Fasahar 5G: Illolin Da Ake Hasashensu Daga Siginar 5G (1)

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 20 ga watan Nuwamba, 2020.

292

Bayan tsawon makonni ko ince watanni da muka kwashe muna amsa tambayoyi da tsokacin masu karatu, a wannan mako dai za mu ci gaba da darasinmu kan fasahar 5G, kamar yadda muka yi alkawari a makon jiya.  Daga wannan mako za mu fara bayani kan illolin da ake hasashen wannan fasaha na dauke dasu.  Sannan a makonnin da ke tafe mu dubi jita-jita da karerayin da ake ta yadawa kan wannan fasaha.  A ci gaba da kasancewa tare damu.

——————–

Illolin Da Ake Hasashe Daga Fasahar 5G

Bayan bayanai kan fa’ida da ingancin da wannan tsari na 5G ke tattare dashi, da yadda samuwansa zai yi tasiri wajen inganta rayuwar al’umma a kimiyyance, da siyasance da kuma fannin tattalin arzikin kasa, zai dace har wa yau mai karatu ya fahimci abubuwan da ake hasashen illoli ne, wadanda wannan fasaha ke dauke dasu.  Na yi amfani da Kalmar hasashe ne, domin har yanzu babu tabbaci kan wadannan illoli, saboda dalilai biyu.  Na farko shi ne, wasunsu ba za su ma faru ba.  Dalili na biyu kuma shi ne, tunda har yanzu wannan fasaha bata habaka ba, bata game duniya ba, ba a iya tantance hakikanin abubuwan da ake hasashe na illa a yanzu, sai nan gaba.

Kafin muyi nisa, zai dace mai karatu ya fahimci cewa, duk wani abu na mu’amala, in dai ba abin da shari’ah ta wajabta ayi mu’amala dashi bane, to, dole ne ka same shi da wani nau’i na cutarwa, bayan amfani.  Wannan ka’ida ce ta rayuwa.  Kuma hakan bai kebance fasahar 5G ba.  Fasaha ce da dan adam ya kirkira, don amfani.  Abin da ake la’akari dashi shi ne: tsakanin amfani da cutarwa, in ma akwai, wanne ne yafi rinjaye?  Bangaren da yafi rinjaye dashi za ayi la’akari wajen hukunci.  Don haka sai mu fadaka. Mu fahimci cewa, don ance wata fasaha na da amfani, wannan bai hana a samu wani nau’i na rashin fa’ida dangane dashi. In kuwa haka ne, sai mu fahimci don an ce fasahar 5G tana da wasu illoli da ake hasashe, ba wani abin mamaki bane.  A tare da cewa jita-jita da karerayi sun yadu sosai kan wannan fasaha, tun kafin a fara amfani da ita.  A mako mai zuwa in Allah Ya so za mu fara bayani kan wadannan zantuka na karya da jita-jita da ake ta yadawa, wanda suka samo asali daga kasashen da suka ci gaba; inda asalin fasahar ta samo asali.

Rage Karfin Na’urorin Hasashen Yanayi

- Adv -

Abu na farko da aka fara ganowa sadda ake gwajin fasahar 5G a kasashen turai da Amurka shi ne, karfin sinadaran maganadisun lantarki (Electromagnetic frequency) da fasahar 5G ke dauke dashi zai iya tasiri wajen rage karfi da karsashin hasken maganadisun na’urar hasashen yanayi.  Su na’urorin hasashen yanayi dai na’urori ne da ake amfani dasu wajen gano yanayin sanyi ko zafi, ko saukan ruwan sama ko janyewarsa, ko ambaliyar ruwa ko girgizar kasa a tudu ko teku (Tsunami).  Har wa yau akwai na’urorin da ake amfani dasu wajen lura da yanayin karkashin kasa.  Wadannan na’urorin dukansu suna dogaro ne da tauraron dan adam dake aikin gano sauyawan yanayi a lokuta daban-daban.  Masu lura da sauyawan yanayi ana kiransu: “Weather Observation Satellites”, su kuma masu lura da yanayin karkashin kasa ana kiransu: “Earth Observation Satellites”.

Gwajin da aka yi dai ya nuna cewa, kusancin dake tsakanin sinadaran maganadisun fasahar 5G na iya katsalandan ga sinadaran maganadisun wadancan na’urori na binciken karkashin kasa ko yanayin gudanurar yanayin duniya.  Wannan katsalandan zai iya tasiri wajen rage kaifin wadannan na’urorin tauraron dan adam da kashi 30 cikin 100.  Hakan kuwa, a cewar masana, na iya tasiri wajen karancin ingancin bayanan da za a samu masu alaka da halin da yanayin da duniya ke ciki, musamman wajen dumamar yanayi (Global Warming).  Don haka, wannan na nuna dole kasashen duniya su yi wani abu kenan.

Sai dai wannan ba wata matsala bace mai girma ko wacce za ta yi tasiri wajen illata duniya ko jama’a.  Domin tuni kasashen Amurka da Nahiyar turai suka fara rage karfin wannan maganadisun fasahar 5G, don kauce wa wancan illa da aka yi hasashensa lokacin gwajin fasahar.  A taron ci gaban kimiyyar sadarwar wayar salula na duniya (World Radiocommunication Conference) da aka gudanar a shekarar 2019, kasashe daban-daban sun ba da tabbacin rage karfin yanayin sadarwar fasahar 5G dake kasashensu, da kimar haske daban-daban.  Don haka, wannan matsala an riga an shawo kanta tuni.

Matsalar Leken Asiri Tsakanin Kasashe

Daga cikin abubuwan da suka jawo hankalin masana kan harkar tsaro a fagen fannin sadarwa na zamani akwai irin tasirin da ake sa ran fasahar 5G za ta yi wajen kara tarin bayanai da yawaitar na’urori da hanyoyin sadarwa.  Wannan wata dama ce da wasu bata gari ka iya amfani da ita wajen aiwatar da kutse cikin na’urorin sadarwar da suka shafi rayuwar mutane – musamman a asibitoci, da wuraren shakatawa da makarantu da hukumomin tsaro.  Bayan wannan, zaman doya da manja da ake yi tsakanin kasar Sin (China) da kasar Amurka da wasu cikin kasashen nahiyar Turai (irin su Burtaniya da sauransu), ya kara jawo damuwa musamman a kasashen Amurka da Turai kan cewa kasar Sin da wasu daga cikin kamfanonin wayar salula dake kasar, musamman kamfanin Huawei (daya daga cikin kamfanonin dake kera na’urorin sadarwa na fasahar 5G), suna iya amfani da wannan dama wajen aiwatar da leken asiri kan kasashe da kamfanonin duniya.

Wannan hasashe ne, duk da cewa kasar Amurka ta yanke alaka da kamfanin Huawei, inda ta haramta wa kamfanonin kera na’urorin sadarwar kasar mu’amalar kasuwanci da kamfanin.  Kasar Burtaniya ma ta yanke alakar kasuwanci tsakaninta da kamfanin Huawei, duk a kan wancan hasashe na cewa kamfanin na iya tatsar bayanan masu amfani da wannan fasaha don bai wa hukumar kasar Sin.  Wannan zargi tuni kasar Sin da ma kamfanin Huawei suka karyata.  Amma duk da haka bai canza komai ba.  Don haka, ma iya cewa har yanzu shi ma wannan illa hasashe ne ake yi, na yiwuwar samuwarta nan gaba, ta la’akari da irin yanayi da dabi’ar tsarin sadarwa na zamani.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.