Matsalolin Katin ATM a Najeriya (1)

Bayyanar katin ATM da bankuna suka fara amfani dashi wajen baiwa masu hulda dasu damar cire kudi cikin sauki, abu ne da aka ta yabawa sosai. A daya bangaren kuma, hakan yazo da nasa matsalolin. A wannan mako za mu fara duba matsalolin katin ATM ne a Najeriya, musamman yadda wasu ke amfani dashi wajen zaluntar jama’a ta barauniyar hanya.

288

Kowace Sauki da Matsalarta

Idan ba sauki bace mai damfare da asalin shari’ar musulunci, kowace sauki na tafe ne da irin nau’in matsalarta.  Wannan ka’ida ce ta rayuwa sananniya, musamman idan mai karatu yayi la’akari da sabuwar tsarin cirewa ko karbar kudi da bankunan Nijeriya suka bullo da ita mai suna Automatic Teller Machine, ko kuma ATM a takaice.  Wannan na’ura ta ATM tana dirke ne a bakin kofar kusan dukkan bankunan Nijeriya da ke manyan biranen kasar nan, wacce kwastomomin bankunan ke amfani da katin da bankinsu ya basu, don cire kudadensu ba tare da sun shiga cikin bankin sunyi layi don karba daga wajen ma’aikatan bankin ba.  Wannan kati shi ake kira ATM Card, a turance.  Katin na kumshe ne da bayanai kan taskar ajiyarka; da lambar taskar ajiyarka, da wasu lambobi na musamman, da kalmomin iznin shirgarka (PIN Cord), sa kuma sinadaran Chip, masu hada alaka tsakanin katinka da injin ATM, da kuma kwamfutocin bankin da kake ajiya, don sheda ka ta wadannan lambobi.

Ta hanyar wannan kati kana iya cire kudi daga taskarka, ko ka duba yawan abinda kake dashi a ciki, ko aiwatar da wasu aiyuka irin su sayen katin wayar salula na kamfanin MTN da dai sauran aiyuka masu nasaba da hakan.  Sannan, sai wanda ke bukata ake bashi; idan ba ka bukata, ba dole bane sai ka karba, duk dadewar da kayi kana mu’amala da bankin.  Amma duk da haka, yana da kyau ka san cewa muddin bankinka ya sanar da kai cewa akwai katin ATM ya tanada maka, ba tare da cewa kai ne ka rubuta kana so ba, to yana da kyau kayi dayan abu biyu; ko dai kaje ka karba ne tun wuri, ka soma amfani dashi, muddin kana bukata kenan.  Ko kuma kaje kace musu baka bukata, sai a san cewa baka karba ba.  Yin hakan na da muhimmanci kamar yadda mai karatu zai san dalili nan gaba.

Lokacin da wannan kati ya fara fitowa da dama cikin mutane sunyi farin ciki da zuwansa, musamman wadanda ke ajiya da  tsoffin bankuna irin su First Bank da Union Bank da Afribank da dai sauran bankuna masu dogon layi wajen karba ko zuba kudi a kullum.  Hakan ya basu damar cire kudadensu duk lokacin da suke so; daga fitowar alfijir zuwa ketowar wani alfijir din – awanni ashirin da hudu kana iya cire kudinka daga banki ba tare da shiga ka bi layi ba, ko kuma jira lokacin bude bankin ba, wanda daga karfe takwas din safiyar kowane rana ne zuwa karfe hudu ko biyar na yamma.  Wannan ba karamar sauki bace, a cewar da dama cikin masu ajiya da bankuna a Nijeriya, musamman ma manyan birane irin su Kano da Kaduda da Abuja da Legas da Fatakwal da sauran birane.  Kamfanin da ke dillancin wadannan mashuna na ATM dai shine kamfanin INTERSWITCH.  Shi ke da na’urorin da ke hada alaka tsakaninsu da mashin din ATM da ke girke a kofofin wadannan bankuna, da kuma kwamfutocinsu masu dauke da bayanan taskar ajiyar mutane.  Wannan kamfani na INTERSWITCH yayi fice kan wannan sana’a, kuma ba shi da abokin hamayya a harkar.  Duk bankunan Nijeriya da katinansa suke amfani wajen baiwa kwastomominsu damar cire kudi ta hanyar na’urar ATM.  Duk da yake nau’ukan mashin ya sha bamban tsakanin bankuna, amma dai kamfani daya ne ke tafiyar da al’amuran.

Matsalolin “ATM” A Nijeriya

Bayan kusan shekaru uku da fara amfani da wannan sabuwar hanya ta mu’amala tsakanin mutane da bankunansu, a yanzu matsaloli sun fara kunno kai babu kakkautawa.  Wannan ka’ida ce ta rayuwa, kuma babu makawa dole sai an samu hakan, musamman ta la’akari da inda wannan tsari ya samo asali, watau kasashen Turai.  A wadannan kasashe, wadanda tun sama da shekaru ashirin suke amfani da wannan tsari na ATM da ma wadansu tsare-tsare makamantansa, sun dade da samun ire-iren matsaloli makamantan wadanda suka fara kunno kai a Nijeriya.  Kamar dai ire-iren matsalolin da suka shafi wayar salula ce da kuma tsarin sadarwa ta wayar tarho da muke ta fama dasu a yanzu.

- Adv -

Matsalolin ATM a Nijeriya suna da yawa.  Kuma ga dukkan alamu ba iyakacinsu ba kenan, akwai saura (duk da yake ba fatan karuwarsu muke yi ba).  Mafi muni daga cikin su shine kana zaune kawai sai kaji sakon text ya shigo cikin wayar salularka, cewa: “ka cire naira dubu kaza daga taskar ajiyarka ta hanyar ATM, a rana kaza, da karfe kaza, a kuma gari kaza”.  Ta yiwu a lokacin da ka samu wannan sako ma baka taba amfani da katin ba, bayan ka karba.  Ko kuma kana amfani da katin, amma ba kai bane ka cire kudin; hasali ma dai watakil baka taba zuwa garin da aka ce ka cire kudinka ta ATM din da ke can ba.  Tirkashi!  Haka ya taba faruwa da wani bawan Allah dan  Gombe.  Babban yayansa da muke aiki wuri guda yake sanar dani cikin shekarar da ta gabata, cewa an aiko masa sakon text cewa ya cire naira dubu dari biyu cikin taskarsa ta hanyar ATM, a Legas.  A cikin sakon aka sanar dashi rana da kuma lokacin da aka ce ya cire kudaden.  Ai nan take hankalinsa ya tashi.  Domin bai taba zuwa birnin Ikko ba.

Na biyu kuma, tunda aka bashi katin,  bai taba amfani dashi ba balle ace ko sacewa aka yi.  A karshe ya duba katin da aka bashi, ga katin nan tare  dashi.  Amma yanzu banki na sanar dashi cewa an cire zunzurutun kudi har naira dubu dari biyu daga taskarsa.  Daidai lokacin da abin ke faruwa yake sanar dani, ya kuma ce zai je bankin don su daddale.  Ban san yaya suka kare ba.  Amma ban da tabbacin ya samu biyan bukata, kamar yadda zamu ji wani labarin makamancinsa nan gaba.  Shin wannan maita ne ko kuwa mene ne?  Ga kati na tare dashi, bai taba zuwa birnin Legas ba a rayuwarsa gaba daya, amma an ce ya cire kudade daga taskarsa.  Wannan lamari ya tayar masa da hankali sosai.

Labari na biyu makamancin wannan shi ma wani ma’aikacinmu ya sanar dani, don abin ya faru ga wani dan uwansa ne na jini, kamar dai labarin baya, kuma daidai lokacin da bankin ya yanke hukuncinsa mara dadin ji yake gaya mini.  Wannan dan uwan nasa ya saba amfani da katin, amma kuma badakalar da aka yi masa a Legas ne, bayan shi yana zaune ne a nan Abuja, ga katinsa na tare dashi.  Sakon farko da ya samu ana sanar dashi ne cewa ya cire naira dubu dari daga taskarsa, a safiyar da text din ta shigo.  Wannan abu ya faru ne da sassafe, tun bai fita aiki ba.  Aka ce a Legas ya cire kudaden, a ranar, da karfe kaza.  Yana cikin shan mamaki irin na bakin ciki, sai ga wani sakon ya sake shigowa, mai sanar dashi cewa ya kara cire naira dubu dari daga taskarsa!  Babban Magana, wai Dansanda ya ga gawar soja.

Wannan abu ya tayar masa da hankali inda nan take ya garzaya bankin don sanar da su.  Bayan sanar dasu, sai suka ce masa ya rubuta takardar korafi kan abinda ya faru, don hakan zai taimaka musu wajen warware matsalar.  Ya rubuta nan take ya basu.  Bayan wasu ‘yan kwanaki, sai suka aiko masa da wasika cewa sai dai ya dau na Annabawa, domin sun duba basu ga inda suke da laifi ko zama sanadi wajen faruwar wannan lamari ba.  Don haka sai dai kawai yayi hakuri. Ire-iren wadannan sun faru ga mutane da dama musamman masu ajiya a birane irin Abuja da Kano da Legas.

Bayan wadannan manyan matsaloli da makamantansu, akwai kuma ‘yan kananan matsaloli masu cin rai da wannan mashin na ATM ke dauke dasu.  Da farko dai, ba wani abin mamaki bane ka kwaso sauri a gaggauce don cire kudi, sai kawai a ce maka babu kudi a cikin mashin din.  A wasu lokuta kuma, sai ka sanya katin ka cire kudin, sai ya makale a cikin mashin din yaki fitowa.  Idan ma baka yi sa’a ba, sai ka bukaci kudin, a ce babu, kuma katin ya makale.  Wannan abu da cin rai yake, musamman idan hakan ya faru da kai ne cikin dare, kuma ranar asabar ko lahadi.  Sai dai kayi hakuri, don mai gadi bazai iya ciro maka katinka daga cikin wannan na’ura ba.  Wasu bankuna kuma ko da katin su kayi amfani sai sun cire maka naira dari biyu.  Idan ka je mashin din wani bankin kuma, da wannan katin, bankin zai cire naira dari, kamar yadda aka saba, bankinka kuma ya sake cire maka naira dari biyu.

Har wa yau, wata matsala da ba kowa ke son ta ba ita ce matsalar rashin kimar kudin da kake bukata.  Misali, idan kaje cire kudi, kana iya sanya yawan kudin da kake so (dubu daya, ko dubu biyu, ko dubu biyu da dari biyar ko makamantan hakan).  Kowane banki ka’idarsa dabam ne wajen baka damar cire kudi.  Wasu bankunan sai dai ka cire dubu daya ko biyu ko uku; ma’ana ba su da tsarin ‘yan dari biyar-biyar.  Ba za ka iya cire naira dubu biyu da dari biyar ba; ko dai ka cire dubu uku ne, ko kuma ka hakura da dubu biyu. Matsaloli ire-iren wadannan mai ajiya na iya hakuri dasu, amma irin wadanda bayani ya gabata kansu a sama ba kowa zai iya lamunce musu ba.  To meye dalilin da ke haddasa faruwar ire-iren wadancan matsaloli?

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.