Tsarin Amfani da Wayar Salula (2)

Kashi na 27 cikin jerin kasidun dake nazari na musamman kan wayar salula da dukkan abin da ya shafeta. A sha karatu lafiya.

361

Sakonnin Tes (SMS)

Haka manhajar sakonnin tes, wato “SMS”, tana daga cikin manhajoji masu alfanu matuka a jikin wayar salula. Tana daga cikin masarrafan da suka kara wa wayar salula shahara da karbuwa a duniya.  Domin ba a dukkan lokuta za ka iya samun mutum a waya har kuyi magana ba.  Ba wannan ba kadai, akwai sakonnin da rubuta su ya fi fadinsu da baki.  Sannan akwai lokutan da masu waya kan kashe don sanyawa a caji, ko don sun shiga wani wuri da ake bukatar kashe wayoyi a cikinsu, ko kuma sun kashe muryar wayar; duk komai na iya faruwa.  A lokuta ko yanayi irin wannan babu yadda za a yi ka iya aiwatar da sadarwar murya da abokin maganarka.  Don haka manhajar sakonnin tes take da amfani matuka.  Akwai da yawa daga cikin mutane wadanda sun gwammace ka aika musu sakon tes da ka kira su, musamman Malamai masa amsa fatawa.  Wannann ke nuna mana matukar mahimmancin wannan manhaja a jikin waya.  To meye tsarin mu’amala da wannan manhaja?

Da farko dai, ba kowa da kowa za ka rubuta masa tes ba.  Ya danganci alakar da ke tsakaninka da mutum.  Idan abokinka ne, kuma ka san ya iya rubutu da karatu, kana iya rubuta masa tes, ta amfani da dukkan dabarun gajarta rubutu (Shorthand) da ka iya; cikin harshen hausa ne, ko Turanci, ko Larabci, ko duk wani harshe da ka san ka iya kuma zai fahimta.  Haka idan ‘yan uwa ne, musamman iyaye.  Idan al’ada ne ku yi wa juna tes tsakaninka da mahaifanka, to, kana iya musu a duk sadda ka samu dama ko bukata ta kama.  Amma idan baku saba ba, to yana da kyau ka nemi jin ra’ayinsu kan haka, don kada ya zama ba su so.  Idan matarka ce babu matsala kana iya mata tes, idan ka san ta iya karatu. Haka idan akwai sako mai mahimmanci duk kana iya aika mata ta tes.  Amma duk mutumin da ka san ba zai iya fahimta ko karanta sakonka ba, bai kamata ka rubuta masa tes ba; barnan kudi kenan da lokaci.  Amma kana iya soyar masa da abin, domin ya fi saukin ma’amala.

Sakonnin tes kamar kira ne, suna bukatar jawabi.  Duk  wanda ya rubuto maka tes, idan wani abu yake bukata na bayani, wajibi ne ka rubuta ka aika masa, muddin kana da lokaci da kuma kudi a wayarka.  Domin zai yi ta sauraranka ne.  Haka idan sako ne na gaisuwa, yana da kyau ka rubuta masa shi ma cewa ka samu sakonsa, kuma kana godiya.  Idan sako ne irin wanda ake turowa daga wannan zuwa wancan, wato “Chain Messages” ko “Forwarded Messages,” irin wadannan sakonni suna daukan dayan fuska uku ne; na farko su ne sakonnin addu’o’i ko hadisai ingantattu, wadandan ana iya tura wa kowa.  Idan wani ya turo maka wadannan, kana iya masa godiya, sannan ka tura wa wani. Domin babu suna a jikinsu, kowa na iya karantawa.

Na biyu su ne wadanda suka kunshi fadakarwa kamar na baya, amma ta hanyar hadisan da basu inganta ba, ko labarun da suka kunshi wasu abubuwan da shari’a bata yarda da su ba.  Irin wannan idan aka turo maka, kuma ka san kuskuren da ke cikinsu, to ba za ka tura wa wani ba.  Sai dai ka fadakar da wanda ya turo maka kuskuren da ke cikin sakon.  Watakila shi bai sani bane, shi yasa.  Ma’ana fatan alheri yake maka.  Misali, kwanakin baya akwai sako da yayi ta yawo cewa wata mata da ba musulma ba ta yi mafarkin Manzon Allah ya umarce ta da yin wasu abubuwa, wanda bayan ta farka, sai ta musulunta, sannan tace manzon Allah yace dole ne kowa yayi su, duk wanda bai yi su ba, to, zai ga tashin hankali a rayuwarsa.  Wannan sakon wani mai karatu ya turo mini, sai na fadakar da shi kuskuren da ke ciki.

Na farko dai yin mafarkin Manzon Allah abu ne mai yiwuwa.  Amma idan a cikin mafarkin aka ce wai wanda aka gani a matsayin Manzon Allah yace a yi wasu abubuwa wadanda suka saba wa shari’a, to a nan ba za a yi ba.  Kuma hakan ke nuna cewa lallai wanda aka gani a mafarkin nan ba Manzon Allah bane. Domin Manzon Allah ba zai taba umartan wani daga cikin mabiyansa da wani sabon shari’a ba, ko abin da ya saba wa shari’a ba.  Shi yasa ma Malamai suka ce duk wanda yace yayi mafarkin Manzon Allah, to sai an tambaye shi ya sifata shi.  Idan ya sifata Manzon Allah daidai da yadda hadisai suka nuna siffarsa, to a nan sai a yarda cewa lallai shi ya gani.  Amma idan ya siffata shi da wani siffar da ba tasa ba, to, lallai ba Manzon Allah ya gani ba.  Shedan ne kawai yake wasa da shi.

- Adv -

Sannan dukkan Malamai sun yarda cewa ba a amfani da mafarki wajen tabbatar da shari’a sai idan abin da mafarkin ya kunsa yayi daidai da shari’a tabbatacciya.  Idan ya saba ba za a karba ba.  Domin Annabawa ne kadai mafarkinsu ke zama wahayi, ba gama-garin mutane ba.  Sannan duk wanda ya turo maka sako cewa ka tura wa mutane adadi kaza, idan baka tura ba abu kaza da kaza zai same ka.  Don Allah ka tambaye shi, shin, Allah ne ya saukar da wahayi kan haka, ko Manzon Allah?  Meye hujjarsa kan haka?  Domin akwai masu turo wa jama’a sakon wasu addu’o’i su ce dole a tura wa mutane kaza, wane ya tura wa wasu, ya samu alheri, wane bai tura ba, abu kaza mummuna ya same shi.  Duk wannan shirme ne. Sai a kiyaye.

Nau’i na uku kuma shi ne sakon tes mai dauke da shagube da cin mutuncin wani, ko wasu nau’ukan mutane ba tare da hakki ba. Kamar shugabanni, ko wasunsu.  Wadanda kuma labaru ne kirkirarru ba gaskiya bane, ana yada su ne don nishadi.  A gaskiya sakonni irin wadannan ba a tura wa wasu.  Domin akwai giba da cin naman wani a ciki.  Mu kiyaye.  Kada mu dauka abin da muka fada da baki ne kadai Allah zai kama mu da laifinsa, a a, duk wata gabar jikinka da kayi amfani da ita wajen yada barna ko shiga hakkin wani, to sai an kama mutum da laifi a kan haka, sai in ya tuba Allah Ya yafe.

Yana da kyau idan ka aika sakon tes ka tabbata sakon ya isa daga jikin wayarka, ma’ana akwai sakon isarwa, wato “Delivery Report” mai nuna cewa sakonka ya isa.  Idan yana nuna yana kan hanya, wato “Pending” to ka san cewa akwai matsalar yanayin sadarwa.  Ta yiwu sakon ya isa, ta yiwu kuma bai isa ba. In so samu ne ka sake aikawa zai fi kwanciyar hankali.  A wasu lokuta kuma tana iya yiwuwa wayar da za ta karbi sakon a kashe take.  Sannan, iya tsawon sakonka, iya yawan kudin da za a cire.  Daga layin MTN zuwa wani MTN din ana cire Naira 5 ne, a sako madaidaici kenan.  Idan ya kai shafi biyu, za a cire naira goma ne.  Idan shafuka biyar ne, naira ashirin da biyar kenan.  Amma idan daga MTN zuwa wani layi ne daban, misali zuwa Etisalat, za a cire maka naira 10 ne a shafi daya.  A shafuka biyar kuma naira 50.  Haka abin yake a sauran layuka.

Daga cikin ‘yan kananan matsalolin da ake samu wajen aika sakonnin tes akwai matsalar lambar cibiyar sadarwa, wato “Center Number.”  Kowane kamfanin waya na da lambobi na musamman da ake amfani da su wajen aiwatar da sadarwa tsakanin wata waya da wata wayar salula ta hanyar manhajar SMS.  Wadannan lambobi dai guda 13 ne.  Misali, na kamfanin Etisalat su ne: +2348090001518, na kamfanin MTN kuma: +234803000000, na kamfanin kuma su ne: +234802000009.  Wadannan lambobi ana samunsu ne a bangaren tsare-tsaren aika sakonnin SMS na jikin kowace wayar salula, wato “Message Settings.”  Sai dai kuma, ba da su wayar ke zuwa ba.  Asali suna cikin katin SIM ne.  da zarar ka shigar da katin SIM a cikin wayar da ka sayo, nan take sai wayar ta nado su, don taimaka maka aiwatar da sadarwa cikin sauki.

Duk sadda kayi ta kokarin aika sakonnin tes, ana ce maka ba a samu, alhali a jikin wayarka ta nuna an aika, to, hakika akwai matsalar lambobin cibiyar aika sakonni.  Ta yiwa sadda kake wasa da wayar a wasu lokuta ko yara sun dauka suna ta tabe-tabe, har suka goge lamba ko sama da haka daga cikin lambobi 13. Muddin basu cika 13 ba, ko kuma aka goge wani aka sa wanda ba daidai ba, har abada ba za ka iya aika sakonnin tes ba.  Sai a kiyaye.  Amma idan aka duba aka tabbatar da lambobin daidai suke, kuma ga sakonni sun ki zuwa, to, akwai matsalar yanayin sadarwa (Network Problem), ko kuma babu isasshen kudi a wayar.  Sai a rika lura.

A karshe, yana da kyau mai karatu ya lura cewa, sakonnin tes sun fi kira irin na murya hadari idan lalura ta taso.  Da farko, da zarar ka matsa “Send”, sakon ya tafi.  Ko da kuwa ka ga an rubuta: “Sending”, watakila kace bari in tsayar, aikin banza ne.  Kai, ko da cire batirin wayar kayi a yayin da ake aikawa, duk aikin banza ne.  Sakon ya riga ya tafi tuni.  Idan ka aika sako, ana iya ciro sakon daga kwamfutocin kamfanin wayarka a kowane lokaci ne.  Sannan ko da kuwa ka goge sakon a wayarka, yana nan a jikin kwamfutocin kamfanin waya.  Za a iya ganinsa, tare da lokacin da ka aika, da kuma mizanin sakon, da lokacin da sakon ya dauka kafin ya isa wayar wanda aika masa.  Don haka sai a kiyaye wajen rubuta abin da za a aika.

Cikin shekarar da ta gabata ne aka gabatar da wani kuduri a majalisar dattawa na kasa, wadda ke neman majalisar ta amince a rika amfani da sakonnin tes da na Imel a matsayin sheda a kotu.  Har yanzu ba a gama tattaunawa kan wannan kuduri ko ba.  Idan aka amince da wannan kuduri, hakan zai nuna cewa sakonnin tes sun zama amintacciyar hanyar tabbatar da hujja kenan a kotu a ko a wajen jami’an ‘yan sanda.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.