka (US Naval Force); abin da ke nuna cewa lallai hakan yana tasiri wajen haddasa fargaba ga sojin kasar.

Masu lura da harkokin tsaro a duniya sun tabbatar da cewa muddin kasar Sin ta gama kera wannan makami mai linzami na DF-21D, to babu abin da ya rage wa kasar Amurka illa ta kwashe komatsenta daga nahiyar Asiya ta koma wata nahiyar daban, ko kuma, a kalla, dole ne ta jirga baya sosai da tafkeken jirgin ruwan yakinta mai suna USS George Washington da ke dauke da jiragen yaki nau’in F18 sama da dubu daya da casa’in da biyu a gab da gabar tekun kasar Jafan.  Zaman kasar Amurka a tekun Pacific dai tana yinsa ne da biyu; na farko shi ne, akwai yarjejeniyar tsaro (Defense Pact) tsakaninta da wasu kananan kasashe, irinsu Jafan da Koriya ta Kudu misali.  Dalili na biyu kuma shi ne lura da shirye-shiryen tsaro da kasar Sin da Koriya ta Arewa ke yi.  To amma samuwar wannan sabon makami mai linzami na iya yi wa shirye-shiryenta targade, domin a halin yanzu dai kasar Amurka ba ta da wani kudurar da za ta iya kare jiragenta daga hadarin da ke dauke cikin wannan makami, balle kare kasashen da ke biyanta sanadiyyar kariyar da take basu a nahiyar.

Masana harkokin tsaro a nahiyar Asiya sun tabbatar da cewa kasar Sin ta fara wannan yunkuri ne don ganin ta kawar da zama da kuma barazanar da kasar Amurka ke mata a farfajiyarta.  Sannan kuma akwai tunanin cewa tana son jawo ra’ayin wasu daga cikin kasashen da ke makwabtaka da ita, don wasu manufofi na siyasa.  A karshe kuma, akwai tunanin cewa kasar Sin na kokarin hakimtar da kanta ne a nahiyar gaba daya, kamar yadda kasar Amurka ke tutiyar yi a duniya.  A karshe suka ce, hasashen da kasar Sin ke yi na ganin hakan ta hanyoyi biyu, a fili suke.  Da farko dai kasar Sin ta janye kasuwar duniya gaba daya, ta inda ta zama gagarabadau wajen habakar tattalin arzikin kasa. Abu na biyu kuma shi ne wannan kokari da take yi wajen samun kebantacciyar kudura ta hanyar tsaro a duniya gaba daya.  Wannan, a cewar kwararru, shi zai bata ‘yancin tattalin arzikin kasa da na siyasa, a siyasar duniya.

A karshe, wani hasashe da wasu kwararru suka kara yi shi ne, da wannan makami mai linzami na DF-21D, kasar Sin na iya darkake wannan tafkeken jirgin ruwan yaki na kasar Amurka da ke tekun Pacific cikin kiftawa da bisimilla, saboda tsananin sauri da tasirinsa, wanda kuma kafin kasar Amurka ta iya kawo harin daukan fansa, dole tana bukatar kusanci da kasar Sin matuka; hakan kuma ba zai iya kara bata damar hakan ba; domin iya kusancinta da kasar, iya hadarin da za ta kara shiga.  Domin kuwa, a cewar wannan hasashe, wannan makami mai linzami na DF-21D na iya jirkice abokan gaba ta hanyoyi uku; a karon farko zai haddasa wuta da hayaki mai tarin yawa, mai iya hana dukkan wani jirgin saman yaki tashi, balle yayi wani tasiri.  Na biyu kuma, zai salwantar musu da injinansu gaba daya, tare da darkake su ta sama.  A karo na uku kuma, idan jiragen yakin suna kan babban jirgin ruwan yaki mai daukan kananan jirage ne (watau Supercarrier), wannan makami na DF-21D na iya dulmuyar da jirgin ruwan zuwa karkashin teku gaba daya ma a huta.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.