Sakonnin Masu Karatu (2020) (5)

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 10 ga watan Afrailu, 2020.

105

Assalamu alaikum, barka dai. Wai me yasa kake rufe “Taskar Baban Sadik” ne wasu lokuta? – Shamsu Sani: shamsusani3333@gmail.com.

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Shamsu. Wannan ya faru ne sanadiyyar gyare-gyare da nake gudanarwa wadanda suka shafi dukkan bangarorin gidan yanar sadarwar. Kasancewar ayyuka suna mini yawa, kada in fara gyaran ta bayan fage ban rufe shafin ba, wani abu ya dauke mini hankali na tsawon kwanaki, shafin sai ya zama kamar wanda ake wa aski ne, bayan an kwashe wasu bangogin gashin kansa, sai kawai aka dauke wuta ko mai askin ya kasa ci gaba. Amma idan rufe shafin kawai nayi gaba daya, ba a iya gane gyare-gyaren sai sadda na saki shafin baki daya. Ayi hakuri. Idan Allah yaso, nan gaba duk gyara-gyaren da zan yi bazai shafi rufe shafin ba.
Da fatan Malam Shamsu ya gamsu. Allah bar zumunci, ya kuma amfanar damu abin da ake ko koyo. Na gode.

Assalamu alaikum Baban Sadik. Allah Ya albarkaci rayuwar Sadik da babansa. Don Allah ina bukatar bayani: ta yaya masu adireshin yanar gizo suke samun kudin shiga, ganin “Data” ake cirewa daga asusunmu. Na gode. – Jafar Sanusi Bena: thisisjafar001@gmail.com.

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Ja’afar. Ina godiya matuka da addu’o’inku. Masu gidajen yanar sadarwa, wanda na san su kake nufi da Kalmar “masu adireshin yanar gizo”, suna samun kudin shiga ne ta la’akari da manufar da ta sa suka bude ko gina gidan yanar sadarwar. Da farko dai yana da kyau ka san cewa shi gidan yanar sadarwa, wanda a harshen turanci ake kira: “Website”, shafi ne mai dauke da shafukan bayanai na zallar rubutu, ko hotuna, ko sauti, ko bidiyo, ko taswira na abin da ko sakon da maginin shafin yake son tallata wa duniya, ko ilmantar dasu, ko fadakar dasu, ko nuna musu. Wannan ke nuna cewa ashe ba kowane gidan yanar sadarwar bane aka bude shi don samun kudi. Misali, “Taskar Baban Sadik” dake https://babansadik.com, gidan yanar sadarwa ne da na bude mai dauke da makalolin da nake rubutawa a wannan shafi, sama da 600 a halin yanzu. Ban bude shi ko gina shi don samun kudin shiga ba, sai don baiwa masu karatu damar mallakar makalolin a duk sadda suka ga damar mallaka ko karantawa. Shafuka da dama haka suke.

Abu na biyu shi ne, gidajen yanar sadarwa da kake mu’amala dasu a waya ko kwamfutarka, ba su da alaka ko na sisin kwabo, da makamashin sadarwar (data) da kake lodawa a layin wayarka don samun siginar Intanet. Shi “data” da kake saya don samun damar mu’amala da fasahar Intanet a waya ko kwamfutarka, fa’idarsa na tikewa ne a kanka da kuma kamfanin wayar da ya samar maka. Shi kamfanin waya (kamar MTN ko Airtel ko 9Mobile) yana sayar da “data” ne don baka damar mu’amala da Intanet. Shi “data” makamashi ne mai ma’auni da ake auna maka, ka biya kudi a baka. Amma a hakikaninsa ba wani abu bane da ya wuce “damar mu’amala da Intanet” ta hanyar kwamfutar kamfanin waya, mai dauke da layi ko titin da ya hade kwamfutocin duniya masu magana ko musayar bayanai tsakanin juna.

- Adv -

Su kuma masu gidajen yanar sadarwa, in don kasuwanci aka bude su (irin su Google, da Jumia, da Yahoo) suna samun kudin shiga ne ko dai ta hanyar tallace-tallace da suke karba daga kamfanonin kasuwanci masu son a tallata musu hajojinsu. Misali mafi saukin fahimta shi ne irin alakar dake tsakanin gidajen rediyo ko talabijin ko kamfanin jaridu, da jama’a ko kamfanonin dake basu talla don a tallata musu ta kafofin sadarwar jarida, ko rediyo (sauti) ko talabijin (sauti da bidiyo). Kamfanoni irin su Google, da Yahoo!, da Microsoft misali, suna karban tallace-tallace ne daga kamfanonin duniya – har da gwamnatoci da jam’iyyun siyasa – don dorawa a shafukansu da na wadanda suke basu tallan su ma, don raba riban dasu. Masu gidajen yanar sadarwa tallace-tallace kuma, irin su Jumia da Konga misali, suna samun kudin shiga ne ta hanyar ribar da suke samu idan suka sayar da hajojinsu ga jama’a. Abu ne mai sauki, wai cire wando ta ka.

Amma kai da kake da wayar salula kuma kake sayan “data” daga kamfanin waya don kayi mu’amala da jama’a ko shafukan sada zumunta, ba abin da ya hada “data” da kake saya da kudaden shigan masu shafin da kake mu’amala da shafukansu idan ka ziyarta. Wannan shi ne takaitaccen bayani. Da fatan ka gamsu. Na gode.

Assalamu alaikum Baban Sadik, don Allah ina neman sanin yadda ake neman kalmomin sirri (Password) a manhajar Matambayi na Google ne. A taimaka mini da kuma “Master Code” na Gionee L900. Sai na ga amsa ta akwatin Imel di na. – Nafi’u Shuaibu, Zamfara State: nafiuushuaibu@gmail.com.

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Nafi’u. Kamar yadda ka sani ne, manhajar Matambayi Ba Ya Bata (Search Engine) na Google yana taimakawa ne wajen nemo bayanai, daga ko ina suke kuwa, muddin an dora su a Intanet, kuma mai neman bayanan ya san dabarun da zai iya bi wajen nemo su. Amma bayani kan yadda ake neman Kalmar sirri a jumlace, ban ce wani abu ne da zai amfaneka ko kara maka fahimta wajen kwarewa a fannin sadarwar zamani ba. Haka bayani kan gamammiyar Kalmar sirri na wayar Gionee L900, kamar yadda ka nema. Ko zan shekara ina aiko maka yadda ake neman wadannan bayanai, ba za su taimaka maka ba, sai ma dakushe maka kokari da hazakarka. A takaice dai, hanyoyi ne masu hadari, kuma marasa fa’ida, ta la’akari da irin yadda bukatarka tazo. Ba wai ina munana maka zato bane.

Dangane da haka, ina shawartarka da ka zage dantse wajen neman ilimi cikin wannan fanni na sadarwa. Idan gyaran wayar salula kake yi ko son ka fara, ya kamata ka samu makaranta ko malami na musamman wanda zai koya maka a aikace, cikin mutunci da natsuwa. Wannan zai sa ka mallaki ilimi a mahallinsa, sannan ka samu albarkarsa, wanda ba shi da iyaka. Kuma zai baka damar mallakar abin da kake son mallaka na dabarun neman bayanai ta hanyar da ta dace kuma cikin natsuwa da kiyaye doka. Amma bibiyar wadannan bayanai ta wannan hanya, a ganina, sam sam bazai taimakeka ba. Don haka, kayi hakuri don kasa baka wadannan dabaru, ba wai babu su bane, sai don ba ta wannan hanya ake mallakarsu ba. Ina fatan ka fahimceni kuma za ka gafarceni. Na gode.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.