Sakonnin Masu Karatu (2020) (3)

Tsarin "Flashing" da "Rooting" Wayar Salula

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 27 ga watan Maris, 2020.

75

(Ci gaban tambayar makon shekaranjiya ce)

Hard Reset

Hanyar gyaran waya na yi-da-kanka na gaba shi ake kira: “Hard Reset”. Wannan tsari aikinsa daya ne da wanda ya gabace shi. Bambancin dake tsakaninsu kawai shi ne: tsarin “Factory Reset” ana motsar dashi ne ta cikin wayar, kamar yadda na siffata a sama. Shi kuma tsarin “Hard Reset” ana aiwatar dashi ne ta wajen wayar salula. Wato ta amfani da maballan waya. amma duk tasirinsu daya ne. Wani na iya cewa in kuwa haka ne, to, meye kuma na kawo wannan? Amfanin wannan shi ne, a wasu lokuta wayarka na iya shiga matsala mummuna, ta zama a sume, ta mace gaba gaba daya; ba ka iya kunnawa ta tsaya daram. Hakan kan faru idan kwayar cuta ta kama ta, misali, ko wata matsala da ka iya jefa ta cikin irin wannan yanayi. Ko kuma wasu daga cikin bayanan babbar manhajar wayar dake motsa ta idan aka kunna (System boot files), suka gurbace. Ta wannan hanya ana iya gyara ta in abin bai wuce gona da iri ba. Bayan haka, akwai wasu damammaki ma da wannan tsari ke bayarwa, wanda tsarin “Factory Reset” ba ya bayarwa, wajen gyaran waya cikin sauki.

Yadda ake iya gyaran wayar da ta birkice ta amfani da wannan tsari dai ya danganci nau’in wayar, da kamfanin da ya kera ta, da kuma zamanin da aka kera ta. Amma cikin sauki dai, gama-garin hanyar da ake bi dai shi ne: idan wayar a kunne take, sai a kashe ta, ta hanyar matsa maballin kashe wayar dake waje, wato: “Start Button”. Idan ta mace gaba daya, sai hada maballin kunna waya (Start Button), da maballin rage sauti (Volume Down) ka matsa ka rike su tsawon dakiku 10 zuwa 15, har sai ka ga tambarin kamfanin wayar ya nuno, alamar tana gab da kunnuwa Kenan – kana iya gane hakan ta hanyar diri ko jijjiga da za ta yi – daga nan sai ka saki maballin rage sauti, kaci gaba da rike maballin kunna wayar; da zarar ka ga ta nuna: “Android System Recovery”, sai ka saki. A wata wayar kuma za ka rike dukkan maballan ne ko da ka ga tambarin kamfanin waya baza ka saki daya daga cikinsu ba, har sai ka ga alamar “Android Sytem Recovery” sannan ka saki.

Da zarar wayar ta iso wannan mataki, sai kayi amfani da maballin sautin waya na sama ko na kasa, wajen haurawa ko gangarawa nau’ukan bayanan dake shafin. Akwai zabi kamar haka: “Reboot system now”, wanda zai baka damar sake kunna wayar. Sai “Apply Update from ADB”, wanda ke baka damar dora wa wayar bayanan babbar mabhaja don sabunta su, idan hakan bai yiwuwa ta hanyar wayar. Sai “Wipe data/Factory reset”, wanda shi ne ke gudanar da aikin “Factory Reset”, kamar yadda sunan ya nuna. Sai “Wipe cache partition”, wanda kai tsaye zai share dukkan bayanan ta taskance masu tuna mata da matakan da take bi wajen aiwatar da ayyukan da mai waya ya saba yinsu. Sai bangaren “Reboot to bootloader”, wanda zai sake kunna wayar, amma ta amfani da wata babbar manhaja da ake son ta hau, kai tsaye. Sai kuma “Power down”, wanda in ka matsa zai kashe wayar ne kai tsaye. Sai kuma “Update from SD Card”, idan kana bukatar sabunta babbar manhajar wayar ta hanyar ma’adanar wayarka.

Tunda goge tsare-tsaren wayar zaka yi, sai ka zabi “Wipe data/Factory reset”, ta hanyar maballin kunna wayarka, nan take wayar za ta kashe kanta. Da zarar ta gama komai sai ka zabi “Reboot System Now”, wannan zai sa wayar ta mutu sannan ta sake kunna kanta kai tsaye, bayan aiwatar da abin da aka umarceta.

- Adv -

Tsarin “Flashing” da “Rooting”

A wasu lokuta idan matsalar ta girmama, amfani da hanyoyin da suka gaba bai warkar da wayar, sai an mata mai gaba ta hanyar filashin, kamar yadda muke fada a harshen namu. Kalmar “Flashing” wani tsari ne da ake amfani dashi wajen sauya wa wayar salula wasu siffofi daban, ko wajen warware matsalar dake damunta, wanda sauran hanyoyin da na zayyana a baya basu iya warwarewa. Da farko dai, wasu sun dauka Kalmar “Rooting” da “Flashing” duk ma’anarsu daya ce. Ba haka lamarin yake ba.

“Rooting,” wanda na dade da yin bayani mai tsayi akansa a baya, shi ne balle dukkan wata kariya da kamfanin wayar salula ya gina a jikin wayar, wanda bai baiwa mai amfani da waya damar aiwatar da wasu abubuwa, kamar cire wasu manhajojin da wayar tazo dasu, da goge wasu bayanai, da loda wa wayar wasu manhajoji ba ta asalin hanyar da ake loda mat aba (irin su Play Store dsr). A takaice dai, ya zama an zaftare wa wayar salula dukkan wasu kariya da magininta ya bata, shi ake kira “Rooting”. Shi kuma “Flashing” hanya ce da ake bi wajen aiwatar da tsarin “Rooting” cikin sauki. Ma’ana, samun damar farke babbar manhajar wayar salula don aiwatar da wasu ayyuka wadanda asalin magininta bai bata daman yin hakan ba, yana yiwuwa ne ta hanyar “Flashing” babbar manhajar wayar. Wannan daya daga cikin aikin aikin “Flashing” da ake wa wayar salula.

Sauran hanyoyin sun hada da goge tsare-tsaren wayar, kamar yadda ake ta hanyar “Factory Reset” da “Hard Reset”. Haka kuma idan wayarka ta samu matsala, ta kasa tashi ko kunnuwa sanadiyyar kwayar cuta da ta kama ta ko gurbacewar bayanan babbar manhajar wayar, ana iya amfani da tsarin “Flashing” wajen loda mata asalin bayanan wayar masu inganci don farfado da ita.

Sabanin tsarin “Factory Reset” da ake iya gudanar dashi ta wayar salula kai tsaye, daga cikin babbar manhajarta ko daga waje, tsarin “Flashing” ba ya yiwuwa sai ta amfani da kwamfuta, da asalin wayar salular da ake son gyarawa, da wayar musayar bayanai (USB Cable) irin na wayar salular, da kuma manhajar da ake son loda wa wayar, don farfado da ita ko kuma inganta ta.

Wannan, a takaicen takaitawa, shi ne bayani kan bambancin dake tsakanin wadannan hanyoyin gyara wayar salula. Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.