Kasashe Masu Karfin Nukiliya a Duniya (2)

Ci gaba da bayani kan kasashe masu karfin nukiliya a duniya. A sha karatu lafiya.

4,340

Kasar Sin

Ita ce cikon ta biyar a jerin kasashen da ake kira The Nuclear Club.  Su ne kasashen da suka mallaki makamin nukiliya tun kafin a kulla yarjejeniyar hana yaduwa balle kera makamin a duniya.  Kasar Sin ta mallaki nata makamin ne a shekarar 1964, ta kuma yi gwajin farko wanda ta sanya wa suna “596’ ne cikin wannan shekara.  Ita ce kasar Asiya ta farko da ta fara mallakan wannan makami, kuma ita ma tayi haka ne don a san da zamanta a wannan nahiya – musamman ganin yadda kasashe irinsu Amurka da Rasha ke ta fankama don mallakan wannan makami, a wancan lokaci.  Kasar Sin ta kuma yi gwajin makamin nukiliya nau’in H-Bomb a shekarar 1967, daidai wani bigire mai sun Lop Nur.  A halin yanzu kasar Sin ta mallaki makamin nukiliya guda dari da sittin (160), dari da talatin cikinsu masu rai ne, a farke suke!

Kasar Indiya

A farkon al’amari, duk kasashen duniya sun san kasar Indiya a matsayin kasa ce mai sarrafa makamashin nukiliya don samar da wutar lantarki, wanda wannan na cikin abin da Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) ke lura da bunkasa shi.   Kasar Indiya ta fara mu’amala da fasahar Nukiliya ne tun wajajen shekarar 1970s, sanadiyyar samar da wutar lantarki da take yi ta amfani da makamashin sinadaran Nukiliya.  Amma kuma, abin mamaki, taki ta sanya hannu kan yarjejeniyar hana kerawa da yada makamin nukiliya, kamar sauran kasashe, duk kuwa da dadewa da tayi tana amfana da makamashin, da kuma ganin cewa wannan shi ne abin da dama ake so, ba wai kera makamin ba.  Ashe da biyu, wai an daki biri da rani.

Cikin shekarar 1974 kasar tayi gwajin wani ‘halattaccen makamin nukiliya’, wanda mizani da tsarinsa bai kai sanannen makamin nukiliya ba.  Ta sanya wa wannan makami suna ‘The Smiling Buddha’.  Wannan abu da kasar Indiya tayi ya haddasa cece-kuce tsakanin kasashen duniya, na yadda tayi dabarar kera makamin nukiliya sanadiyyar amfani da makamashin da take yi.  Sai a lokacin aka lura cewa, ashe bata sanya hannu kan yarjejeniyar hana kera wannan makami ba, balle a tuhume ta.  Tayi dabara kenan!

Alal hakika kasar Kanada tafi kowa bakin ciki kan abin da kasar Indiya tayi, domin ita ce ke sayar wa kasar da sinadarai tare da fasahar makamashin don samar da wutar lantarki.  Babban abin da ya zaburar da ita, kamar sauran kasashe, shi ne ganin cewa kasashe irin su Sin da Rasha sun sanya ta a tsakiya.  Don haka ita ma ta kama dahir.  Cikin shekarar 1998 tayi wani kyakkyawan gwaji kan wani makamin nukilya mai rai, karkashin wani shiri mai suna ‘Operation Shakti’.   Da tafiya tayi nisa, ya tabbata cewa kasashen Yamma sun yi na’am da wannan dabara da kasar Indiya tayi, don kasar Amurka ta kulla yarjejeniyoyi da ita cikin shekarar 2006.

Wannan tasa masu lura da harkokin siyasar duniya ke ganin wata alama ce da ke nuna cewa an shigar da ita cikin kasashe masu hakkin mallakar makamin nukiliya na halal (Nuclear Club).  Har wa yau, cikin shekarar ne dai Shugaban Amurka George W. Bush ya ambaci kasar Indiya a matsayin wata “Dattijiyar Kasa mai Karfin Nukiliya”.  Wadannan yarjejeniyoyi da aka kulla tsakanin Amurka da Indiya sun samu tabarrakin dukkan Majalisun kasar Amurka baki daya.  A halin yanzu kasar Indiya na da makamin nukiliya da adadinsu ya kai dari da arba’in, kuma masu rai ne.

Kasar Pakistan

Kowa ya san yadda aka raba kasar Indiya gida biyu bayan samun ‘yancin kai, lokacin da kasar Pakistan ta samu nata bangare, kasancewar galibinsu Musulmi ne.  Tun sannan suke ta fafatawa a tsakaninsu, musamman kan bodan Kishmeer da ke tsakaninsu.  Don an rabu ne dutse a hannun riga. Don haka kasar Pakistan na jin makwabciyarta ta mallaki makamin nukiliya, sai ita ma ta sha alwashin lallai sai ta mallaka.  Firanministan kasar Pakistan na wancan lokaci, Zulfiqar Ali Bhutto, ya fara wannan alwashi cikin shekarar 1965, cewa ‘muddin kasar Indiya ta mallaki makamin nukiliya, to mu ma sai mun mallaki namu; ko da kuwa hakan zai kai mu ga cin ciyawa ne (saboda talauci)’.  Kamar kasar Indiya, ita ma Pakistan ta fara ne daga samar da makamashin wutar lantarki ta amfani da makamashin nukiliya.  Cikin shekarar 1970 ta kafa cibiya kan makamashin nukiliya don samar da wutar lantarki.  Akwai alamun ta san abin da makwabciyarta ke yi a daidai wannan lokaci.  Don cikin wadannan shekaru (1970s) ne ita ma ta fara hakilon samo fasaha iri-iri daga kasashen Yamma, don wannan aiki a boye.  Wanda ke da alhakin wannan aiki kuwa shi ne Dakta Abdulqaadir Khan, wani kwararren injiniya kan kimiyyar karafa (Metallurgist).  Yayi aiki a wata masana’antar makamashin nukiliya da ke kasar Nedalands a shekarar 1972, inda hukumomin kasar suka fara tuhumarsa da aikin leken asiri don satar fasahar makamin nukiliya a madadin kasarsa.

To amma bayan shekaru biyu (1974), sai ya bar kasar, don dawowa gida Paskitan.  Hukumar Nedalands ta so ta kai shi kotu kan wannan tuhuma da take masa, amma sai Hukumar Leken Asirin kasar Amurka, wato CIA, ta bata tabbacin cewa ba matsala, suna lura da jujjuyawarsa cikin abin da yake yi.  Dawowarsa gida ke da wuya, sai shugaban Pakistan na wancan lokaci, wato Muhammad Zia’ul Haqq, ya bashi matsayin mai lura da wannan shiri na samar da makamin nukiliya ga kasar gaba daya.  Yayi yawace-yawace zuwa wasu kasashe don wannan aiki.  Akwai kuma tabbaci cewa kasar Sin ta taimaka wa Pakistan wajen wannan shiri.  Wannan ya taimaka musu sosai, inda suka samu mataki na farko na wannan makami daidai shekarar 1980.

- Adv -

Har zuwa wannan lokaci, kasar Pakistan bata rattafa hannu kan yarjejeniyar hana kera makamin nukiliya a duniya; ita ma ta kame, kamar yadda makwabciyarta tayi a farkon lamari.  Har zuwa shekarar 1990, lokacin da kasar Amurka ta tabbatar wa duniya cewa lallai kasar Pakistan ta mallaki wannan makami, wanda hakan ya sa ta yanke dukkan wata alaka da ta shafi harkar soji da tattalin arzikin kasa a tsakaninsu.  Don haka, kasar Indiya na kaddamar da gwajin da tayi cikin shekarar 1998, sai kasar Pakistan ta nuna wa duniya cewa ita ma fa ta kawo.  Nan take ta kaddamar da nata gwajin na nukiliya, wanda tayi a saman wani tsauni da ke lardin Chagai.  Ta kuma sanya wa wannan makami suna Chagai-1.  A halin yanzu duk duniya ta sheda cewa kasar Pakistan ta mallaki wannan makami, kuma zuwa yanzu, tana da adadin makamin nukiliya masu rai, masu jiran ko-ta-kwana, guda sittin (60).

Kasar Koriya ta Arewa

Sabanin kasashen Indiya da Pakista, kasar Koriya ta Arewa mamba ce cikin kasashen da suka rattafa hannunsu kan yarjejeniyar hana yaduwar makamin nukiliya a duniya, amma da ta ga baza ta sha ba kan manufarta da ke boye, sai ta fice daga kaidin wannan yarjejeniya cikin shekarar 2003.  Abin da ya haddasa hakan kuwa shi ne zarginta da kasar Amurka tayi, cewa lallai tana ci gaba da inganta makamashin Yuraniyon ta karkashin kasa, wanda hakan ya sha bamban da manufar samar da wutar lantarki.  Ana shiga shekarar 2005 sai kasar ta ayyana cewa ta mallaki wannan makami na nukiliya.  Amma kwararru kan harkar suka ki amincewa da wannan ikirari nata.  Don haka sai ta gudanar da gwajinta na farko cikin shekarar 2006, sanadiyyar matsin-lamba da kasar Amurka ta ke mata ta karkashin kasa.  Ta sanya wa wannan gwaji nata suna “The Beginning”. 

Da farko babu wanda ya yadda cewa gwajin makamin nukiliya ne, saboda makamashin da makamin ya fitar sanadiyyar gwajin bai kai na wadataccen makamin nukiliya ba.  To amma daga baya, sai kwararru kan nukiliya da ke kasar Amurka suka tabbatar da cewa lallai makamin nukiliya ne, bayan sun yi nazarin hayakin da makamashin ya haifar lokacin gwajin, wanda na’urar tauraron dan Adam ta kasar ta dauko musu daga sararin samaniya.  A yanzu kasar Koriya ta Arewa ta mallaki wannan makami har guda goma (10), ta kuma kaddamar da gwajinta na farko ne cikin teku.

Kasar Isra’ila 

Na tabbata duk masu karatu zasu yarda idan nace kasar Isra’ila na cikin kasashen da ba kowa ya san halin da suke ciki ba, ta kusan dukkan bangarorin rayuwa kuwa.  Wannan haka yake, kuma har zuwa yanzu, Hukumomi a birnin Tel Aviv sun ki fitowa su fadi matsayinsu kan rade-radin da ake ta yi cewa kasar ta mallaki makamin nukiliya tun wajajen shekarar 1979.  Da farko dai, kasar Isra’ila ba mamba bace cikin yarjejeniyar hana kerawa da yada makamin nukiliya.  Ma’ana bata rattafa hannunta kan wannan yarjejeniya ba, sam.  Wannan ke nuna cewa ba da banza ba taki rattafawa.  Na biyu, akwai rade-radin da ke nuna cewa tayi gwajin makamin nukiliyarta ta hadin gwiwa ne da kasar Afirka ta Kudu, wacce tuni ta wargaza nata shirin ba tare da matsin-lamba daga wata kasa ba.  Wannan gwaji sun yi shi ne cikin shekarar 1979.  Na uku, akwai shiri mai rikitarwa da kasar ta fara yi cikin shekarar 1960, kan abin da ya shafi mallakar makamin nukiliya.  Amma da Yizthak Rabin yaje ziyarar aiki a matsayinsa na Ambasadan kasar Isra’ila zuwa Amurka, aka tambayeshi kan wannan shiri da kasarsa ke yi, sai yace “mallakar makamin kawai ba tare da gwaji ba, baya nuna cewa an mallake shi, sai an yi gwaji sannan hakan zai nuna ana da wannan makami”.  Wannan kawai hargowa ce irin ta harshen diflomasiyya.  Kuma galibin masu lura da harkokin siyasar duniya sun dauki wannan batu a matsayin tabbaci ne, duk da kwane-kwanen da yayi ta yi.

Dalili na hudu da ke nuna lallai kasar Isra’ila ta mallaki wannan makami shi ne samuwar masana’anta ko cibiyar binciken nukiliya a garin Dinoma, wanda a farko hukumomin kasar suka karyata, suka ce masana’antar saka tufafi ce, ba ta nukiliya ba.  Amma a karshe bayanai sun nuna ba haka bane, lokacin da wani kwararre kan harkar makamin nukiliya na kasar mai suna Mordechai Vanunu ya fasa kwai cikin shekarar 1986, inda ya tabbatar wa duniya cewa lallai kasarsa ta mallaki wannan makami, kuma shi ma ma’aikaci ne a wannan masana’anta.  Jaridar The Sunday Times da ke kasar Ingila ce ta dauki wannan labari, kuma duk duniya ta karanta.  Amma wani abin mamaki shi ne, Hukumar Isra’ila taki yin bayani kan haka, sai ma kama wannan bawan Allah tayi, ta yanke masa hukuncin zama gidan kaso na tsawon shekaru goma shatakwas, da sunan wai yaci amanar kasa.

Haka ma kwararrun masana fasahar nukiliya a Amurka da ke karkashin Kungiyar Masana Kimiyya ta Amurka, wato Federation of American Scientists (FAS), sun tabbatar da manyan alamu da ke nuna cewa Isra’ila na kera makamin nukiliya.  Wannan kungiya ta samu wannan tabbaci ne daga hotunan da na’urar tauraron dan Adam na kasar Amurka yai ta daukowa daga sararin samaniya, mai nuna manyan motocin daukan mizail, wanda shi ne sanannen kwanson da galibi ake amfani dashi wajen safarar wannan makami, tare da wasu mazubai irin na diban makamai (Weapon Bunkers), a wasu wurare da ke nuna bigiren atisaye ne na wucin-gadi.  A nasu kiyasin, sun nuna cewa kasar ta mallaki a kalla abin da ba ya kasa saba’in zuwa dari biyu (70 – 200), na makami mai rai.

Ana cikin haka sai ga dalili na karshe, ranar 26 ga watan Mayu na wannan shekara, inda tsohon shugaban kasar Amurka Jimmy Carter ya tabbatar wa duniya a taron da yayi da ‘yan Jaridu a birnin Wales, cewa lallai kasar Isra’ila ta mallaki wannan makami na nukiliya.  Ya kuma nuna cewa a halin yanzu, Isra’ila na da kawunan makami masu rai na nukiliya, guda dari da hamsin (150).  Idan muka dubi dalilan da ke sama, da ikirarin da wasu masana suka ta yi, za mu ga cewa babu warwara tsakanin saba’in zuwa dari biyu, da kuma adadin dari da hamsin da Jimmy Carter ya bayar.

Wadannan su ne kasashe masu karfin makamin nukiliya a duniya a halin yanzu.  In Allah Ya yarda a mako mai zuwa za mu kawo bayanai kan makamashin nukiliya; ma’ana, yadda ake sana’anta sinadaran da ake kera wannan makami dasu, wajen samar da wutar lantarki.

A ci gaba da kasancewa tare damu.

- Adv -

You might also like
3 Comments
 1. Abubakar Umar says

  Allah ya saka da alkhairi, lallai muna faidantuwa.

 2. ali umar says

  Allah yasaka.

 3. Abubakar umar says

  Salam, Baban sadiq ina maka fatan Alheri kai da iyalanka.

  TAMBAYA
  Shin baban Sadiq Kasar IRAN bata cikin jerin kasashen da suka mallaki makamin NUKILIYA ne? Naga bakasata acikin jerin kasashen ba. Ko kuma su nasu makamin da ake tasa musu takunkumi akansa ba nukiliya bane?

  Daga ma ‘abocin bibiyar rubutunka akai akai
  Abubakar Umar Azare, Bauchi state.

Leave A Reply

Your email address will not be published.