Sakonnin Masu Karatu (2020) (17)

Tsarin Rediyon FM da AM a Wayar Salula (1)

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 6 ga watan Nuwamba, 2020.

84

Assalamu Alaikum Baban Sadik, muna godiya matuka da irin bayanan da muke samu daga gareka, Allah Ya kara basira. Tambayata a nan ita ce: kowace wayar salula tana da rediyo nau’in FM, amma ban taba ganin wayar salula mai dauke da rediyo nau’in AM ba. Shin, hakan bazai yiwu bane? Daga Abubakar Sa’idu Dankanjiba.

Wa alaikumus salam Babana. Barka da warhaka. Lallai wannan tambayar taka tambaya ce da ta cancanci a amsa ta. Domin duk da cewa na dade ina bincike kan hanyoyi da na’urorin sadarwa na zamani, amma sai daga baya na binciko dalilin rashin hakan, lokacin da galibin wayoyin salula na zamani suke ta zuwa da fasahar rediyo. A halin yanzu dai, in ka kebe nau’ukan wayoyin salula na kamfanin Apple, wato: iPhone da sauran danginta, zai yi wahala ka samu wata wayar salula da ba ta dauke da fasahar rediyo a tare da ita. Amma kamar yadda ka lura ne, rediyon wanda ke iya gudanuwa a zangon FM ne. To me yasa har yanzu babu wani kamfani da ya samar da rediyo mai gudanuwa a zangon SW, ko AM, ko MW? Abin sai kace hadin baki? To meye dalili?

Da farko dai, ba wani hadin baki bane tsakanin kamfanonin kera wayoyin salula, tunda ba a kasa daya suke ba dukansu. Na biyu, ita kanta fasahar rediyon da muke gani a wayoyin salula, ba wai lokaci daya kamfanonin sadarwar wayar salula suka yanke shawarar kirkira da dorawa a kan wayoyinsu don amfanin masu wayoyin ba. Wani abu ne da ya dauki lokaci mai tsawo. Asali dai kananan wayoyin salula ne a da suke zuwa da rediyo. Daga baya abin yazo kan manyan wayoyi, har a karshe dai ya game ko wace irin wayar salula.

Dalilin farko dai da yasa wayoyi ba su zuwa da fasahar rediyo a farkon lamari shi ne yaduwar akwatunan rediyo a duniya, da kuma wasu kayayyakin na’urorin sadarwa masu dauke da fasahar rediyo a Turai da Amurka, irin su na’urar iPod Nano, da iPod Touch duk na kamfanin Apple. Mutane da dama kanyi amfani dasu wajen sauraren wakoki. Daga baya sai wayar salula ta fara yaduwa, wanda hakan ya rage adadin akwatunan rediyo da ake kerawa a duniya. Wannan yasa mutane a kasar Amurka suka fara neman kamfanonin kera wayoyin salula, musamman Apple, su sanya fasahar rediyo a wayoyin da suke kerawa. Wannan ne dalilin da ya zaburar da kamfanonin waya wajen fara dora fasahar rediyo mai gudanuwa a zangon FM, a kan wayoyin salula. To amma me yasa sai FM?

Babban dalilin da yasa kamfanonin kera wayoyin salula suka zabi fasahar FM shi ne don saukin mu’amala. Shirye-shiryen gidajen rediyo na gudanuwa ne a zango daban-daban. Wadannan zanguna suna dauke ne a sararin samaniya. Kuma sautin shirye-shiryen na gudanuwa ne a yanayin haske, wanda na’urorin gudanarwar ke sarrafawa tsakanin cibiyar shirye-shirye da mahallin da mai rediyo ke iya samun wadannan shirye-shiryen a rediyonsa don sauraro. Su tasoshin FM suna gudanuwa ne a zango takaitacce, amma mai ingantaccen tsarin sauti. A wannan mahallin ko zangon, rugumutsin dake sararin samaniya bai cika yin tasiri wajen hana sakon sautin gudanuwa ba. Kuma a duk sadda aka cilla shirye-shirye, nan take ake iya samunsu.

- Adv -

Wannan yasa ko ana ruwa, za ka ji gidajen rediyon FM suna gudanuwa ba matsala. Haka ko da rediyon yana kusa da na’urar kwamfuta ce, ko wayoyi masu dauke da makamashin lantarki irin wadanda ke ratsa garuruwa ko unguwanni, wannan bai hana kaji shirye-shiryensu kai tsaye. Sannan a yayin da kake saurare, baza kaji sautin yana karuwa ko raguwa ba, a lokaci guda. Sannan baza kaji wasu tasoshi na shiga cikin tashar da kake saurare ba. Dukkan wannan ya faru ne sanadiyyar yanayin dabi’ar kadadar sadarwar da zangon FM. Wannan yasa ko doguwar eriya (antenna) ba ka bukata wajen kama tashar FM.

Zangon FM a Wayar Salula

Sadda aka bukaci kamfanonin kera wayar salula su dora fasahar rediyo a wayoyinsu, masana suka ce ba wani abu ake bukata ba illa “motsar” da bangaren da zai iya baiwa wayar salula daman kamo tashoshin rediyo cikin sauki. Wannan ya faru ne saboda da wayar salula da fasahar rediyo, duk a zangon haske daya suke gudanuwa. Ma’ana suna amfani ne da sauti ta hanyar haske, don aiwatar da sadarwa. Wannan nau’in haske kuwa shi ake kira: “Radio Wave”. Kuma dukkan na’urorin da akwatin rediyo ke bukata wajen gano tasha, da kamo sauti, da sarrafa sauti da kuma jiyar da mai rediyo wannan sautin, duk ita ma wayar salula tana dauke dasu. Shahararru daga cikin wadannan na’urori dai su ne: Na’urar “Tuned Circuit”, da “Antenna”, da kuma “Receiver”. Ga takaitaccen bayani nan kan kowanne.
Na’urar “Tuned Circuit” dai ita ce wacce ke kamo tasha sannan ta killace tashar da mai akwatin rediyo ke sauraro. Wannan ke hana shigar wata tashar cikin wacce ake sauraro; iya gwargwadon karfi da ingancin na’urar rediyon mai sauraro. A jikin allon na’urar wayar salula (Circuit Board) akwai wannan na’ura. Da zarar an motsa ta shikenan, an samu wata siffar rediyo dauke a wayar salula.

Ita kuma na’urar “Antenna” ta ce na’urar dake karban makamashin sauti ko murya daga na’urar “Transmitter”, ta mayar dashi zuwa siginar rediyo (Radio Signal), don cilla wa na’urar “Receiver” dake akwatin rediyo. Wannan nau’i biyu ce. Akwai wacce ke gine cikin wayoyin salula, da wadanda ke girke a jikin akwatunan rediyo. Sannan ayyukanta uku ne. Na farko shi ne karba tare da sarrafa makamashin sauti zuwa siginar rediyo, don tafiyar dashi a sararin samaniya. Na biyu shi ne daidaita yanayin sauti wajen karbansa ga mai sauraro ta hanyar akwatin rediyonsa. Wannan shi ne asalin aikinta, a al’adance. Aikinta na uku shi ne warware sautin da ta cafko daga tashar sararin samaniya wanda ke yanayin siginar rediyo, zuwa yanayin da mai sauraro zai iya ji ya amfana dashi. Wannan na’ura ta “Antenna” dake girke a wayar salula na iya sinsino, tare da dauko sakonnin shirye-shirye daga zangon FM zuwa kan wayar salular, don bai wa mai wayar damar saurare. A takaice dai, ba a bukatar wata doguwar wayar “Antenna” daga waje don mu’amala da wadannan tashoshi dake wannan zangon FM.

Sai na’urar “Receiver”. Wannan ita ce na’urar da ke karbar warwararren siginan rediyo daga na’urar “Antenna” kamar yadda bayani ya gabata a sama, don jiyar da mai akwatin rediyo hakikanin sauti ko muryar mai gabatar da shirye-shiryen da yake sauraro. Wannan na’ura tana da mahimmanci matuka ga akwatin rediyo ko wayar salula. Domin idan ta lalace, to babu abin da za a iya sauraro daga gare ta.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.