Satar Zati a Kafafen Sadarwa Na Zamani (2)

Kashi na biyu cikin jerin kasidun dake bincike kan Satar Zati a kafafen sadarwa na zamani.

260

Ma’ana da Asalin Kalmar “Identity Theft”

Wannan kalma dai asalinta tagwayen kalmomi ne.  Kalmar farko ita ce: “Identity” wadda ke nufin: “Zati” ko “Hakikanin abu.”  Kalma ta biyu kuma ita ce: “Theft”, wacce ke nufin “Sata.”  Wato “Satar Zati” Kenan.  Amma a fannin kimiyyar sadarwa na zamani, idan aka ce: “Identity Theft”, ana nufin: “Yin amfani da bayanai ko sunan dake wakiltar wani mutum ko hukuma ko ma’aikata, da gangan, don cinma wata manufa mummuna, ba tare da sani ko yardarsa ba.”  Wanda ke aiwatar da irin wannan nau’i na ta’addanci kuma shi ake kira: “Identity Thief,” wato: “Barawon Zati.”  Kafin muci gaba, zai dace mu fayyace wannan ma’ana dalla-dalla.

Abu na farko shi ne “Yin amfani da bayanai ko suna…”.  Hakan nufin an mallaki bayanai ko sunan Kenan, ta hanyar kutse ko zamba cikin aminci, ko kuma samuwar bayanan ko sunan a fili ba tare da wani kaidi ba.  Abu na biyu shi ne, wadannan bayanai ko sunaye, na “…wakiltar wani mutum ne (namiji ko mace), ko hukuma (ta gwamnati a kowace kasa), ko ma’aikata (mai zaman kanta)…”  Ma’ana, suna da bayanan da aka samu, ko aka sace ta hanyar dandatsa wato kutse, na wani mutum ne, ko wata hukuma ta gwamnati ko wata ma’aikata ko kamfani.  Abu na uku shi ne, “…da gangan…”  Wato ba kuskure aka yi ba, a a. Abu ne da aka yi da manufa.  Abu na hudu shi ne “…don cinma wata manufa mummuna…”  Ma’ana, dalilin da yasa aka mallaki wadancan bayanai shi ne don cinma wata manufa ta musamman, ba wai kawai an gani bane ko mallaka irin ta al’ada.  Sai abu na karshe, shi ne “…ba tare da sani ko yardarsa ba.”  Wannan ke nuna ko da wanda aka mallaki bayanansa ya san an mallaka, amma muddin ba da amincewarsa bane, abin ya zama kwace Kenan, wato mafi muni daga cikin nau’ukan sata Kenan.  Idan kuma bai sani ba, abu yayi biyu, wai shege da hauka.  Wannan, a fayyace, ma’anar “Satar Zati” Kenan, ko “Identity Theft,” a harshen turancin sadarwa na zamani.

Wani zai ji abin bambarakwai, wai namiji da sunan Rakiya.  Ba wai kai bane za a sace, wasu bayanai ne dake wakiltarka, wadanda a duk inda aka gansu, to, kamar an ganka ne.  Idan bayar dasu aka yi don wata bukata, to, kamar kaine ka bayar dasu.  Idan shigar dasu aka yi wani wuri don neman izni, kamar kaine ka nemi iznin.  Idan mika su aka yi don biyan wasu kudade na wasu hajoji, kamar kaine ka mika su.  Idan kisa aka yi, ko duk wani nau’in ta’addanci a kasa, to, kamar kaine kayi wannan kisa ko ta’addancin, kai tsaye.  Don haka, idan jami’an tsaro suna neman wanda yayi wancan aiki, kai tsaye kai za a nema.

Wannan kalma ta “Identity Theft” an kirkireta ne a shekarar 1964, sadda wasu ke amfani da sunayen mutane don cinma wata manufa a kasashen Amurka da turai, ta hanyar sata ko zamba cikin aminci.  Wannan tsari na satar zati har yanzu ana amfani dashi a wannan kasa tamu ko ma ince kasashe masu tasowa.  Amma ta ragu matuka a kasashen da suka ci gaba.  Saboda galibin jama’a an taskance bayanansu wuri daya.  Amma a kasashenmu har yanzu ba abin mamaki bane kaji ance an kama wani da yake ikirarin shi ne wani babban jami’in gwamnati.  Misali, cikin watan Maris na wannan shekara aka kama wani bawan Allah dake zambatar mutane, yana cewa shi ne shugaban hukumar EFCC, wato hukumar dake lura da yaki da ta’annutin kudin gwamnati.

Nau’ukan Bayanai

Wadannan bayanai dake wakiltarka a kafafen sadarwa na zamani dai suna da yawa.  Kuma muddin aka sace su, to, kamar hakikaninka ne aka sace.  Daga cikinsu akwai sunanka.  A wasu lokuta ma ba wai shafinka za a kwace ba, za a yi amfani da sunanka ne kawai a bude wani shafi, a dora hotonka, sannan a aikata ta’addanci da wannan suna.  Daga cikin bayanan akwai hotunanka.  Su ma ana dauka, musamman ganin cewa a bainar jama’a suke idan a kafar sada zumunta ce.  Daga cikin bayanan akwai lambar wayarka, da lambar gidanka, da lambar keke ko mashin ko motarka, da lambar katin shedar zama dan kasa (National ID Card), da lambar katin ofishinka (Staff ID Card), da alkunya ko lakabin da aka sanka dashi (kamar “Baban Sadik” misali), da matsayinka a al’umma ko a ofis ko na sarautar gargajiya.  Idan kana da adireshin Imel da adireshin Gidan yanar sadarwa ma duk ana iya amfani dasu a damfari jama’a.

Daga cikin bayanan har wa yau akwai sakonnin da ka taba rubutawa, ko kasidunka, ko rubuce-rubucenka da kayi bincike ka rubuta, ko sakon bidiyo, ko sauti, ko wani tambari ko ramzi naka da aka sanka dashi.  Daga ciki har wa yau akwai lambobin katinka na banki, wato: “ATM Card Number,” da lambobin taskarka na banki, wato: “Account Number,” da lambobin dake kan cak dinka na banki, wato: “Cheque Serial Numbers.”  A kasashen da hukuma ke baiwa jama’a marasa aikin yi tallafi sanadiyyar rashin aiki ko tsufa ko wani dalili na tattalin arziki, suna da abin da ake kira: “Social Security Services,” kuma duk wanda ke karkashin wannan shiri daga cikin al’ummar kasar, yana da lamba ta musamman da ake kira: “Social Security Number” (SSN).  Wannan lamba tana da matukar mahimmanci ga rayuwar mai rike da ita.  Domin da ita yake karban tallafi daga hukuma a duk wata.  Ita ma ana iya sace ta a damfari hukuma da ita.  Sai na karshe, wato lambar haraji, wato: “Tax Identification Number” (TIN).  Ita ma tana da matukar mahimmanci ga rayuwar mai rike da ita, kamar yadda za mu ga misali a aikace nan kusa.

- Adv -

Dukkan wadannan bayanai suna wakiltarka ne.  Iya gwargwadon yadda aka sanka dasu, iya gwargwadon yadda za a yarda da abin da aka aiko ko bayar ko miko ta hanyarsu ko amfani dasu.  Kuma su ne abin da Barawon Zati (Identity Thief) ke hari.  Da zarar ya sace ko same su, ta kowace hanya ne, zai yi amfani dasu don biya masa bukatunsa.  Nan gaba kadan mai karatu zai ga nau’ukan dalilan dake sa a aiwatar da irin wannan tsari na ta’addanci.

Yaduwa da Bunkasa da Tasiri

Satar Zati sana’a ce ta ta’addanci dake kan yaduwa kamar wutar daji a kasashen duniya, ko ince a kafafen sadarwa na zamani.  Kusan kowace kasa na da wani kaso na hasara da take yi a duk shekara sanadiyyar wannan sana’a mummuna.  Iya gwargwadon yadda fannin sadarwar zamani ya bunkasa a kasar, iya gwargwadon barnar da ke aukuwa, musamman idan hukuma bata sa ido a kai ba.

A cikin littafinsa shahararre mai take: “Identity Theft,” marubuci Jim Whiting ya rubuta cewa a kasar Amurka, a shekara ta 2012 kadai, anyi hasarar dala biliyan goma shabiyar ($15,000,000,000) ta hanyar wannan mummunar sana’a na Satar Zati.  Idan ka juya kimar wannan adadi na kudi zuwa nairan Najeriya, zai baka kusan Naira Tiriliyon biyar da biliyan dari hudu (N5,400,000,000,000).  Wannan daidai kasafin kudin Najeriya Kenan a shekara ta 2015.  Bayan hasarar kudade, wannan sana’a tayi mummunar tasiri a kan Amurkawa sama da Miliyan goma sha biyu.

A taron shekara-shekara na Kungiyar Lauyoyin Najeriya (Nigerian Bar Association) wanda akayi a shekarar 2017, jaridar Premium Times (ta Agusta 22, 2017), ta ruwaito shugaban Hukumar Sadarwa ta Kasa – National Communication Commission (NCC) – wato Farfesa Umar Danbatta yana cewa a duk duniya, Najeriya ita ce ta uku a fagen aikata miyagun laifuka ta hanyar kafafen sadarwa na zamani (Cybercrime).  Kasashen da suka mata fintinkau su ne: gwaggo Amurka, da yadiko Ingila.

Farfesa Danbatta yace a shekarar 2015 kadai, Najeriya kasarmu ta gado, ta yi hasarar wuri na gugan wuri har naira biliyan dari da ashirin da bakwai (N127,000,000,000) ta hanyar manyan laifuka, ciki har da Satar Zati.  Danbatta ya ta’allaka alhakin faruwan hakan ne kan rashin hukumomin gwamnati masu tasiri da za su iya dakile faruwan wannan ta’addancin.  Wanda wannan shi ne babban matsalar da kasar ke fama ita a dukkan fannonin rayuwa da hukuma ke da ruwa da tsaki a ciki.

A nasa bangaren, Shugaban majalisar dattawa ta Kasa, Dakta Bukola Saraki, shi ma ya ayyana wannan adadi na kudi da kasarmu tayi hasararsa ta wannan hanya, a daya daga cikin taruka da aka gayyaceshi kan harkar sadarwa.

A cikin wani rahoto na musamman mai take: “Cyber Crime Made Easy,” babban kamfanin kwamfuta da kayayyakin sadarwa na zamani, IBM Inc. dake kasar Amurka, ya bayyana hanyoyi da matakai na musamman da masu wannan dabi’a ke amfani da ita wajen kaiwa ga muradinsu.  Daga ciki dai akwai samar da wata manhaja ta musamman da suka yi wacce tayi yayi tsakanin shekarar 2010 zuwa 2015 mai suna: “ZEUS”, wacce ake iya amfani da ita wajen sato kowane irin bayani ne ake son sacewa a cikin kwamfuta.  Duk kwamfutar da aka kai mata hari ta amfani da wannan manhaja, kuma aka dace manhajar ta hada alakar sadarwa tsakaninta da ita, to, duk abin da ke cikin kwamfutar tana iya kwafo su.

Samuwar wannan manhaja da sauran ire-irenta sun taimaka matuka wajen sawwake hanyoyin da ake bi wajen tattara bayanan jama’a a boye ba tare da sanin mai bayanan ba, musamman dai a mahallin da ba mai bayanan bane ke adana da kanshi, irin su dandalin sada zumunta da dai sauransu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.