Satar Zati a Kafafen Sadarwa na Zamani (11)

Kashi na 11 cikin jerin kasidun da muke kwararowa kan Satar Zati a kafafen sadarwa na zamani. A sha karatu lafiya.

115

Alamomin dake Nuna An Sace Zatinka (4)

Bayyanar Hotunan Batsa a Shafinka

Alama ta goma shabiyu ita ce, kayi ta samun kiraye-kiraye daga jama’a cewa ana ganin hotunan batsa fa a shafinka.  Mun shiga bangaren Dandalin Sada Zumunta kenan.  Wannan kan faru ne galibi a Dandalin Facebook, inda wani dan ta’adda zai haye maka shafi kai tsaye, yayi ta yada hotunan batsa, don yunkurin cin ma wata manufa.  Wannan nau’i na ta’addanci yana da bangarori biyu ne.  Akwai wanda ya shafi yaduwar kwayoyin cutar kwamfuta (Malware) da zasu iya harbar shafinka, sanadiyyar abota da wani wanda shafinsa ya harbu.  Ko kuma ka samu kanka cikin wani Zaure (Group) da aka harba da kwayar cutar kwamfuta.  Wannan zai sa duk mambobin Zauren su ma su harbu.  Wannan ya sha faruwa.  A yanayi irin wannan ba za a ace an sace maka zatinka ba.  domin a galibin lokuta ma zaka samu wani ne daga cikin mambobin Zauren yai ta shige shigen shafukan batsa a Intanet, a karshe abin ya iso ga Zauren da yake.  Ala ayyi halin dai, idan haka ta faru, nan take duk wanda ya harbu zai ta samun sakonnin batsa a shafinsa kai tsaye, ba tare da saninsa ba.

Bangare na biyu kuma shi ne wanda wani zai sace bayanan shafinka ko ta hanyar ganinsu, ko ka taba bashi, ko ya ji kana gaya ma wani, ko kuma, a karon karshe, yayi amfani da tsantsar hasashe ya gano.  Zai iya hawa shafin, saboda hikidin dake zauciyarsa a kanka, yayi ta loda hotonan batsa.  Duk abokanan zasu gani, amma idan ba yawan hawa shafin ma kake yi ba, baza ka taba sani ba, sai dai a nusar da kai.  Da zarar ka ji an kiraka ana cewa: “Wane me ke faruwa ne da account dinka?  Mun ga hotunan batsa birjik bila adadin…”, to alamar an sace zatinka kenan.

A nan aiki ya same ka ja, ko da kuwa abokananka sun san baza ka yi haka ba.  Na farko, ya jefa ka cikin tsantsar bakin ciki.  Na biyu, wadanda basu sanka ba a zahirin rayuwa – musamman masu ganin shafin a karon farko –  za su dauke ka mutumin banza.  Na uku, kafin ka iya kwace shafin daga hannunsa, in dai da gangar yayi, zai yi wahala.  Karshenta sai dai ka bude wani, ka sanar da jama’a cewa ga abin da ya faru.  Duk wanda ya ga abu kaza a shafinka, to, ba kai bane.  Wannan mummunar ta’ada ta fi faruwa ga mata, musamman matan aure.  Akwai lokuta da dama da aka bukaceni don neman mafita kan irin wannan matsala.

Sakonnin Neman Agaji Ga Abokanka

- Adv -

Alama ta goma sha uku ita ce, jama’a suyi ta kiranka cewa: “Wane me ya faru ne?  Mun ga ka aiko sako cewa a taimaka maka da kudi kana cikin kunci a wani wuri…”  Da zarar ka ji haka, to, lallai wani kato ya haye kan shafinka, ko ya kwafi irin shafinka, ya dora bayananka, dauke da hotunanka, don sace maka zatinka.  Irin wannan ya sha faruwa ga mutane masu mutunci, musamman Malamai dake Arewacin Najeriya.  A lokuta da dama an sha sace shafukansu, a rika bibiyan abokansu ana neman su aiko kudi ta hanyar aika katin waya, saboda neman fita daga wani kunci da suka samu kansu a ciki, wai.

Wasu kuma kan yi garkuwa da shafin ne, su ce sai an basu dubu kaza, kafin su saki.  Ka ji iskanci irin na dan ta’adda.  Babbar matsalar ma ita ce, babu tabbacin idan an basu kudin za su saki shafin.  A takaice dai idan irin haka ya faru, sai dai ayi amfani da dabarun kwarewa a fannin sadarwa wajen kwato shafin ko kuma bude wani, idan abu ya gagara.  Bayan nan, a sanar da jama’a cewa duk wanda aka bukaci ya ba da wasu kudade da sunan neman agaji, to, kada ya bayar.  Ba asalin mai shafin bane.

Bayyanar Bayanai ko Hotunan ‘Yan Ta’adda

Alama ta goma sha hudu ita ce, kaga hotuna ko sakonni masu alaka da ta’addanci ko ‘yan ta’adda a shafinka, masu nuna lallai kaima kana tare dasu, ko kana yaba abin da suke yi.  Wasu ‘yan ta’adda kan yi wannan saboda tsabar kyashi ko kishi mai alaka da ilimin addini.  Babbar manufar ita ce don a nuna wa duniya cewa Malam wane, ko Sheikh wane, dan ta’adda ne, ko yana tare da ‘yan ta’addan duniya.   Yunkuri ne na hada shi da jama’a ko da jami’an tsaro, saboda watakila an buga dashi wajen tattaunawa an kasa.

Masu aikata wannan ta’ada dai suna bin dayan hanyoyi biyu ne. Ko dai su sace shafin gaba daya, ta yadda za su samu daman yada abin da suke so ga dukkanin abokansa da mabiyansa, cikin sauki ba tare da matsala ba.  Hanya ta biyu kuma ita ce, idan an kasa samun hawa shafin da kwacewa, sai a kirkiri wani shafi na musamman mai dauke da sunansa, da lakabi ko alkunyansa, da irin sakonnin da yake rubutawa a shafinsa na asali, sannan a ci gaba da dora irin shegantakar da ake bukata.  Ko ma dai da wace hanya aka yi amfani, manufar dai iri daya ce.

Wadannan, a takaice, su ne alamomin da ake iya gane an sace wa mutum zatinsa ta kafafen sadarwa na zamani.  Don haka sai a kiyaye.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.