Nazari Kan Karin Harajin Kudin Kiran Waya Da Na “Data”

An kiyasta cewa idan wannan sabuwar doka ta Karin haraji ta fara aiki, kamfanonin wayar salula za su kara yawan kudin da suke caja na kiran waya a duk minti guda; daga naira ashirin (N20.00) ko kasa da haka da suke cira a yanzu, zuwa naira arba’in (N40.00).  Haka ma, gigabyte 1 na “data” da a yanzu ake saya a kan naira dubu daya (N1,000.00) a misali, zai koma naira dubu biyu da dari biyar (N2,500.00). – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 19 ga watan Agusta, 2022.

241

A makon da ya gabata ne Babbar Ministan Kudi da Tsare-tsaren Tattalin Arzikin Kasa, Hajiya Zainab Ahmed Shamsuna, ta sanar da kudurin gwamnatin tarayya na kara harajin kudin kiran waya da na damar amfani da fasahar Intanet ta hanyar wayar salula, abin da a harshen turanci aka fi sani da: “Data”, da kashi 5 cikin 100 (5%).  Ministan ta sanar da hakan ne a taron masu ruwa da tsaki a fannin sadarwar wayar salula a Najeriya.  Inda ta kara da cewa, wannan kari dai daman yana cikin sabuwar Dokar Hada-hadar Kudade na shekarar 2020 (Finance Act, 2020), wanda aka rattafa wa hannu shekaru biyu da suka gabata, wanda kuma sanadiyyar tanade-tanadensa ne aka samu karin harajin kayayyaki (Value Added Tax – VAT) daga kashi 5 zuwa kashi 7.5 (5% zuwa 7.5%).

Hajiya Zainab dai ta kara da cewa, wannan kari na kashi 5 da za a ci gaba da karba, zai fara aiki ne nan ba da dadewa ba, kuma tuni Hukumar da take shugabanta ta sanar da dukkan hukumomin gwamnati da kuma kamfanonin sadarwar da abin ya shafa.  Illa dai ranar da za a fara aiwatar da dokar ne ake kan tattaunawa tsakaninta da sauran masu ruwa da tsaki a fannin sadarwar.  Kuma harajin zai shafi kudin kiran waya ne, da na amfani da “data.  Abin da wannan ke nufi shi ne, idan ka kira waya, daga cikin kudin da za a cire, akwai wannan kashi 5.  Haka idan ka sayi “data”; duk sadda kayi amfani dashi ana cajanka kudin damar da aka baka ne na amfani da fasahar Intanet a wayarka, kuma daga cikin kudin da za a caje ka, akwai wannan kashi 5 na haraji.

A nashi bangare, kamar yadda jaridar Daily Trust da sauran jaridun Najeriya suka ruwaito, Kungiyar Masu Amfani da Layukan Wayar Salula ta Kasa, wato: “National Association of Telecoms Subscribers”, Cif Adeolu Ogunbanjo, ya nuna bakinsa da wannan kuduri na Karin harajin kudin kiran waya da na “data”, yana mai bayyana cewa akwai rashin damuwa da halin da ‘yan kasa ke ciki, da kuma yanayin da tattalin arzikin kasa ke ciki.  Wannan, a cewarsa, ba shi ne lokacin da ya dace da wannan kari ba.

A bangaren kamfanonin wayar salula su ma, sun bayyana ra’ayi makamancin wannan.  Inda suka kara da cewa, wannan kari na haraji wani Karin nauyi ne ga fannin sadarwa a Najeriya, domin a halin yanzu ma akwai nau’ukan haraji guda 39 da kamfanonin sadarwa ke dauke dashi.  Bayan haka, yawaitan nau’ukan haraji kan kamfanonin sadarwa na iya kore masu zuba jari a wannan fanni mai matukar mahimmanci ga rayuwar al’umma.  Ba wannan kadai ba, yawaitan haraji na iya sa kamfanoni su rage ma’aikata, don rage dimbin kudin da suke kashewa wajen tafiyar da kamfanin.  Domin wannan kari zai rage adadin lokaci da “data” da masu amfani da wayar salula ke saya.  Kai, wasu ma na iya rage adadin layukan da suke amfani dasu – misali, daga layuka 2 ko 3, zuwa layi 1 kacal.  Hakan ne zai rage adadin kudin shiga ko ciniki da wadannan kamfanoni ke samu a duk wata.

An kiyasta cewa idan wannan sabuwar doka ta Karin haraji ta fara aiki, kamfanonin wayar salula za su kara yawan kudin da suke caja na kiran waya a duk minti guda; daga naira ashirin (N20.00) ko kasa da haka da suke cira a yanzu, zuwa naira arba’in (N40.00).  Haka ma, gigabyte 1 na “data” da a yanzu ake saya a kan naira dubu daya (N1,000.00) a misali, zai koma naira dubu biyu da dari biyar (N2,500.00).

- Adv -

Dalilan Gwamnati

Ministan Kudi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki ta ce dole ne gwamnati ta aiwatar da wadannan sauye-sauye saboda fadada hanyoyin samun karin kudaden shiga don gudanar da ayyukan gwamnati da ayyukan ci gaban kasa.  Wannan ya biyo bayan kudurin gwamnatin tarayya ne wajen yaukaka aljihun gwamnati ta wasu hanyoyin daban, sanadiyyar rashin tabbas dake fuskantar kasar a fannin kasuwancin gurbataccen mai.

Shawarwari

Ta la’akari da halin da tattalin arzikin kasa ke ciki ba wai a Najeriya kadai ba, duniya gaba daya, zai dace gwamnatin tarayya ta sake tunani kafin aiwatar da wannan kari na haraji.  Bayan karancin kudi da jama’a ke fama dashi, darajar Naira ta zagwanye biyo bayan hauhawan farashi (Inflation) da muke fama dashi.  A ka’idar tattalin arzikin kasa a nazarce, mafi munin yanayin tattalin arziki da kowace al’umma za ta samu kanta a ciki shi ne, ya zama an samu hauhawan farashin kayayyaki, tare da rashin aikin yi.  Wannan yanayi shi ake kira: “Stagflation”.  A yanayi irin wannan kuwa, kamata yayi hukuma ta tallafa wa al’umma ta dukkan hanyoyin da za ta iya, amma ba kara karban abin da ke hannunsu ba.  A kasar Amurka misali, dauke haraji ma gwamnati tayi daga kayayyakin masarufi irin su iskar gas na dafa abinci da sauransu.

Amfani da wayar salula a halin yanzu ya zama lalura.  Akwai layukan wayar salula sama da miliyan 170 masu rai, a Najeriya, a halin yanzu.  Da yawa cikin mutane kanyi amfani da wayar salula wajen kasuwanci, da sada zumunci, da neman aikinyi don toshe lalurar rayuwa.  Kara haraji a wannan fanni zai kara kuntata wa jama’a, kari kan halin da suke ciki a yanzu.  Muna sa ran Hukuma za ta dubi wannan lamari da fuskar tausasawa ga al’umma.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.