Sakonnin Masu Karatu (2020) (2)

Tsarin "Soft Reset" da "Hard Reset"

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 20 ga watan Maris, 2020.

63

(Ci gaban tambayar makon jiya ce)

Hanyoyin Gyara Waya a Sawwake

Kamfanonin wayoyin salula, kamar yadda na sanar a farko, sun samar da hanyoyin warware ire-iren matsalolin da bayaninsu ya gabata a baya, cikin sauki.  Wadannan hanyoyi dai suna da yawa, kuma hawa-hawa ne.  Ga takaitaccen bayani nan kan shahararru daga cikinsu, tare da bambance-bambancen dake tsakaninsu.  Kamar yadda na sanar da farko ne, matakan sun fi wadanda ka zayyana a sama yawa:

Tsarin Soft Reset

A tsarin sadarwar wayar salaula, kalmar “Soft Reset” na ishara ne ga tsarin sake kunna waya don samar mata da nishadi, idan lafiyarta lau, ko kuma gyatta wasu yan kananan matsaloli da suka shafi yanayin sadarwa, ko sauti ko kuma sumewar wasu manhajoji na dan kankanin lokaci.  Da zarar ka kashe wayar ka sake kunna ta, mafi yawancin lokuta wadannan matsaloli sukan tafi.  Bayan haka, yana da kyau ka rika kashe wayarka ma kana sake kunna ta, ko da babu komai.  Don wannan na kara mata nishadi, sannan yana bata damar wartsakewa ta zama wasai.  Wannan hanyar magance matsala a waya bai da wata matsala idan anyi, ma’ana bazai goge maka bayanan dake wayarka ba, haka ma ba zai goge maka wata manhaja ko sauya tsare-tsaren da ke dora wayarka a kai ba, wato: “User Settings” kenan.

- Adv -

A harshe mafi saukin fahimta, akan kira wannan tsari da suna: “System Restart” ko “Reboot”.  Ba wani abu yake nufi ba illa kashe wayar da sake kunna ta, bayan tazarar dakiku (seconds) 10 zuwa 15.  Idan kuma ta sandare ko ta sume, ta inda ba ka iya sarrafa ta, hanya mafi sauki shi ne ka cire batirinta, in zai yiwu, sannan ka sake mayar dashi bayan dakiku 10 zuwa 15.  Wannan shi ake kira: “2nd Level Soft Reset”.

Tsarin Factory Reset

Mataki na biyu shi ne: “Factory Reset” ko “System Reset”.  Wannan ita ce hanyar da ake amfani da ita wajen goge tsare-tsaren wayar salula ta hanyar mayar da ita “sabuwa” kamar yadda tazo a farkon sayenta.  Mai karatu na iya fahimtar haka daga sunan.  Tasirin wannan hanyar gyara waya shi ne, idan kayi, duk tsare-tsaren da ka dora wayar a kai (User Settings) zasu goge.  Duk manhajojin da ka saukar a kan wayar, zasu goge.  Duk bayanan da manhajar wayar ta adana sanadiyyar amfani dasu da ake yi, wato “Application Data”, za su goge.  Manhajojin Imel da ka dora a wayar, da adireshin Imel dinka kake karban sakonnin Imel dasu, duk zasu goge.  A karshe, idan ka taba sabunta babbar manhajar wayar, wato: “System Update”, duk bayanan dake da alaka da hakan, su ma zasu goge.  Misali, idan kana amfani d waya mai dauke da babbar manhajar Android 9, sai ka sabunta babbar manhajar zuwa Android 9.1, ko Android 10 misali, da zarar ka yi “Factory Reset”, za ta koma asalin zubin babbar manhajar da tazo dashi a farko.  A takaice dai, yadda aka kera wayar a farkon lamari, haka za ta koma.

Dangane da wayar, abu daya ne kawai wannan hanyar gyaran waya ba ta iya yi, shi ne goge asalin bayanan babbar manhajar wayar, wato: “System Files”, da sabunta su kamar yadda suka zo a farko.  Don haka, idan wayar ta kamu da kwayar cutar wayar salula wato: “Virus”, kuma hakan ya gurbata wasu bayanan babbar manhajar wayar, wannan hanya ta “Factory Reset” ba za ta iya gyara su ba.

Bayan haka, wannan hanya na da alaka ne kai tsaye da tsare-tsaren waya (Settings) da dukkan bayanan da suka shafe su. Don haka, idan kana da bayanan da ka saukar, na sauti ko bidiyo ko tsagwaron bayanai akan wayarka, wannan tsari bazai taba su ba.  Haka idan kana da ma’adanar bayanai da ka kara wa wayar, wato: “Memory Card”, dauke da bayanai a ciki, ita ma ba za a taba ta ba.  Wani abin farin ciki ma shi ne, mai waya na iya aiwatar da wanann tsari na gyaran waya, ba wani abu bane mai wahala.  Idan kana amfani da wayar Android ne, kaje bangaren “System”, ka gangara “Advanced”, sai ka matsa “Reset”, za a budo maka zabi uku: “All Settings”, wanda zai goge iya tsare-tsaren da ka sa wa wayar kadai, sai “Network Settings”, wanda zai goge iya tsare-tsaren da suka shafi tsarin sadarwa kadai, sai kuma “Reset Phone”, wanda aikinsa shi ne goge dukkan tsare-tsare da bayanan da ka loda wa wayar, kamar yadda bayani ya gabata.  A wasu wayoyin kuma daga “Settings” za ka je “System” sai kaje “Reset”.  Kana matsa “Reset” za a bukaci ka sanya Kalmar sirrin da wayar ke amfani dashi, wato PIN, ko kuma tambarin hannu ko kuma zanen kariya (Pattern Lock), don ba da umarnin aiwatar da tsarin.  Kana shigar da Kalmar sirrin, nan take za a tambayeka: “Erase Everything?”, wato: “Ka yarda a goge komai?”  Kana matsa eh, shikenan, wayar za ta kashe kanta cikin dakiku 5 zuwa 10.  Sai ta sake kunna kanta bayan ta aiwatar da abinda aka umarceta da yi.

Akan yi amfani da Kalmar “Master Reset” don nufin “Factory Reset”, don nuna gamewar tasirin wannan tsari.  Duk dai abu daya sunayen biyu ke nufi.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.