Tsarin Fasahar Sadarwar Rediyo a Kimiyyance (2)

Kasida ta biyu cikin jerin kasidun dake mana bayani kan hakikanin fasahar dake samar da siginar rediyo. A sha karatu lafiya.

180

“Haske” a Al-Kur’ani

Kamar yadda na sha maimaitawa a baya, cewa Al-Kur’ani mai girma ba littafin kimiyya da fasaha bane, littafin shiriya ne da Allah ya aiko shi ga bayinsa don fayyace musu hakikanin abin da yake son suyi masa, wato BAUTA kenan.  Wannan yasa Allah ya cika littafin da nau’ukan ilmomi da dama, wadanda kwakwalwa da binciken dan adam ba su iya kaiwa makurarsu balle su tantance su gaba daya.  Babu wani nau’in ilmi da babu shi a cikin Al-Kur’ani.  Muddin baka gani ba, to, karatunka ne bai kai ba.  Amma idan ka samu wadanda suka sani, tabbas za su fitar maka da komai dalla-dalla sanka-sanka.

Daga cikin hikimomin hakan shi ne, don bawa yasan Allah hakikanin sani, da cikan mulkinsa da ikonsa, da kuma gamewar ilminsa gaba daya.  Duk wani abin da ka gani na ilmi kowane iri ne, ribar kafa ce.  Amma manufar ita ce a shiryar dakai ga abin da zai fahimtar da kai hakikanin Mahaliccinka, da hakikanin abin da yake bukata daga gareka.   Bayanai kan haka sun gabata a cikin doguwar kasidarmu mai take: “Tsakanin Kimiyyar Kur’ani da ta Zamani: A Ina Aka Hadu?”, shekaru kusan bakwai da suka gabata.

- Adv -

Allah ya ambaci nau’ukan haske guda biyu a littafinsa, dangane da asalinsu.  Wannan zance na cikin Suratu Yoonus, Aya ta 5, inda Allah ke cewa: “Shi ne wanda Ya sanya muku Rana, babban haske, da Wata mai haske…”   (Sura 10, Aya 5).  Abin da bangaren wannan aya ke nuna mana shi ne, da Rana da Wata duk suna da haske dake samuwa daga gare su.   Sai dai kuma Allah ya bambanta sunayen hasken nasu a kalmomi biyu; a harshen Hausa duk ma’ana daya muke basu, saboda rashin yalwar kalmomi irin na Larabci.   Ya ambaci hasken Rana da suna “Ad-Dhaw’u,” hasken Wata kuma ya ambaceshi da suna “An-Noor.”   Malamai suka ce bambancin dake tsakaninsu shi ne, shi hasken rana an kira shi da “Ad-Dhaw’u” ne saboda abubuwa biyu; hakikanin haske ne dake da asali daga jikin Ranar.  Dalili na biyu kuma, haske ne mai dauke da zafi.

A bangaren Wata kuma, shi ma Allah ya ambaci haskensa da suna “An-Noor” ne saboda dalilai biyu, kamar yadda Malamai suka ambata.  Dalili na farko shi ne, haske ne wanda ake danganta wa Wata, amma ba asalin haskensa bane; haske ne dake bijiro masa daga hasken Rana.  Idan mai karatu ya dubi taswirar yadda Rana da Wata da wannan duniya tamu suke shawagi, zai ga cewa kowanne daga cikinsu yana shawagi ne a falakinsa.  Allah ya ambata mana haka a cikin Suratu Yaseen.  Sannan ba suna shawagi bane a jiha ko bangare iri daya, a lokaci daya, a yanayi daya ba, a a.  Kowanne na shawagi ne a tsarin da Allah yayi masa dangane da yanayin mahalli ko falakinsa.  A galibin lokuta Rana da Wata kan kasance a jiha dake da akasi da juna, sai ya zama Rana na hasko Wata ne kai tsaye.  Wannan haske dake darsowa daga jikin Rana shi yake darsuwa a jikin Wata, shi kuma Wata, yayin da duniyarmu ta fuskanto shi bayan ta juya wa Rana baya, sai ya hasko mata hasken da ya darsano daga jikin Rana.  Dalili na farko kenan.

Dalili na biyu kuma Malamai suka ce an ambaci hasken Wata da suna “An-Noor” ne saboda haske ne mai sanyi, ba kamar hasken Rana ba.  Dalilin kasancewarsa haske mai sanyi shi ne, don ba asalin haskensa bane.  Jikin Wata kamar gilashi ne; duk abin da ya hasko shi, nan take yake haskaka shi kan abin da ko jihar da ke fuskantarsa a akasi.  Wadannan nau’ukan haske guda biyu suna cikin nau’ukan hasken da dan adam ke iya ganinsu da idanunsa, wato “Visible Light.”

Wadannan su ne takaitattun bayanai dake mana sharan fage kan haske da abubuwan da suka shafe shi.  Hakan zai taimaka mana wajen tantance hakikanin bayanan da za su biyo baya kan tsarin aikawa da karban sautin shirye-shiryen gidajen rediyo da talabijin, da yadda suke bayyana a akwatunanmu, a yayin da ake yada su.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.