Fasahar Intanet a Wayar Salula (2)

Kashi na biyu kan batun mu’amala da Intanet a wayar salula.

390

Shiga Intanet ta Wayar Salula

Da farko dai, kamar yadda muka sanar, zamu yi misali da wayar kamfanin Nokia ne, wacce ta fi shahara.  A Nokian ma zamu dauki Nokia 6230i, don kawo misali.  Idan ka tashi shiga Intanet ta hanyar wayar salula, abu na farko da za ka tabbatar shi ne ko wayar tana da ”Web”, don ba dukkan wayoyi bane ke da wannan tsari.  Don tabbatarwa, sai kaje Menu, ka gangara, sai ka ci karo da ”Web”, ko “WAP”, ko “GPRS Services” ko “Login”.  Duk wadannan kalmomi ne da wasu kamfanoni ke amfani dashi.  Amma kamfanin Nokia na amfani ne da kalmar “Web” a dukkan wayoyinta.

Don haka idan ka iso “Web” a Nokia 6230i, sai ka matsa shi, za ka fara cin karo da “Home”, wanda idan ka matsa zai kai ka zauren gidan yanan sadarwan Nokia ne, kai tsaye; sai “Bookmarks”, inda za ka iya adana adireshin gidajen yanan da ka ziyarta kuma suka burgeka; sai “Downloads”, inda za ka samu rariyar likau zuwa wuraren da za ka iya samun muryoyi (Tones) da labulen fuskar wayar salula (Themes) dsr; sai kuma “Last Web Address”, wanda shi ne zai kai ka gidan yanan sadarwan da ka ziyarta na karshe, a baya, idan ka yi hakan; sai “Service Inbox”, wanda bamu bukatarsa cikin bayaninmu; sai “Settings”, inda za ka tsara hanyoyin yawo ko lilo da tsallake-tsallake a wayarka; sai kuma “Go to Address”, inda za ka shigar da adireshin gidan yanan sadarwan da kake son shiga – shi zamu kira “address bar” a nan; sai na karshe, watau “Clear Cache”, ita “cache” jaka ce da ke adana dukkan aikin da kayi a wannan bangare na “Web” – duk inda ka ziyarta, da yawan shafukan da ka shiga.  Sai dai ba za ka iya ganin komai ba, don ita “clear cache” aiki daya kawai take yi, shi ne share wannan jaka gaba daya.

Da zaran ka gama dubawa ka tabbatar da cewa kana da alamar “Web” a Menu dinka, to sai mataki na biyu, shi ne samun kamfanin sadarwan da ke da tsarin Intanet a Network dinsu.

Wannan shi ne abin da galibin masu bugo mani waya basu fahimta ba sosai; kasancewar kana da wayar salula mai “WAP” ko “Web” a cikin jerin Menu dinta, ba shi ke nuna za ka iya lilo da tsallake-tsallake a ciki ba.  Sai kamfanin sadarwanka na da tsarin Intanet.  A Nijeriya ina ganin kamfanin MTN da Globacom ne kadai ke da wannan tsari.  Idan ka sayi katin SIM din MTN, misali, ka sanya ma wayarka, sai kaje ofishinsu kuma su tsara (configure) maka wayar.  Idan suka tsara wayar, za su aiko maka da sakonnin text guda biyu; na farko zai sanar da kai ne cewa ka adana (save) sakon da za a aiko maka nan ba da dadewa ba; na biyun kuma za a sanar da kai ne cewa an gama hada maka, kuma kana iya amfana da hanoyin mikawa da karban sakonni na MTN a ko ina kaje.

Amma akwai sabbin layukan MTN da ake sayarwa yanzu masu 0803, idan ka samu irinsu, to baka bukatan zuwa ofishinsu don su jona ka, muddin wayar salularka na da tsarin “WAP” ko “Web”.  Kana sanya katin SIM din kawai za ka ji sakonni sun shigo guda biyu, masu dauke da bayanan da na sanar a sama.  Sai ka adana su a cikin wayarka (ka aika dasu Saved Messages, don kada ka mance ka share su idan suna Inbox).  Amma idan layin Globacom kake dashi, za ka iya kiransu a layin “customer care”, ko kuma kaje ofishinsu.  Da zaran an gama tsara maka wayarka shikenan.  Sai lilo da tsallake-tsallake kawai.

- Adv -

Shawarwari

Kafin mu karkare, yana da kyau mai karatu ya fahimci wasu abubuwa dangane da abin da ya shafi yin lilo da tsallake-tsallake a wayar salula.  Da farko dai suna cajin kudi, ba kyauta suke bayarwa ba.  Duk da yake idan layinka na MTN sabon layi ne, ka iya sa’a cikin dare ka jima kana lilo ba a cire maka ko kwabo ba (na taba sa’an haka na kusan tsawon awa daya a layin Maman Sadiq).  Suna caji ne dangane da yawan haruffan da ka karanta ko ka bude, ba wai da yawan mintuna ko awannin da kayi kana lilo ba.

Idan ka budo shafuka masu hotuna ne, to za a caje ka sosai, domin hotuna sun fi haruffa yawa da nauyi, a ka’idar na’urar sadarwa.  Don haka idan ba ka bukatar wayarka ta riƙa budo maka hotuna a shafukan da kake yawo a ciki, sai kaje “Settings” a layin “Web”, don canzawa (Web = Settings = Appearance Settings = Show Images = No).  Idan ba wani tsananin bukata kake dashi ba wajen yin lilo a wayar salularka, ya zama sakonnin Imel kawai za ka riƙa dubawa ta nan, don kada cajin ya yawaita.  Idan kana son yin awa daya ko sama da haka, zan ba ka shawara da kaje mashakatar tsallake-tsallake kawai, watau “Internet Café”.  Bayan haka, duk sanda kayi lilo da tsallake-tsallake (browsing) ta wayar salularka, to sai ka gyatta saitin agogon wayar, idan ba haka ba, za ka ga ta cilla gaba da awa daya.  Me yasa?  Oho!

Daga karshe kuma, sai ka yawaita caja batirinka, domin duk lokacin da ka shiga “Web” ka fara yawo a duniyar gizo, wayarka na daukan kaso mai yawa wajen aiwatar da wani aiki da ya sha karfin mizanin batirin da take zuka a yanayin da ba wannan ba.  Sai a kiyaye.

Kammalawa

Wannan shi ne bayani a takaice.  Da fatan masu karatu sun gamsu.  Idan da akwai inda ba a fahimta ba, to a rubuto ta text ko Imel, don samun cikakken bayani.  Ina mika godiyata ga dukkan masu bugowa don gaisawa ko neman Karin bayani, musamman Malam Rabi’u Ayagi daga Kano, da Malam Muhammad Abbas Jos, da Malam Muntaka Dabo Zaria, da kuma Malam AbdusSalam, shi ma mazaunin Jos.

Na gode.  Na gode!

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.