Sakonnin Masu Karatu (2020) (7)

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 24 ga watan Afrailu, 2020.

64

Assalamu alaikum Baban Sadik, sharhin littafin nan da kake yi, duk da baka ƙarasa ba, na ji daɗinsa ƙwarai da gaske. Saboda na daɗe ina neman littafin da zai wayar mini da kai sosai akan abin da ya shafi Kwamfuta, duk da dai shafinka na Kimiyya da Ƙere-Ƙere ya taimaka min ba kaɗan ba. Sai dai abin da ke faruwa shi ne, sau da yawa masharhanta za su yi sharhin wani littafi mai fa’ida a jarida, kuma su zaɓar wa mutane littafin (recommend) don karantawa, amma abin takaici shi ne, sai ka rasa in da za ka samo littafin don ka saya. Don haka ne nake fatan a ƙarshen wannan sharhi naka, za ka gaya mana inda za mu samu wannan littafin a nan Kano don mu saya. Allah Ya saka da alheri. Naka: MB Mahmoud Gama: musababamahmoud560@gmail.com.

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Mahmoud. Abin da ka fada kam haka ne. A karshe na gama sharhin littafin, kamar yadda na san ka gani ko ma karanta. Don mallakar wannan littafi kuma, kana iya tuntubar marubucin littafin kai tsaye, kamar yadda na sanar da sauran masu bukata irinka sadda suka tuntubeni. Na aika maka lambar wayarsa ta akwatin Imel dinka. Allah sa a dace, amin.

Assalamu alaikum Baban Sadik. A taimakeni da amsoshin wadannan tambayoyi don Allah. Ga tambayoyin. (1) Wane irin kalubale ake fuskanta idan aka bude gidan yanar sadarwa (Website)? (2) Idan mutane suna kai ziyara wannan gidan yanar sadarwar, shin, wanda ya kirkiri shafin yana da wani kaso a cikin “Datar” da suke Konawa ne? Idan haka ne ya kason yake? (3) Zuwa wane lokaci ne Google yake fara saka talla a shafin Intanet idan an bude? Sai kuma shawarwarin da za ka bamu akai wanda wata kila tunaninmu bai kai nan ba. Mun gode. Daga Magaji Aminu, dalibi a Kwalejin Ilimi ta Tarayya dake nan Kano: maadam743@gmail.com.

- Adv -

Wa alaikumus salam, Malam Magaji. Da farko dai, kalubale da ake fuskanta wajen tafiyar da gidan yanar sadarwa dai suna da yawa, kuma ba iri daya kowa ke fuskanta ba. Ya danganci kwarewarka. Shin, kai ne za ka gina kuma ka tafiyar da shafin? In eh, kalubalen da zaka fuskanta ya sha bamban da na wanda zai ba wani ne kudi a gina masa, sannan ya tafiyar ko a tafiyar masa. Duk da haka, abin da yafi komai wahala dangane da gidan yanar sadarwa shi ne tafiyar dashi. Domin kana bukatar sa ido a kan shafin a kullum, sakonni za su rika shigowa – daga masu ziyara ko wadanda suke adana maka shafin – dole ka saurare su. Wasu lokuta haka kawai jama’a zasu kasa samun shafin saboda matsalolin sadarwa a kamfanin da ke adana maka shafin, ba daga matsalar Intanet din waya ko kwamfutarsu ba. Sannan ga matsalolin yan dandatsa masu kutsowa cikin shafukan mutane. Dole dai kullum idonka na kan shafin.

Na biyu, masu ziyara a shafinka ba su da alaka da abin da zaka samu na kudi don sun kona “data” don ziyartar shafinka. Idan kana da haja da kake sayarwa, suka saya, nan ne za ka samu kudi. Ko ka dora tallace-tallace jama’a suka matsa har suka ziyarci tallar da kansu, ba kai ka matsa ko ka aiko wasu su mats aba (don Google zasu gane). Amma haka kawai mutum yasa “data” a wayarsa ya ziyarci shafinka a Intanet, ba ka samun ko kwabo.
Abu na uku, kamfanin Google kan sa talla ne a shafin dake dauke da zallar bayanai masu dinbin yawa, wanda ke samun masu ziyara na wani adadi a duk mako, sannan ya zama cikin daya daga cikin harsunan da tsarin Google Adsense ke karbar talla dasu – wanda kuma harshen Hausa ba ya cikin wadannan harsuna. Domin suna sanya talla ne a shafuka ko gidan yanar sadarwa mai dauke da harsunan da masu tallace-tallacen ke bukatar a sanya. Shahararru daga cikin wadannan harsuna dai su ne harshen Turancin Ingilishi, da Larabci, da Mandarin, da Faransanci, da Sipaniyanci da dai sauransu. Harshen Hausa, kamar yadda na fada a baya, ba ya cikin harsunan. Don haka, idan gidan yanar sadarwarka na dauke da makaloli ne na labaru ko bincike da aka rubuta a harshen Hausa, to, kamfanin Google ba ya dora talla a shafin.

Na karshe, shawara dai ita ce, idan an tashi gina gidan yanar sadarwar, a tabbata an samu manufa tabbatacciya wacce don ita ce aka bude, kuma a lazimci hakuri. Na san da yawa cikin mutanenmu dake bude shafukan Intanet galibi don kokarin sanya talla ne. Wasu lokuta sukan kalli abin da was uke samu na kudi daga shafukan da suka bude, wanda su kuma basu san irin wahalar da masu wancan shafi suka sha ba a farko, da irin tsawon lokacin da suka dauka suna ta kintsa shi ba. Hakuri wajibi ne, sannan a tanadi duk abin da ake son dorawa don sawwake wa mai gina gidan yanar aikinsa, sannan a karshe, a guji daukan aikin wasu a sa a shafin ba tare da basu hakkinsu na mallakar fasahar ba. Da yawa cikin matasanmu da na sani, sun sha bude tasha a Youtube don taskance bidiyo da manufar samun kudaden shiga daga Google, amma sai su dauko bidiyon wasu daga Intanet, ko ma daga wasu tashoshin na Youtube, su rika dorawa a nasu tashar. Alhali masu wannan dandali na Youtube ba wawaye bane; suna da fasaha dake iya tantance inganci ko rashin ingancin kowane bidiyo aka dora a kowace tasha ce ta Youtube. Idan an taba dora shi a Youtube, kana dorawa zasu gane. Wannan zai sa su fahimci kamar satar fasahar jama’a kawai kazo yi. Daga nan sai su ma hana ka rajista. Don haka sai a kiyaye. In da hali, duk wani bayani da za a dora a ya zama kai ne ka samar dashi, wato orijina ne, kamar yadda ake cewa a al’adance. Idan ya zama dole sai an aro wasu makaloli daga wasu shafuka, to, dole a kiyaye hakkin mallaka.

Wannan shi ne dan abin da zan iya cewa. Allah sa a dace, ya kuma sa albarka cikin abin da ake da kudurin yi. Na gode.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.