Satar Zati a Kafafen Sadarwa na Zamani (10)

Kashi na 10 cikin jerin kasidun da muke kwararowa kan Satar Zati a kafafen sadarwa na zamani. A sha karatu lafiya.

156

Alamomin dake Nuna An Sace Zatinka (3)

Rashin Samun “Bill” Daga Hukumar Lantarki Dsr

Wannan ita ce alama ta takwas, wacce ta kunshi rashin samun takardar biyan kudin wuta ko gas, a kasashen dake amfani da wannan tsari.  Misali, hukumomin dake ba da makamashin lantarki da makamashin gas na dafa abinci kan aiko wa masu hulda dasu takardar biyan kudi a duk wata, wato: “Monthly Bill” kenan.  Domin a galibin ire-iren wadannan kasashe, gidajen mutane a jone suke da bututun gas na dafa abinci.  A duk karshen wata, kamfanonin kai aiko da “Bill” don a biya abin da aka sha na wuta ko gas.  Rashin zuwan wannan “Bill” na tsawon lokaci, musamman watanni biyu ko sama da haka”, alama ce dake nuna wani dan ta’adda ya sauya adireshin gidanka, saboda sace maka zati da yayi yana amfanuwa da wata fa’ida da har yanzu mummunan tasirinta bai bayyana maka ba.  Wannan a kasashen da suka ci gaba kenan.

Amma mu a wajenmu nan, rashin zuwan Bill ma ai kamar sauki ne gare mu.  Sai mu dauka watakila an mana rangwame ne.  Don haka ba za mu damu ma ba.  Amma wannan kuskure ne.  A ka’ida dole ne mutum ya kira su ko yaje ofishinsu, yaji meye dalilin da ya sa ba aiko masa ba.  Zai iya yiwuwa wani ya canza adireshin gidansa da nashi, amma shi bai sani ba.  Wannan kan faru sosai a kasashe irin su Amurka, da Ingila da sauran kasashen da suka ci gaba.

Hana Bashin Banki Sanadiyyar Bashin Baya Da Baka San Da Shi Ba

A kasashen Turai da Amurka, akwai bankuna da sauran kamfanonin hada-hadar kudi masu bayar da bashi, ya Allah na hajoji ne ko na tsabar kudi.  Idan baka biya wanda ake binka a baya ba, ba a baka sabo.  To, a wasu lokuta ‘yan ta’adda kan sace bayanan mutane, sai suci bashi da sunansu, da adireshinsu, ba tare da sanin masu taska ko katin ba.  Sai ka je kawai za ka karbi bashi, sai ace maka ai ka karbi bashi lokaci kaza, na tsabar kudi kaza, baka biya ba.  Kana jin haka, to, alamar wani dan ta’adda ya sace maka bayananka kenan, ya kuma ci bashi da sunanka.

A nan kuma aiki ya same ka.  Dole ne ka tabbatar musu cewa lallai ba kai bane ka karbi wannan bashi.  Kuma ma, baka san dashi ba.  Daga nan za a gudanar da bincike.  Ta yiwu ya karbi wannan bashi ne ta hanyar shafinsu na Intanet, ko ta hanyar kira a waya da sunanka, ko ta hanyar fasahar gajeren sakon waya, wato: “USSD”, kamar yadda wasu bankuna ke bayar da dama a Najeriya.  Ka ga kenan ashe ba bankin yaje ba.  Baza ka samu kubuta ba har sai ka gamsar da masu bankin ko kamfanin cewa wanda ya karbi wancan bashi na farko baka san dashi ba, kuma ga hujjoji, ba wai da fatan baki kawai za ka fada su amince da kai ba.  Wannan ita ce alama ta tara.

- Adv -

Sanarwar Sauyin Adireshi Daga Gidan Waya

A gidajen waya inda ake karba da aika wasiku rubutattu, wato: “Post Office”, kowane mai rajista a wurin yana da adireshin gidansa da wurin aikinsa.  Domin a kasashen da suka ci gaba, har gida ana kawo maka wasika.  Haka idan ma kana son aikawa, a titin unguwarku akwai akwatin karfe an kafe, inda za ka zura wasikar da kake son a aika ma wani.  Ma’aikatan hukumar ko kamfanin za su zo su kwashe.  Ba Kaman nan kasashenmu da dole sai kaje ofishinsu sannan za ka iya daukan wasikar da aka aiko maka ko aika ma wasu ba.

To, a ire-iren wadannan kasashe, idan ka sauya adireshinka, nan take za a aiko maka sakon tabbatarwa.  Amma idan kawai kana zaune sai kaga sako daga Gidan Waya cewa: “An tabbatar da sauyin adireshin da ka bukata!”, kai tsaye, kuma ba kai ka bukaci hakan ba, to, alamar wani dan ta’adda ya mallake taskarka kenan.  Idan baka garzaya ka sanar dasu ba, dukkan sakonninka can za a rika kaisu.   Wanda kuma ka san duk wanda yayi wannan, ba wai hakikanin wasikun ne damuwarsa ba, akwai abin da yake hari daga bayananka.  Wannan ita ce alama ta goma kenan.

Karuwar Haraji

Alama ta goma shadaya ita ce, ya zama kudin harajin da kake biyan hukuma yana karuwa, ba tare da karuwan kudaden shiganka ba.  Wannan na faruwa ne a kasashen Turai da Amurka, inda hukuma ta san kudaden da kake samu, wanda kuma daga nan ne take kiyasta abin da za ka rika biya na haraji.  Galibin lokuta kowa ya san abin da yake biyan hukuma a matsayin haraji.  Idan ya samu karuwan kudaden shiga sanadiyyar samun wani aiki kari a kan wanda yake yi, abin da hukuma ke cire masa na haraji zai karu.

Amma wasu lokuta ‘yan ta’adda kan sace bayanan mutane, sai su kara bayanan harajinsu a kan na wanda suka sace bayanansa.  Sai ya zama abin da ke kan sunansa na kudaden a zahiri yake samu a duk wata ko shekara, ya karu kenan.  Don nan haka nan take sai hukuma ta kara abin da zai rika biya na haraji.  Kawai kana zaune a gida sai ka ga hukuma ta kara maka haraji ba tare da wani karuwar kudaden shiga ba.  Idan haka ya faru, to, wani ya sace zatinka kenan, ya dora kudaden shigansa a kan naka.  Ya zama abin da ya kamata a rika cire masa na haraji ya dawo kanka kenan.  To ta yaya zai iya dora nauyinsa a kanka?

A al’ada akwai abin da ake kira: “Tax Identification Number” ko “TIN” a gajarce.  Lambobi da hukumar tattara haraji ke baiwa ma’aikata (A Najeriya ma akwai wannan tsari).  Kowane ma’aikaci lambarsa ta sha bamban da na dan uwansa. Kamar dai lambar wayar salula ce; kowa tasa daban take.  Idan kayi sakaci wani ya sace wadannan lambobi naka, nan take zai rika amfani dasu a duk inda aka bukaci ya bayar da lambar harajinsa ne.  Wadanda suka bukaci lambar ba wai tantancewa za su yi ba, a a, kawai zasu alakanta lambar ne da sunansa, sannan su mika wa hukumar tattara haraji.  Ita kuma da wadannan lambobi za ta yi amfani wajen zaftare harajin.  Ba ruwanta da duba sunayen da aka alakanta su da wadannan lambobi.  Wannan ke nuna cewa duk wanda ya bayar da lambarka a matsayin tasa ce, a karshen wata, kai za a rika cire wa haraji maimakon shi.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.