Sakonnin Masu Karatu (2020) (18)

Tsarin Rediyon FM da AM a Wayar Salula (2)

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 13 ga watan Nuwamba, 2020.

111

(Ci gaban amsar tambayar makon jiya)

Da wadannan na’urori da bayaninsu ya gabata wayar salular zamanin yau ke iya lalubo tashoshi don jiyar da mai wayar salula shirye-shiryen rediyo a zangon FM cikin sauki. Da sauti rau-rau, ba ya rawa kuma ba ya yankewa. Kuma kamar yadda bayani ya gabata a baya, wadannan su ne manyan dalilan dake sawwake wa masu kera wayoyin salula har su iya dora fasahar rediyo mai amfani da zangon FM a wayoyin salular zamanin yau. Wannan ke sa ka iya kamo tasha cikin sauki, kaji sauti ingantacce, sannan duk inda wayarka take, kana iya saurare ba tare da samun katsalandan din yanayin sadarwa ba.

Zangon AM a Wayar Salula

A yayin da wayoyin salula ke zuwa dauke da rediyo mai iya kamo tasha a zangon FM, babu wata wayar salula mai dauke da rediyo dake iya kamo tashoshi a zangon AM, ko SW, ko ma MW. Meye dalili? Akwai manyan dalilai kamar guda uku. Biyu daga cikin dalilan nan sun shafi bangaren kimiyya ne. Na ukun kuma ya shafi bangaren kasuwanci ne.

Dalilin farko shi ne, su shirye-shiryen rediyo ana watsa su ne a zangon gudanarwa. Wannan shi ake kira: “Radio Band”. Kalmar “Radio Band” na nufin tasha ce ko titin da siginar rediyon dake dauke da sautin masu gabatar da shirye-shirye yake gudanuwa a kai; daga ma’aika zuwa makarba. Wannan mahalli yana dauke ne da lambobi dake nuna Zangon da mai sauraro zai lalubo shirye-shiryen da yake son sauraro, ko tashar dake aiwatar dasu. Na san mai karatu ya saba jin masu gabatar da shirye-shiryen rediyo suna cewa: “Za a iya lalubo mu a mita 90, ko mita 45, ko mita 25, ko mita 35 don sauraron shirye-shiryenmu,” misali.

- Adv -

Wadannan lambobi duk suna dauke ne a wannan tasha da ake kira da suna: “Radio Band.”
Su kuma wadannan zanguna sun kashu kash-kashi ne. Akwai masu fadi, da tsayi, wadanda duk nisan inda gidan rediyo yake, za ka iya kamo tashar, kuma ka saurari shirye-shiryensu da suke yi. Wannan dabaka shi ne zangon AM, wato: “Amplitude Modulation.” Sannan akwai zangon dake biye da na AM, wadanda suke su ma masu fadi ne amma basu kai girman na farko ba. Su kuma su ne ke dauke da zangon SW (Short Wave), da kuma MW (Medium Wave). Idan mai karatu ya dauki akwatin rediyo, ya kalli fuskar akwatin, daidai wajen da ke dauke da lambobi tashoshi, zai ga zanguna guda hudu ne. Akwai AM, sai MW, sai SW, sa kuma kuma FM. Wadannan zanguna, duk suna dauke ne a “Radio Band”, wato jimillar zangon dake dauke da dukkan shirye-shiryen gidajen rediyo, a ko ina suke a duniya.
Daga cikin zangunan nan guda hudu, zangon FM ne ke dabakar karshe, wato a sama. Shi yake dauke da takaitaccen tsarin maimaituwan sauti a lokacin karba ko aikawa. Amma zangon AM, shi ke can kasa, duk da fadi da girman kadadarsa. Kana bukatar doguwar eriya (Antenna) wajen kamo tashoshin dake zangon. Shi yasa kake ganin akwatunan rediyo ke zuwa da dogayen eriya a tare dasu. A wasu lokuta ma har sai ka kara da doguwar waya, musamman idan kaje wajen masu gyaran rediyo za ka ga haka. Don haka, muddin masu kera wayoyin salula suna son wayoyin su zo dauke da rediyo mai amfani a zangon AM, to, dole ne su Makala wa wayoyin doguwar eriya daga waje, wacce za ta taimaka wa wayar iya kamo tashoshin dake zangon AM. Hakan ba karamin kalubale bane a gare su, domin zai kara wa wayar nauyi, sannan ita kanta eriyar wata Karin dawainiyar kashe kudi idan za a kera da kuma Makala ta.

Dalili na biyu kuma, ko da ma sun zabi su sanya wa wayoyin salula eriya, to, babbar kalubale na biyu ita ce: sautin shirye-shiyen rediyo a zangon AM ba shi da inganci sosai, musamman idan ka hada da na zangon FM. Ba a ma hada su. Domin sautin a zangon AM bai fita sosai; dishi-dishi yake. Sannan idan wayarka na dauke da rediyo a zangon AM, idan ka tsaya kusa da kwamfuta ko wani inji, ko dirkar wayar lantarki (electric pole), ko talabijin, nan take sautin rediyon zai fara daukewa. Za ka rika jin wata kara tana maka katsaladan. Sannan idan ana ruwan sama aka fara walkiya ko cida, zai rika tasiri wajen sautin rediyon. Wannan ma na iya yi wa fasahar rediyon dake wayar illa idan ya ci gab ana tsawon lokaci.

Dalili na uku kuma na karshe shi ne, a zamanin yanzu, musamman a kasashen da suka ci gaba, kididdigar masu amfani da zangon AM yayi karanci sosai. Sannan hatta gidajen rediyo, yanzu galibinsu duk suna amfani ne da zangon FM wajen yada shirye-shiryensu. Sai kalubale na karshe ma, da yawa cikinsu sun koma yada labaru ko shirye-shirye ta hanyar yanar intanet, wato: “Online Radio” ko “Internet Radio”. Wannan yasa galibin kamfanonin kera wayoyin salula ke ganin zai zama hasara ne su dora wa wayar salula wata fasahar da aka daina yayinta, sannan tana ma dauke da matsala – amfaninta ga mai wayar salula ya gaza rashin fa’idarta nesa ba kusa ba. Don haka, da su kashe kudi wajen abin da bazai jawo musu riba ba, sai ma faduwa, gwamma su takaitu ga fasahar FM dake da ingancin sauti, da kuma karancin wahala wajen mu’amala.

Wadannan su ne dalilan da suka sa ko kadan ba ka jin labarin rediyo mai watsa shirye-shirye a zangon AM a kan wayoyin salula. Tabbas zai iya yiwuwa kaji ana sauraren tashoshi irin su Sashen Hausa Rediyo Najeriya Kaduna, da su BBC Hausa (wadanda a zangon AM da SW suke) a kan wayar salula irin ta yau. Kada ka rudu, akwai dayan dalilai biyu. Ko dai mai wayar ya saukar da manhajar gidan rediyon ne a kan wayarsa, yake amfani da ita wajen saurare. Wannan ke nufin lallar akwai tashar a kan Intanet kenan. Ba wai fasahar rediyon da wayarsa tazo da ita bace yake amfani da ita wajen saurare. Ko kuma mai saurare ya kamo tashar ne kai tsaye daga shafinsu na Intanet, yana saurare. Amma wayar salula dauke da fasahar rediyo a zangon AM ko SW ko MW, babu – saboda dalilan da suka gabata.

Wannan shi ne dan abin da zan iya cewa. Da fatan ka gamsu. Allah sa a dace, amin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.