Fasahar 5G: Gabatarwa

Bayani Kan Abin da Makalar ta Kunsa Gaba Daya

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 8 ga watan Mayu, 2020.

223

Gabatarwa

Cikin makonni takwas da suka gabata mun ci gaba da amsa tambayoyin masu karatu ne, don samun daman karin haske da gamsuwa.  Tambaya ta karshe da ta rage mana, tsakanin watan Maris da Afrailu da suka gabata, ita ce wacce Malam Aminu Sa’id dake garin Kondiko na Jihar Jigawa, ya aiko.  Tambaya ce mai tsawo, domin ta yi rabin shafi guda.  A takaice, yana so ne yasan ma’ana da asalin sabuwar fasahar sadarwar zamani da za a ci gaba da amfani da ita a marhalar sadarwar zamani na biyar, wato: “5G”.  Meye alakar wannan sabuwar fasaha da kamfanin Google, in akwai?  Sannan ko wannan sabuwar fasaha ce za ta maye gurbin fasahar marhala ta hudu mai suna: “4G – LTE”? Cikin abin da yake son sani har wa yau, shin, wai yaushe ne kasarmu Najeriya za ta fara cin gajiyar wannan sabuwar fasaha?  Sannan, ko ya dace aci gaba da kirkirar sababbin fasaha a fannin sadarwa masu saurin isar da sako mai yawa cikin kankanin lokaci, bayan ga “data” na tsada a Najeriya?  Kuma wai shin ma dai, tsakanin hukumar sadarwar wayar salula ta kasa (National Communication Commission – NCC) da kamfanin sadarwar wayar salula (irin su MTN, da Airtel, da Glo, da 9Mobile), waye da laifi wajen tsadar “data” a Najeriya?

Wadannan tambayoyi ne masu yawa, kamar yadda mai karatu ya gani.  Sannan Malamin ya yi su ne a kan gaba; daman ina jiran gama amsa tambayoyin masu karatu ne don kutsawa cikin wannan fanni.  Bayan haka, wannan fasaha na daga cikin abin da ake ta jita-jitar cewa kasar Sin ta yi amfani da ita ne wajen yada wannan cuta ta Coronavirus, ko COVID-19.  A takaice dai, akwai jita-jita da dama a kanta.  Da wannan naga dacewar gudanar da bincike tare da samar da rubutu mai tsayi, kamar yadda na saba a baya, don gamsar da masu karatu kishirwan da suke fama da shi.  Amma kafin nan, zai dace mai tambaya yasan cewa babu alaka tsakanin tsadar kudin “Data” a Najeriya da samuwar sabuwar fasahar sadarwa ta 5G.  Sannan, bayani kan wa ke da laifi tsakanin hukumar NCC da kamfanonin sadarwa wajen tsadan “Data” a Najeriya, sai ince da farko dai tukun, shin, yaushe ne “Data” ya kara kudi ne a Najeriya?

A iya sani na, a kusan galibin lokuta cikin rage kudin “data” ake a Najeriya.  Bayan rage kudadensu, hukumar NCC bata gushe ba tana azalzalar kamfanonin sadarwar wayar salula da su samar da yanayi mai sauki da inganci na sadarwa ga ‘yan Najeriya.  A yanzu haka akwai hanyoyin amfanuwa da “Data” da yawa; an nau’anta su.  Akwai na hawa kowane irin shafin Intanet kake so, tsakanin wanda za ka saya na yini guda, da na mako guda, da wanda za ka amfana dashi cikin dare kadai, da wanda za ka iya amfani dashi cikin wata guda, da na watanni biyu, da dai sauransu.  Sannan akwai nau’in “Data” da za ka saya don amfani da manhajar wayar salula da shafukan sada zumunta kadai.  Misali, akwai na hawa WhatsApp, da Facebook da dai sauran makamantansu.

- Adv -

Dangane da batun rashin ingancin “Data” a wayoyin salula kuma, ina kyautata zaton Malamin na nufin idan ka sayi data, bayan dan kankanin lokaci ne sai ya kare, watakila ba tare da ka yi amfani da wasu abubuwa dake jan data ba, a al’adance.  Dangane da wannan korafi, akwai mahanga biyu.  Na farko, tabbas ana samun lokutan da za ka sayi data amma nan take, watakila ma ko amfani dashi baka yi ba, sai kawai kaga babu.  Hakan na faruwa ne sanadiyyar matsalolin na’urorin kamfanin wayar salula.  Kuma muddin ka fahimci haka, to, hanya mafi sauki ita ce ka kira kamfanin wayar salula – ko ba ka jin turanci akwai wadanda za su yi magana dakai cikin harshen Hausa – ka sanar dasu abin da ya faru.  Idan suka duba zasu ga abin da ya cinye maka data.  Kuma muddin daga gare su ne, to, nan take zasu dawo maka dashi kuma su baka hakuri.  Kamar yadda ko kudi ne kasa, sai kawai aka kwashe ba tare da kayi amfani dashi, idan ka musu korafi zasu mayar maka.  Domin suna iya ganin ta wace hanya aka yi amfani da kudin ko datan.  Tangarda ce ta na’ura.  Na san da yawa cikin wadanda suka kira suka yi korafi, kuma aka mayar musu da abinsu.  Hakkinka ne.

Mahanga ta biyu kuma ita ce, zai yiwu kai ne ka cinye abinka ba tare da ka sani ba.  Wadannan wayoyi na salula suna dauke ne da manhajoji da muke amfani dasu, wato: “Applications” kenan.  Wadannan manhajoji kuma galibi mun saukar dasu ne daga cibiyar manhajoji ta Google mai suna: “Play Store”, idan wayar salula nau’in Android ce.  Wannan ke sa a lokaci-lokaci wadannan manhajoji suna musayar bayanai da asalin shafin kamfanin da ya kirkire su, don samun bayanan karin samun tagomashi.  Wannan sadarwa kuwa suna yi ne galibi ta karkashin kasa.  Bayan haka, asalin babbar manhajar Android ita kanta dake dore kan wayarka, tana musayar bayanai da kamfanin Google, asalin kamfanin da ya samar da babbar manhajar kenan, don samun bayanan karin tagomashi.

Har wa yau, akwai manhajoji ko masarrafan Google dake dore kan kowace wayar salula nau’in Android, irin su: “Google Map” da “Gmail” da “Chrome” da “Youtube” da sauran makamantansu.  Wadannan manhajoji ba a sandare suke ba; duk sadda ka sanya data a wayarka, ka kuma bude data, nan take suna musayar bayanai da kamfanin Google don samun bayanan karin tagomashi.  Bayan haka, idan kana dauke da manhajar Imel irin su “Gmail” ko “Outlook” ko “Yahoo”, to, ka san cewa an kera su ne su rika aiwatar da sadarwa tsakanin wayarka da kamfanin da ke adana maka sakonninka na Imel.  Da zarar ka kunna data, nan take wannan manhaja za ta jonu da taskar sakonni don debo sababbin sakonni in akwai.  Wannan duk hanyoyi ne da wayar salula ke bi wajen jan data dinka ba tare da ka bata wani umarni ba.  Idan mutum bai fahimci haka ba, zai dauka zaluntarsa ake.  Da fatan za a kiyaye.

Kamar yadda na ayyana a sama, daga mako mai zuwa za mu fara bayani kan sabuwar fasahar 5G: za mu ji ma’ana da asalinta, da fa’idojin da take dauke dasu, da yadda aka yi ta sha bamban da sauran wadanda suka gabace ta, da kuma illolin da ake ganin tana dauke dasu.  A karshe, za mu tattauna kan mafi shaharan jita-jitan da suka yadu dangane da wannan sabuwar fasaha.

Aci gaba da kasancewa tare da mu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.