Web 3.0: Fasahar “Blockchain” (1)

Kamar yadda na sanar a sama, daga wannan mako zuwa makonni biyu dake tafe za mu yi nazarin Fasahar Blockchain ne, tare da alakarta da tsarin wannan marhala da muke fuskanta na sadarwa, da kuma tsarin hada-hadar kudi ta hanyar na’urori da hanyoyin sadarwa na zamani, wato: “Cryptocurrency”, musamman ma fasahar Bitcoin. – Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 13 ga watan Mayu, 2022.

293

Matashiya

Idan masu karatu basu sha’afa ba, a watan da ya gabata kafin mu amsa tambayoyi da wasu labarai, muna nazari ne kan sabuwar fasahar giza-gizan sadarwa na duniya nau’i na 3, wato: “Web 3.0”.  A makalar farko munyi matashiya kan alakar wannan sabuwar fasaha da wadanda suka gabaceta.  Inda nayi takaitaccen bayani kan nau’in Intanet na farko, wato: “Web 1.0”, da siffofinta, da kuma nakasar da take dauke dashi, idan aka kwatanta da wadanda suka zo bayanta.  Haka ma munyi takaitaccen bayani kan nau’in Intanet na 2, wato: “Web 2.0”, da fa’idojin da fasahar ke dauke dasu, da kuma kalubalen da a halin yanzu muke fuskanta.  Wadanda su ne dalilan da suka sa a halin yanzu ake yinkurin samar da kashi na 3, wato: “Web 3.0”.

A bangaren fasahar giza-gizan sadarwa nau’i na 3 (Web 3.0), na gabatar da makaloli har guda 3, akwai fasahohi kusan guda 5 da su ne ake sa ran za su jagoranci ci gaban da wannan marhala ke dauke dashi.  Na farko ita ce fasahar “Artificial Intelligence”, wacce muka gabatar da makaloli na tsawon makonni 3.  Sauran fasahohin dai su ne: Fasahar “Blockckain”, wanda a wannan mako da makonni biyu dake tafe zamu yi nazari a kai, sai fasahar “Metaverse”, da fasahar sadarwar wayar salula ta 5G – a baya munyi nazari kan wannan fasaha cikin makonni kusa ngoma da doriya, a wannan karon takaitaccen nazari za mu yi, wanda zai bayyana alakar dake tsakanin fasahar da wannan marhalar giza-gizan sadarwa ta 3, wato: “Web 3.0”.  Fasaha ta karshe da za mu yi nazari kanta ita ce fasahar “Edge Computing”, wacce za ta taimaka wajen kusantar da bayanai ga jama’a don samunsu cikin lokaci da kuma inganci, sama da yadda muke ta’ammali dasu a halin yanzu.

Kamar yadda na sanar a sama, daga wannan mako zuwa makonni biyu dake tafe za mu yi nazarin Fasahar Blockchain ne, tare da alakarta da tsarin wannan marhala da muke fuskanta na sadarwa, da kuma tsarin hada-hadar kudi ta hanyar na’urori da hanyoyin sadarwa na zamani, wato: “Cryptocurrency”, musamman ma fasahar Bitcoin.  Bayani ya gabata cewa wannan marhar sadarwa ta “Web 3.0”, tsarinta ya sha bamban da sauran marhalolin sadarwa ta bangaren Intanet.

Fasahar “Blockchain”

- Adv -

Fasahar “Blockchain” dai tsari ne da ya kunshi gamammen runbun adana bayanai a Intanet, mai cike da kariya da aminci, kuma duk bayanan da aka adana a cikinsa, babu mai iya canza shi.  Bayan haka, wannan tsari yana cin gashin kansa ne; ma’ana babu wata hukuma da ko gwamnatin wata kasa ko wani kamfani da yake kula dashi ko kayyade tsarin ma’amala a kansa.  A kan wannan tsari na Fasahar “Blockchain” ne ake aiwatar da cinikayyar hada-hadar kudi na Bitcoin, da Etha da sauran nau’ukan kudaden zamani da ake amfani dasu ta hanyar Intanet kadai.

Wannan fasaha ta “Blockchain” dai tana cikin manyan ginshikan da za su tabbatar da tsarin alakokin kasuwanci tsakanin mutane da kintsa tsarin ayyukan hukumomin kasashe, da kuma manyan kamfanoni.  Ba don komai ba, sai don tsari ne da zai magance wasu daga cikin manyan matsaloli da kalubalen da duniya ke fuskanta a tsarin mu’amala a giza-gizan sadarwa ta duniya na marhala ta biyu da muke ciki yanzu, wato: “Web 2.0”.  Wadannan matsaloli kuwa sun hada da rashin amintuwa da juna, saboda matsalar zamba cikin aminci.  Da tsaiko da ake samu wajen tantance hada-hadar kudi a tsarin harkokin kudade na al’ada da muke amfani dasu a yau – wanda ya shafi bankunan kasuwanci da manyan bankuna kasashe – da matsalar rashin ingancin bayanai saboda kutse da a kullum kamfanoni ko jama’a ke fama dashi a shafukansu na Intanet, da dai sauran matsaloli.

Siffofin Fasahar “Blockchain”

Karkashin tsarin Fasahar “Blockchain”, kamar yadda na sanar a sama, cewa tsari ne mai dauke da cikakkiyar kariya da tsaro, abin bai tsaya a nan kadai ba.  Wannan tsari na dauke da manyan siffofi ne guda hudu.  Ga bayanin wadannan siffofi nan kamar haka:

Rumbun Adana Bayanai

Wanna shi ake kira “Database” a harshen fasahar sadarwa na zamani.  Amma ya sha bamban da irin rumbun adana bayanai na al’ada da aka sani kafin shekarar 2008 (wadanda kuma har yanzu ake amfani dasu).  A yayin da rumbun adana bayanai na al’ada suke adana bayanai a tsarin jadawali (wato: “Tables”), a tsarin Fasahar “Blockchain” ana adana bayanai ne a tsarin “Gungu-gungu”, wato: “Blocks”, ko “Chunks”.  Duk sadda wani ya shigar da bayanai a wannan rumbu, nan take ake za a dunkule shi zuwa gungun bayanai, wato: “Block”, sannan a hade shi cikin jerin gungun bayanan dake gudanuwa a tsarin, kai tsaye.  Shi yasa ake kiran tsarin da suna: “Blockchain”, wato: “Sarkar gungun bayanai”.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.