Sakonnin Masu Karatu (2022) (7)

Yawan Daukewar Wayar Salula

Bayan dukkan wannan bayani, hanya mafi sauki wajen gano hakikanin abin da ke sa waya ta shiga irin wannan yanayi shi ne zuwa wajen mai gyara.  Shi zai duba ta, don tabbatar hakikanin abin da ya same  ta.  – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 23 Satumba, 2022.

139

Kamar makon jiya, yau ma za mu ci gaba ne da amsa tambayoyin masu karatu.  Da fatan za a ci gaba da kasancewa tare damu yadda aka saba.

——————-

Assalamu alaikum, amincin Allah ya tabbata a gareka.  Me yasa wayata take daukewa haka kawai?  Daga Kamal Suwarin: 07047154007.

Wa alaikumus salam Malam Kamal, barka ka dai.  A gaskiya dalilan dake sa waya ta rika kashe kanta ba tare da an kashe ta ba, suna da yawa sosai.  Shahararru daga ciki sun hada da matsalar gangar-jiki.  Misali, idan na’urar cajin wayar (Charging Point) ta lalace, makamashin batirin zai rika karewa da wuri, kuma nan take za ta mutu ko ba a kasha ta ba.  Haka idan wayar ta fadi kasa, ko wani abu ya fadi kanta mai nauyi, tana iya mutuwa nan take, saboda gocewar batir (musamman idan a baya an taba canza mata batir), ko lalacewar fuskar wayar (Screen), ko kuma tsinkewar wayar dake jone da fuskar wayar wanda ke bata makamashin lantarki.  Haka idan abu mai nauyi ya daki wayarki, ko ta fado daga sama zuwa kasa, iya gwargwadon gumurzun da tayi wajen fadowa iya yadda ababen cikinta za su tabu.  Zai zama kamar mutum ne yayi hadari ya bugu; ba za ka wata alamar gujewa ba a jikinsa ko rauni, amma a can cikinsa watakila ya samu rauni mai girma, ko a kwakwalwarsa, ko cikinsa.  Ire-iren wadannan matsaloli na iya sa waya ta rika mutuwa da kanta, iya gwargwadon lahanin da hadarin ya haifar mata.

A daya bangaren kuma, kwayar cuta (Virus) na iya jefa ta wannan yanayi, musamman idan ya shafi kwakwalwarta.  Wannan zai haukatar da ita, ya rika jefa ta cikin yanayin sumewa da farfadowa.  Bayan haka, matsalar karancin ma’adana ma na iya jefa ta cikin wannan yanayi.  A ka’ida idan ka kunna wayar salula, takan debo bayanan manhajar da za ka yi amfani dasu ne daga asalin ma’adanarta (Read Only Memory – ROM) zuwa ma’adanar wucin-gadi (Randon Access Memory – RAM).  Wannan ma’adana ta RAM ce ke baka damar sarrafa manhajar da ka budo.  Sabo da duk manhajar da ka budo, nan take zuwa ta kwanta.  Da zarar ka gama amfani da ita, sai ta koma can a matsayin bayanai.  Wannan ma’adana ta RAM galibi karama ce.  Idan ka budo abubuwa da yawa a lokaci daya, tana iya cikewa.  Idan kuma ta cike, ta yadda babu masaka-tsinke, hakan na iya sumar da ita.  Sai ta carke cak! Ba gaba ba baya.  Ko kuma, a karshe ta mutu.

Bayan dukkan wannan bayani, hanya mafi sauki wajen gano hakikanin abin da ke sa waya ta shiga irin wannan yanayi shi ne zuwa wajen mai gyara.  Shi zai duba ta, don tabbatar hakikanin abin da ya same  ta.

Da fatan ka gamsu da wannan gajeren bayani.

- Adv -

Salamun alaikum Baban Sadik, barka da warhaka.   Don Allah a min bayani; katin SIM dina ne nayi masa “welcome back” har sau uku amma nambobina basu dawo ba. Yaya zan yi? Na gode. Daga Umar A. Umar Mazoji, Matazu LG, Katsina: 07046493147.

Wa alaikumus salam, barka ka dai Malam Umar.  Fatan kana lafiya kaima.  Ai lambobinka ba za su dawo ba.  Duk da cewa katin SIM na dauke da ma’adanar lambobi, amma ma’adanar ba ta da girma.  Galibi takan taskance lambobi 200 ne; ba ya wuce haka.  Bayan haka, wayoyin salula na zamani kan taskance lambobin waya ne a kansu, ba a kan katin SIM ba.  Mu kaddara wayar karamar waya ce wacce ke taskance lambobi akan SIM, ko don haka ta zo, ko kuma kai ka tsara hakan, idan aka samu matsala katin SIM ya lalace ko aka sace waya har ta kai ga an canza SIM, ko da kuwa wancan lambar ce ta farko aka mayar, ba za taba samun wadannan lambobin da ka taskance a kan katin ba.

Shi yasa ma a duk sadda kaje ofishin kamfanin waya don matsalar da ta shafi canza layi, za su gaya maka karara cewa lambobin da ka taskance a kan wayarka ba za su dawo ba.  Me yasa?  Saboda wadannan lambobin na kan katin SIM din ne.  Kuma su kansu suna iya ganin lambobin ne idan katin yana aiki a kan wayarka.  Da zarar katin ya lalace, ko kuma an sace, ka ga ba zai kasance a kan waya ba.  Wannan yasa ba za a iya ganinsu ba.  Su kuma idan sun tashi baka, ko da asalin lambobin layin za a mayar maka, katin zai zama sabo ne.  Sabon kati za a dauko a zana masa lambarka da ta bace.  Wannan shi ne dalilin da yasa lambobinka ba za a su dawo ba.

Hanya mafi sauki wajen magance ire-iren wadannan mataloli ita ce, kayi rajistan adireshin Imel na kamfanin Google, wato Gmail kenan.  Idan kana da rajista da Gmail, kuma ka dora a kan wayarka, duk lambobin dake kan wayarka ana taskance maka su ne a wata manhaja na kamfanin Google mai suna: “Google Contact”, wacce ke like da akwatinka na Imel.  Idan aka sace wayarka, ko goge lambarka aka yi  bayan an halaka wayar, da zarar ka canza waya, kana kunna data ka dora adireshinka na Gmail, dukkan layunka za su dawo a cike, babu kwange.

Wannan dan abin da ya samu kenan na bayani.  Da fatan ka gamsu.

Assalamu alaikum. Suna na Abba Salihi. Muna kokarin kafa Makaranta mai suna Kano Institute of Technology. Saboda haka, za mu yi matukar farin ciki in za ka turo mana da abubuwan da ka rubuta akan Kimiyya da Kere-Kere.  Ga adireshina kamar haka: asalihi@yahoo.com, asalih@gmail.com.  Muna kara godiya.

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Abba Salihi.  Zan so sanin wasu fannoni ne kuke da bukata?  Sannan a wani yanayi?  In dai karantar da dalibai za ayi, akwai Karin bayani da zan bukata don tabbatar da cewa na baku abin da yake mai fa’ida ne.  Don haka, zai dace ka min Karin bayani kan abin da na bukata.  Na aika maka wannan sako ta adireshinka na Gmail da Yahoo! kamar yadda ka aiko.  Sai na ji daga gareka.  Na gode.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.