Sakonnin Masu Karatu (2022) (6)

Bayani Kan Pi Network da eNaira

Zancenka gaskiya ne kan cewa ana amfani da hanyar kutse wajen satan kudaden zamani dake Intanet.  Hakan ya sha faruwa sosai, kuma yana faruwa.  Ba su kadai ba, hatta lokacin da Babban Bankin Najeriya wato: “CBN” ya kaddamar da nau’in kudin zamani na eNaira, bayan an dora manhajar a cibiyar Play Store, sai da wasu suka aiwatar da kutse cikin manhajar. – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 16 ga watan Satumba, 2022.

254

Kamar makon jiya, yau ma za mu ci gaba ne da amsa tambayoyin masu karatu.  Da fatan za a ci gaba da kasancewa tare damu yadda aka saba.

————–

Assalamu alaikum Baban Badik, a gaskiya ina fa’idantuwa da rubuce-rubucenka sosai.  Allah ya kara basira.  Tambayata game da eNaira shi ne yan Dandatsa ko yan Yahoo Yahoo!, ba za su ina karya tsaron sirrin mai asusu su mishi sata ba kamar yanda kwanan baya naga anyi akan kudin Intanet na Cryptocurrencies? daga Abubakar Sa’idu Dankanjiba. 07033631603.

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Abubakar.  A wannan zamani da muke ciki mai cike da ci gaba a fannin kimiyya da fasahar sadarwa na zamani, babu wata manhaja, ko wani tsari na hada-hadar kudade da ba za a iya keta masa hurumi ba.  Kawai ya danganci kwarewar mai son yin hakan ne ko rashin kwarewarsa.  To amma, kamar yadda Hausawa ne ke cewa, a cikin ido ake tsawurya; idan muka ce sai ran da aka samu “cikakkiyar” kariya a wannan mahalli ne sannan za mu yi ta’ammali dashi, to ashe za mu mutu har duniya ta tashi bamu samu biyan bukata ba.  In dai muna jiran “cikakken kariya” ne.  Wannan kenan.

A daya bangaren kuma, ana samun ci gaba sosai wajen samar da kariya, ko ma ince an samu, dangane da manhajojin da kake magana a kai.  Manhajar e-Naira dake cibiyar Play Store, tana dauke da hanyoyin kariya sosai.  Sannan dole ne kai ma a matsayinka na mai amfani da manhajar, ka kiyaye hanyoyin kariyar da manhajar ta tanada.  Idan baka kiyaye su ba, ba  ka samun kariyar da kake bukata.  Hanyoyin kuwa su ne:  ka zama mai kaffa-kaffa da wayarka – kada ya zama kullum wayarka na hannun wani.  Duk wata manhajar wayar salula mai amfani da tambarin kariya (Bar code) wajen ta’ammali da ita, ana iya keta mata hurumi ta amfani da wata wayar ko ta kwamfuta.  Na biyu, ka sanya Kalmar sirri mai tsauri, wanda ba kowa zai iya hararo abin da kake shigarwa ba.  Na uku, kayi amfani da tambarin hannu (Biometric) a matsayin hanyar hawa manhajar.  Na hudu, a duk sadda ka hau ka gama aiwatar da abinda kake so, kada ka rufe wayar kawai, a a, ka fita daga cikin manhajar a ka’idance.  Ma’ana, ka matsa: “Log Out”, wanda za a ka same shi a bangaren hagu ko dama a shafin da kake, daga can kasa.

Zancenka gaskiya ne kan cewa ana amfani da hanyar kutse wajen satan kudaden zamani dake Intanet.  Hakan ya sha faruwa sosai, kuma yana faruwa.  Ba su kadai ba, hatta lokacin da Babban Bankin Najeriya wato: “CBN” ya kaddamar da nau’in kudin zamani na eNaira, bayan an dora manhajar a cibiyar Play Store, sai da wasu suka aiwatar da kutse cikin manhajar.  Bayan haka ma, hatta kwamfutocin dake da dauke da wadannan tsare-tsare sai da aka kai musu farmaki.  Kari a kan haka ma, masu wannan mummunar tabi’a suka ta kirkirar hanyoyin yaudarar mutane ta kafafen sadarwa – irin sakon tes, da Imel, da kafafen sada zumunta – don yaudarar mutane su basu bayanansu na sirri don su kutsa cikin taskokinsu na banki, musamman manhajar eNaira.  Amma a karshe an dakile wadannan hanyoyi.

A takaice dai, dabi’a ce ta zamantakewa cewa a duk sadda aka samar da wani abu mai amfani ga jama’a, sai an samu bata-gari da za su bi wasu hanyoyin don ganin sun zambaci mutane ko hana ruwa gudu.  Irin wannan kuwa bazai taba fakuwa ba. Shi yasa hukumomi da kamfanonin da abin ya shafa suke amfani da kwararru wajen ganowa da kuma dakile masu ire-iren wadannan abubuwa.

Allah kara tsare mu baki daya, amin.  Wannan shi ne dan abin da ya samu.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

Assalamu alaikum. Allah Ya ƙara basira. Don Allah kayi min bayani akan Pi network. Aminu Umar Zariya. Na gode: 07035586603.

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Aminu.  Ina godiya da addu’o’inku kamar kullum.  Wadannan kalmomi da ka ambata dai sunaye ne na’ukan kudaden zamani, wato: “Cryptocurrencies”, ko “Kiripto”, kamar yadda ake ambatonsu a harshen Hausar zamani.

PI Coin

Kwandalar PI (PI Coin) dai nau’in kudin Intanet ne da wani kamfani mai suna “Pi Network” ya kirkira kuma a halin yanzu ake hako shi (Mining) ta hanyar amfani da wayar salula.  Wannan tsari na kamfanin Pi Network dai ya saba wa tsarin da sauran kamfanonin kudaden zamani suke bi wajen samar da irin wannan kudi.  A yayin da a ka’ida kowane kamfani ke kirkira sannan ya samar da kwamdalolin da yake son sayar wa mutane don ci gaba da kasuwancinsa a cibiyar hada-hadar kudaden zamani na Intanet, wato: “Cryptocurrency Exchanges”, shi kamfanin Pi Network ya zabi ya baiwa mutane damar hako kudaden ne daga kan wayoyinsu na salula, ta amfani da manhajarsa dake kan cibiyar Play Store.  A yayin da mutane ke hako kudaden, shi kuma yana bin matakan da suka dace wajen kaddamar da shi.  Sai ya zama a yayin da ya tashi kaddamarwa, ba ya bukatar sayar wa kowa, tunda tuni mutane sun gama samun kudaden a lalitarsu.

An kirkiri wannan kamfani ne a shekarar 2019, kuma duk da cewa a baya ya sha alkawarin kaddamar da kwandalarsa mai suna: “Pi Coin” a shekarar 2020, amma daga baya sai ya daga zuwa karshen 2021, sannan ya sake dagewa zuwa karshen shekarar 2022.  Wannan yasa a halin yanzu kwandalar Pi ba ta da farashi, tunda ba a kaddamar da ita ba. Kuma wannan yasa babu wata cibiyar hada-hadar kudaden zamani da ake sayar da ita.  Hakan har wa yau ya jefa shakku sosai a zukatan mutane, har yasa ake ganin kamar duk yaudara ce.

Duk da haka, wannan kwandala ta Pi ta fi shahara a kasashe masu tasowa.  Mutane suna nan suna ta hakowa ta amfani da wayoyinsu na salula.  A wasu wuraren ma tuni mutane sun fara sayar da nasu, don samun kudade.  Suna hakan ne ta hanyar aika wa juna a bisa wani farashi da suka kayyade a tsakaninsu.  Masu saye kuma suna tarawa ne don idan ta “fashe”, kamar yadda suke fada, sai su sayar su sha jar miya.

Mafi hadarin dake tattare da wannan kwandala a kasashe masu tasowa musamman a nan gida Najeriya shi ne, masu hako wannan kwandala sun dora mata dogon buri, saboda irin karairayin da ake musu cewa idan aka kaddamar da kwandalar farashinta zai fi ma na kwandalar Bitcoin.  Wasu na ganin duk kwandala guda sai ta fi miliyan daya.  Wasu su ce dala dubu goma ($10,000), wasu su ce sai ta kai dala dubu dari uku da hamsin ($350,000) duk kwandala daya.  Sukan ce, idan ta fashe za su sayi gidaje, da filaye, da motoci, da zuwa Makka, da yin aure ko karo aure ga masu mata.  Akwai wani bidiyo da na gani daidai lokacin da nake hada wannan Makala, inda ake tambayar wani matashi da bai shige shekaru 25 ba, bayan an nuna masa wasu katafaran gidaje da adadin kudadensu zai kai miliyan 50 kowanne, cewa kwandalar Pi nawa zai bayar don sayan wadannan gidaje?  Sai yace idan aka karbi kwandalolinsa na Pi guda uku aka bashi wadannan gidaje, “Wallahi tallahi” (kamar yadda ya fada), an cuceshi.  Wannan ke nuna matukar jahilci da burin dake zankame cikin zukatan da yawa cikin masu rike da wadannan kwandaloli da ko kaddamar dasu ba ayi ba, balle a san nawa zasu kama wajen kiman farashi.

Wannan, a takaice, shi ne bayani kan wadannan kwandaloli guda biyu.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.