Sakonnin Masu Karatu (2020) (8)

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 1 ga watan Mayu, 2020.

122

Assalamu alaikum Baban Sadik, barka da wannan lokaci ya aiki?  Tambayata ita ce: ana iya hada kira biyu a lokaci daya da waya nau’in “TECNO T660” ko kuma “TECNO 582”; kenan kira biyu su fita daga wayarka kuma kowannensu yana jin abin da ake fada?  Sako daga Mansur Garba, Darna Tsolawo, Illela L.G.A. Sokoto: mansurgarba79@gmail.com.

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Mansur.  Idan na fahimci tambayarka, kana nufin aiwatar da kira biyu a lokaci daya.  Akwai wayoyin salula masu dauke da wannan kudura.  Amma sai ka fara kiran layi daya, idan mai layin ya dauka, sai ka sake kiran wani layi daban, shi ma idan ya daga, sai ka sake kiran wani layin, iya yawan kiran da wayar ke iya dauka.  Wannan shi ake kira “Conference Call”.  Amma ba kowace waya bace ke da wannan tsari.  Galibin wayoyin zamani sun fi zuwa dashi.  Amma wadannan nau’ukan waya na kamfanin Tecno da ka zayyana, ban taba amfani dasu ba, don haka bazan iya tantance ko suna da wannan tsari ba.  Da fatan ka fahimta.  Na gode.

Assalamu alaikum.  Ina fatan Baban Sadik yana nan lafiya.  Ina tambaya ne kan idan mutum ya sayi wayar salula sai ya zama sato ta aka yi, shin, ana iya amfani da hanyar “Tracking” a gano shi? In eh, to mene ne mutum zai yi don kiyaye kanshi in ya samu kansa a irin wannan yanayi?  Wassalam.  Daga Yusuf: yusufulislam79@gmail.com.

Wa alaikumus salam, Malam Yusuf barka dai.  Lallai akwai tsari da ake amfani dashi yanzu na gano wayar da aka sace, da ma kwamfutar da aka sace.  Wannan tsari shi ake kira: “Mobile Phone Tracking,” kuma galibin jami’an tsaron kasar nan – ‘Yan sanda –  suna da na’urorin da ake iya ganowa.  Don haka, idan har mutum ya sayi wayar da ya san satowa aka yi, to, lallai akwai yiwuwar ayi amfani da wannan tsari wajen gano ta.  Kuma idan mutum yayi rashin sa’a aka kama shi, ba lalai ya sha da dadi ba.

Abin da wannan zance ke nufi shi ne: akwai masu sayar da wayoyin salula na hannu (Second Hand ko Fairly Used).  Wadannan wayoyi na hannu dai kala biyu ne.  Akwai wadanda daga kasashen waje ake shigowa dasu.  Wadannan su ake kira: “London Use”.  Galibinsu za ka gansu da tambarin kamfanonin waya na kasashen Amurka, irin su ‘T-Mobile”, da “Verizon”, ko kuma “AT&T”.  Sai kashi na biyu, wadanda wasu ne ke kawowa su sayar musu.  Misali, idan kana da wayar salula da kake son sayarwa, kana iya zuwa wajen masu sayar da ire-iren wadannan wayoyin salula ka sayar musu, ko dai don ka sake sayan wata a wajensu, ko ka karbe kudinka kasa a aljihu.  Ire-iren wadanda ake kawowa a sayar musu, akwai na sata.  Idan aka yi rashin sa’a mutum ya sayi na sata, tunda ba wani alama bane da ita, kuma a karshe aka gano na sata ne, to, kai fa ka shiga uku; da kai da wanda ya sayar maka, idan ma kana kusa da inda yake kenan.

- Adv -

Don haka, hanya mafi sauki ita ce, kada ka sayi wayar salula sai ka san mai ita.  Idan kuma ta kama kaje wajen masu sayar da ta hannu, to, idan ka saya kace a baka rasitin wayar, kuma ka adana.  A duk sadda wani abu ya faru, kana iya nuna wa hukuma wannan rasiti, sannan daga nan za a iya sanin inda mai sayarwa yake don a tuhume shi wanda ya sayar masa ko inda ya samu.  Amma sayan waya wajen masu sayar da ta hannu ba tare da ka karbi rasiti ba, ko kuma haka kawai kaga mutum na yawon neman wanda zai sayi wayarsa, baka sanshi ba, kuma baka san daga inda ya samo ba.  To, a gaskiya hadari ne babba ka saya.  Duk wanda zai sayar maka da waya, to, ya baka kwalin wayar, da rasitin wayar.  Idan tasa ce, kuma ka sanshi, to, matsalarka ragaggiya ce.

A karshe, yana da kyau hukuma ta sanya wa masu sayar da ire-iren wadannan wayoyi na hannu ido, ta musu rajista, ta kuma basu ka’idoji.  Ya zama suna da rajista.  Duk wanda ya kawo waya zai sayar musu, su dauki sunansa, da lambar wayarsa, da adireshinsa, da hoton katin shedar zama dan kasa (National ID Card) ko lasisin tukin mota misali.  Sannan in da hali, ya kawo kwali da rasitin wayar.  Wannan zai taimaka kwarai wajen gano masu sace wayoyin mutane suna sayarwa.  Da zarar ta sata ce, to, zai yi wahala ma a kawo musu sayarwa.  Ka ga, su kansu sun tsira daga fadawa cikin wannan musifa.

Don haka, idan har kana tunanin wayar da ka saya ta sata ce, to, hanya mafi sauki da zaman lafiya ita ce ka mayar da ita wajen wanda ya sayar maka, ka karbi kudinka.  Allah kare ka, ya kuma kiyaye mu baki daya, amin.

Assalamu alaikum Baban Sadik barka da warhaka, da fatan ka wuni lafiya.  Ina da tambaya kamar haka:  wani lokaci nakan ji wani labari ko tarihi idan aka samu wani mutum a Afirka mai ilimin kere-kere, turawa sukan zo su dauke shi su tafi da shi kasarsu don ya nuna musu yadda yake wadannan kere-keren.  Bayan ya nuna musu sai su kashe shi.  Don Allah meye gaskiyar irin  wandannan labarum?  Idan haka ne, me yasa ba sa son ‘yan Afirka su samu wannan illimi sai dai su?  Daga Abdulmajid, Libya: madjidoudjibo@gmail.com.

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Abdulmajid.  A gaskiya ba ni da tabbaci kan wannan zance naka.  Kamar yadda kaji a bakin mutane, haka nake ji wasu lokuta.  Abin da na san na taba karantawa mai kama da wannan, shi ne bayanan masana tarihin tattalin arzikin kasa, irin su Farfesa Walter Rodney, cikin shahararren littafinsa mai suna: “How Europe Underdeveloped Africa”.  Wannan littafi ya rubuta shi ne don nuna irin yadda turawan mulkin mallaka suna talauta kasashen Afirka a sadda suke musu mulkin mallaka, ta hanyar bautar dasu da kuma kwashe musu arzikin da suka mallaka, tare da kashe wadanda suka musu taurin kai.  A cewar Farfesa Rodney, wannan na cikin manyan dalilan da suka sa kasashen Afirka musamman, suke talauce.  Amma zancen cewa turawa na daukan wadanda suka kware a kere-kere su kai su kasashen su, idan suka koya musu tsarin kere-keren sannan su kashe su, ba ni da tabbaci.  Wannan shi ne abin da zan iya cewa.  Kuma da fatan ka fahimta.  Na gode.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.