Karantar da Ilimin Kimiyya ta Kafafen Yada Labarai

A wannan mako mun dubi tasirin mujallu da jaridu dake Intanet ne wajen karantar da mutane ko fadakar dasu kan ilimin kimiyya. Mun kuma dubi tsarin jaridun Najeriya wajen yin hakan ko rashinsa.

496

Kafafen Watsa Labaru Cikin Al’umma

Abu ne sananne cikin kowace al’umma, musamman a wannan zamani da muke ciki, cewa kafafen watsa labaru, musamman jaridu da kuma mujallu, kafafe ne masu muhimmanci da ake amfani da su wajen fadakar da al’umma.  Bayan labaru da a kullum suke samarwa, kafafen watsa labaru na jaridu da mujallu na taimakawa gaya wajen sawwake samuwar nau’ukan ilmi da dama, musamman wadanda ba kowa da kowa ke iya zuwa ya dauke su ba a makarantu ko a gaban masana fannin.

A wasu kasashe da suka ci gaba a fannin tattalin arzikin kasa da siyasa, kafafen watsa labaru – musamman jaridu da mujallu – basu takaitu da samar da labarai na siyasa, da tattalin arzikin kasa, da adabi, da zamantakewa kadai ba, hatta fannin kimiyya da kere-kere suna tsallakawa.  Sukan yi hakan ne galibi ta hanyar hirarraki da suke yi da masana a fannin, ko dauko wasu kasidu da makaloli da aka rubuta masu tasiri wajen ciyar da al’umma gaba a ilmance, ko wasu sakamakon bincike na kimiyya da wasu kwararru suka yi ko suke kan yi, ko kuma, a karshe, wani abin mamaki da al’ajabi da ke faruwa ko ya faru cikin al’umma, da kuma tasiri ko mahangar kimiyya kan wannan lamari.

Bayan haka, a wasu kasashen ma ba a tsaya a nan kadai ba, hatta jaridu da mujallu na musamman akwai, masu fayyace bayanai kan bincike da kuma sababbin kasidu da makaloli da wasu kwararru suka fitar, don yada su ga al’umma baki daya. Misali, a kasar Amurka akwai mujallu na musamman masu samar da bayanai da sakamakon bincike na kwararru kan kimiyyar sararin samaniya, da kimiyyar karkashin kasa, da kimiyyar halitta, da kimiyyar inganta muhalli, da kuma kimiyyar sadarwar zamani – wato bangaren kwamfuta kenan da sauran kerarrun kayayyakin sadarwa na zamani.  Akwai mujallar Science, wacce ke fitowa a duk wata, akwai mujallar The Scientific American wacce ke fitowa ita ma a duk wata, akwai mujallar The New Scientist, ita ma a duk wata take fitowa.  Bayan haka, akwai mujallar Physics, wacce ke fitowa duk wata, da kuma mujallar National Geographic, wacce ke dauko bayanai kan sakamakon binciken da kwararru ke yi dangane da kimiyyar karkashin kasa da muhalli.  A fannin kimiyyar sadarwar bayanai kuma, akwai mujallar PC World, wacce ke fitowa a duk wata, dauke da kayatattun bayanai kan hanyoyin mu’amala da kwamfuta, ko dukkan kayayyakin sadarwa na zamani.  Wadannan ba iyakansu ba kenan, na kawo su ne a matsayin misali.

Idan muka koma kan jaridu, zamu ga cewa nan ma basu yi kasa a gwiwa ba.  Misali, a kasashen Larabawa, akwai manya kuma shahararrun jaridu masu taimaka wa dalibai da ma al’umma baki daya wajen samar da bayanai ko karantarwa cikin fannin kimiyya da dukkan fannonin da suka shafe shi.  A kasar Saudiyya akwai jaridar Okaz, wacce ke taimakawa.  Haka a kasar Misira, akwai jaridar Al-Jumhuriyyah, wacce ke nakalto tambayoyin da aka yi wa daliban sakandare lokacin jarabawarsu, tare da amsoshin wadannan tambayoyi baki daya, duk a fannin kimiyya.  Misali, a bugunta na 1 ga watan Mayu na wannan shekara, jaridar ta nakalto dukkan tambayoyin da aka yi wa daliban sakandare kan kimiyyar sinadarai, wato Chemistry, tare da amsa dukkan wadannan tambayoyi, cikin  sauki.  Dukkan wannan aiki da jaridar take yi, kyauta ne, ba wai wani kamfani bane ko wata makaranta ko wata hukumar gwamnati ke daukar nauyin yin hakan ba.  Wannan aiki da hidima da wadannan jaridu da mujallu ke yi na matukar taimaka wa dalibai wajen kara musu kwazo da kuma cusa musu kwadayin abin a zuciyarsu.

- Adv -

Ina Jaridu da Mujallun Nijeriya Suke, Wajen Yada Ilmin Kimiyya?

Abu ne bayyananne cewa kashi saba’in da biyar cikin abubuwan da mujallu da jaridun kasarmu ke dauke da su duk kan harkar siyasa ne da tattalin arzikin kasa da zamantakewa.  Wannan ba aibu bane ko kadan, amma in da za a samu tsari irin wancan, kamar yadda muka gani a wasu kasashen, da lallai dalibanmu za su so hakan.  Musamman ma samun hakan cikin harshen gida – Hausa ko Inyamuranci ko kuma Yarbanci.  Domin daya daga cikin manyan matsalolin da ke ci wa ilmi tuwo a kwarya a kasar nan, shi ne rashin fahimtar inda karatu ya dosa a zuciyar dalibai.  A duk shekara abin sai dada gaba-gaba yake yi, kamar ciwon ajali.

A nan ba na nufin wai a daina amfani da harshen turanci wajen karantar da dalibai a makarantu, sam ba can na dosa ba.  Abin da nake nufi shi ne samar da wata kafa wacce za ta rika agaza wa dalibai, ta hanyar da suke fahimtar ilmin da ake koyar da su cikin harshen turanci.  Hakan kuma ba zai yiwu ta dadi ba sai da taimakon kafafen watsa labaru – musamman mujallu da jaridu.  Duk da cewa a kasashen Afirka muna fama da matsalar rashin damuwa da karatu, musamman wannan zamani da muke ciki mai dauke da kayayyakin isar da ilmi ta amfani da kayayyakin fasahar sadarwa.  Amma duk da haka, akwai karuwar masu karatun mujallu da jaridun Hausa fiye da shekaru goma da suka gabata.  In kuwa haka ne, to akwai tabbacin cin nasara cikin yardar Allah.  Domin tsawon shekaru uku da wannan shafi yayi yana hankado bayanai kan nau’ukan ilmin kimiyya musaman na sadarwa da sararin samaniya, masu karatu da dama sun fa’idantu da dan abin da ake ciyar da su a shafin.  Na fahimci hakan ne ta hanyar masu bugo waya da aiko sakonnin tes don neman Karin bayani kan yadda za a yi su samu shiga makarantu na musamman da ake budewa masu karantar da fannoni makamantan wannan.  Akwai wadanda suka shiga, wasu ma sun kusan gamawa – duk ta wannan hanya.

Abu ne mai kyau idan jaridunmu musamman na Hausa, za su rage yawan shafukan da suke sadaukarwa wajen hirarraki da cuku-cukun siyasa, ko in hakan ba zai samu ba, to su kara ko da shafi daya ne a duk mako, don gabatar da wasu nau’ukan bayanai masu alaka da fannin kimiyya.  Akwai mutane da dama da suka yi rubutu kan fannin kimiyya cikin harshen Hausa, amma saboda rashin kudin bugawa, ko kuma rashin kafar yadawa, abin na nan a zube.  Har wa yau, cikin watan Yulin nan naci karo da wani bawan Allah a garin Gusau, wanda yake rubuta littafi na musamman kan ilmin Fiziya.  A halin yanzu yana babi na biyar, kuma cikin hirar da nayi da shi ne yake sanar da ni cewa babban abin da ya kai shi ga hakan dai shi ne matsalar da yake samu daga dalibansa na sakandare da yake karantarwa.  Yace a duk sadda ya karantar da su cikin harshen Turanci kadai, ba su fahimta ko kadan, sai ya koma gida ya tsara darasi na musamman cikin harshen Hausa, don yi musu maimai kan darasin baya. Wannan ne ma yasa, a cewar Malamin, duk sadda yake da darasi, sai ya juya darasin zuwa harshen Hausa kafin ya shigo aji.  Da zarar ya gama karantar da su a turance, sai ya koma bayani cikin harshen Hausa.  Yace akwai dalibansa da dama masu kaifin basira wajen lissafi da fahimta, to amma ba su da kudura wajen harshen turanci balle fahimtar turancin da ke kunshe cikin fannin da ake karantar da su.

Ka ga da ace akwai dama makamanciyar wadda ke wadancan kasashe, da tuni an karu da abubuwa da dama.  Domin wannan zai taimaka wa daliban sakandare, musamman wadanda ke karatu a halin yanzu, da wadanda ke da sha’awar ci gaba a fannin kimiyya.  Ga wadanda kuma suke da sha’awa ta baka kadai, za su samu damar sanin yadda fannin yake, tare da fa’idantar da kansu.  Tabbas na san ba abu bane mai sauki yin hakan a kasa irin Nijeriya, saboda tsarin siyasa da tattalin arzikin kasar sun sha bamban da wadanda ke sauran kasashe.  To amma duk da haka, sadaukar da kai za mu yi don ganin al’umma ta ci gaba.  Muna bukatar ilmin kimiyya matuka a wannan kasa tamu, musamman kasar Hausa, kuma hakan ba zai samu ta dadi ba sai mun habaka ‘ya’ya da jikokinmu.  Idan muka dubi kasashe irinsu Saudiyya da Iran, za mu samu ‘yan kasar ne suka kware cikin fannonin ilmi da dama, kuma suke amfani da kwarewarsu wajen ciyar da kasar da ma al’ummarsu gaba. Don haka kafafen watsa labaru na da irin rawar da za su taka wajen wannan aiki mai matukar muhimmanci.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.