Sakonnin Masu Karatu (2014) (12)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

86

Salaamun alaikum, muna matukar jin dadin shafinka. Na karanta amsar da ka bayar kan yadda ake adana sakonnin tes ta ma’adanar katin waya (Memory Card), na kuma ji dadin wannan amsa. Amma ta yaya za a iya yin hakan ta amfani da wayar Gionee S20?  Ina kuma barar kasidarka ta musamman da ka rubuta kan bayanin sama da kasa, kamar yadda yazo a Kur’ani. Ga Imel di na: erudite2011@live.com.

Wa alaikumus salam, na gode da yabawa. Lallai yadda kaji bayani a baya, babu wani bambanci tsakanin wayoyi kan yadda za ka iya taskance sakonninka na tes zuwa ma’adanar katin waya, wato “Memory Card.”  Dangane da kasidar da ka bukata kuwa, ka duba akwatin Imel dinka, na turo maka. Allah sa mu amfani da abin da muke karantawa baki daya, amin. Na gode kuma da fatan ka gamsu.


Assalaamu alaikum, da fatan an yi sallah lafiya Baban Sadik, ina maka fatan alheri.  Daga masoyinka Sulaiman Yunusa Salai, Gumel, Jigawa.

Wa alaikumus salam, ina matukar murna da kuma godiya da wanna bushara da fatan alheri da ka mani. Allah kara mana dankon kauna tsakaninmu, amin. Na gode.


Salaamun alaikum, Baban Sadik shin, mene ne “Blogger” kuma yaya ake amfani da shi?  Allah ya taimakeka, ya kuma kara maka basira, amin.  Daga: Sabi’u Uba Yola, Adamawa.

Wa alaikumus salam, barka da warhaka. “Blogger” dai a takaice wata masarrafa ce da ke taimaka wa mutane wajen bude taska ko mudawwana a Intanet.  Ma’ana wani wuri ko shafi naka na musamman, inda za ka rika zuba bayananka don amfanin kanka da sauran masu ziyara.  Wannan masarrafa na kamfanin Google ne.  Idan kana bukatar bude shafi na kanka ta amfani da wannan masarrafa, dole sai ka bude akwatin Imel na Gmail, sannan ka je shafin da ke: www.blogger.com/start.  Idan ka shiga sai ka shigar da bayanan Imel dinka, za  kai ka inda za ka cika fom don bude shafinka na musamman.  Da fatan ka gamsu.


- Adv -

Assalaamu alaikum Baban Sadik, ina fatan kuna lafiya.  Don Allah wai wayar salula mai dauke da babbar manhajar Android na kasar Sin da wacce ba ta kasar Sin ba, wacce ce ba ta saurin cinye bayanai idan ana shawagi a Intanet da ita?

Wa alaikumus salam, barka ka dai. Ai batun cinye bayanai ko saurin zanftare bayanai sanadiyyar shawagi a Intanet ba matsala ce ta wayar salula a karan-kanta ba.  Wannan ya ta’allaka ne ga nau’in tsarin da kake kai na kamfanin waya.  Idan babu wani tsari na musamman da kake kai, za su rika zaftarar kudin da ke katinka ne kai tsaye.  Amma idan akwai wani tsari (Data Bunble Plan) da kake kai, sai a rika zaftara daga adadin bayanan da aka tanada maka, ba daga kudin katin wayarka ba.  Don haka ka sani, zaftarar kudin katin waya da ake yi kai tsaye ya ta’allaka ne ga rashin tsari da mai waya ya kasa shiga. Ko kuma yana kan tsari, sai adadin bayanan da aka bashi ya kare, a nan kam muddin yana da kudi a katin wayarsa, daga ciki za a ci gaba da zaftara.  Sai ka kiyaye. Da fatan ka gamsu.


Assalaamu alaikum, yaya aka ji da jama’a?  Na karbi lambarka ne don in maka godiya, saboda zaburar da ni da kayi wajen saba mini da fasahar Intanet sakamakon jin bayananka a shirinka na Sunnah TV.  Na kuma fara zaben ajiye muraja’a don Intanet.  Ni daliba ce a Higher Islamic School da ke Gombe.  Baban Sadik Allah saka maka da gidan aljanna, amin.  Daga Ummu Yusuf.

Wa alaikumus salam yaa Umma Yusoof. Ina godiya ni ma matuka da wannan jinjina. Allah amfanar da ke ta wannan hanya da fa’ida mai inganci da alfanu gare ki da al’umma baki daya.  Sai ayi hankali a yayin da ake mu’amala da fasahar Intanet da ma sauran hanyoyin sadarwa na zamani. Allah wuce mana gaba, amin.


Assalaamu alaikum warahmatullah, Allah kara basira, amin.  Bayan haka, na cire ma’adanar waya ta ne daga wayar, daga baya da na tashi mayarwa sai wayar ta nuna mini: “Unformated Memory.”  Da na matsa kuma don inyi formatting sai na ga an ce: “Delete All Data to Format,” aka sa “Yes or No” sai na matsa, sai aka sa “Operation Failed.”  Dalibinka: Musa Adam, Mile 12, Legas.

Wa alaikumus salam Malam Musa, da fatan kana lafiya.  Ta yiwu a karon farko da ka cire katin ma’adanar wayarka akwai kwayar cutar wayar salula a ciki, ko kuma bayan ka cire, ka sa a wata waya wacce ke dauke da kwayar cuta (Virus), shi yasa a karon karshe da kazo mayarwa wayar tace allambaram bata san wannan ba.  Ko kuma, a sadda ka tashi cirewa daga wayar ko daga wata wayar da ka sa bayan ciro ta daga wayar farko, ta yiwu katin ma’adanar a bude yake a wayar, sai ka nemi cirewa ba tare da ka rufe bayanan da ka budo ko ka zuba mata ba.

Wannan zai sa bayanan da ke cikin katin su gurbace (Corrupt).  Idan kuwa suka gurbace, to babu yadda za a yi wayar ta fahimce su balle ta basu ma’adana a cikinta.  Shi yasa tace maka sai ka goge katin kafin yayi amfani.  Nan gaba sai a kiyaye.  Kada a rika cire katin ma’adanar waya (Memory Card) ba tare da ka’ida ba.  Duk sadda kuma katin ma’adanar waya ke bude, ko bayanan cikinsa na bude ne, aka yi yunkurin cire shi daga wayar ba tare da an rufe bayanan ba, to za a samu matsala. Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.