Sakonnin Masu Karatu (2020) (16)

Tasirin Hayakin Sadarwar Wayar Salula ga Lafiya

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 30 ga watan Oktoba, 2020.

115

Assalamu alaikum Baban Sadik, da fatan Sadik yana lafiya. Ina son in da hali ka bani shawara. Ina son shiga makarantar koyon kwamfuta ta mussamman don sanin abin da ya shafi kudi da ake kira Bitcoin ko Digital Currency ko Cryptocurrency. Da kuma Blockchain. Wani irin kwas zan zaba don in san su sosai? Ga email na. miyolaexpress@gmail.com. Ni ne Abdullah Aliyu, daga Abuja. Na gode.

Wa alaikumus salam, barka dai takwarana. A gaskiya ban san wata makaranta ta kwamfuta da za kaje a koya maka wannan nau’in ilimi ba. Domin abubuwa ne guda biyu ke kunshe a ciki. Abu na farko shi ne asalin sana’ar, wanda ya shafi saye ne sayarwa a Intanet. Ana gudanar dashi ne ta hanyar manhajojin gidajen yanar sadarwa da ake amfani da su a Intanet, wato: “Web Applications”! Abu na biyu kuma shi ne, ilimin kwamfuta kafin a iya gudanar da wadannan ayyuka. Makarantun kwamfuta na karantar da ilimin kwamfuta ne kadai. Idan ka iya sarrafa ta, sannan ka iya gudanar da abubuwa a kan Intanet.

Shawarata ita ce, ka samu makarantar kwamfuta don koyon yadda ake amfani da ita. Sannan ta bangaren ilimin wadannan nau’ukan kasuwanci na hada-hadar kudi na zamani a Intanet, shi kuma sai an koyar dakai. Ban san wata makaranta ta musamman dake yin haka ba, gaskiya. Sai dai watakila cibiyoyi ko kamfanonin hada-hadar kudi na Intanet. Su kuma ban ce muna da irinsu a nan Arewacin Najeriya ba. Galibi sun fi yaduwa a Legas. Kuma karantarwar kan zama a zahirin mahalli ne ba wai ta Intanet ba. Ta wannan bangare, muddin ka samu inda za ka koyi yadda ake mu’amala da kwamfuta, to, ina kyautata zaton ba za su rasa sanin inda za ka samu masu wancan kwarewa ba. Amma kafin nan, na san watakila kana samun labarai ne kan yadda wannan nau’in kasuwanci ke da riba sosai, jama’a kan samu kudade da yawa cikin kankanin lokaci. Amma zai dace ka san cewa kasuwanci ne mai matukar hadari, musamman ga wanda bai kware a kai ba. Kamar kasuwancin takardun kudaden kasashen waje ne da ake yi ta Intanet, wato: “Forex Trading”, akwai matukar hadari sosai. Shi yasa ma, dukkan hukumomin hada-hadar kudi dake Najeriya (irin su CBN, da SEC, da NDIC dsr) suka nisanta kansu da wadannan nau’ukan kasuwanci; domin ba su da dokokin dake baiwa masu zuba jari a wannan fanni kariya. Idan aka cuceka wajen ire-iren wadannan kasuwanci na Intanet, Babban Bankin Najeriya (Central Bank of Nigeria – CBN) ba zai kwato maka kudadenka ba. Domin babu wata doka da tace ga yadda tsarin kasuwancin zai kasance, balle ace idan aka yi ba daidai ba, ga hukunci.

Wannan shi ne dan ta’alikin da zan yi. Da fatan ka gamsu. Allah sa a dace, amin.

Assalamu alaikum Baban Sadik, barka da warhaka. Muna godiya da wayar mana da kai da kake yi a fannin kimiyar sadarwa. Don Allah ta yaya masu gyaran waya za su kare kansu daga gubar hayakin da wayar salula take fitarawa a lokacin da suke gyara? Daga Umar A. Umar Mazoji, Matazu Local Govt, Katsina.

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Umar. Da farko dai tukun, zai dace ka san cewa har yanzu babu wani bincike tabbatacce da hujjoji ingantattu da ke nuna cewa hayakin maganadisun lantarki dake fita daga jikin wayar salula na kawo cutar kansa (wato Sankara, ko Daji), kamar yadda ake ta jita-jita tsawon shekaru. A shekarun baya an mini tambaya kan haka kuma na gudanar da bincike inda na gabatar da hujjoji daga hukumomin kiwon lafiya na duniya dake kasashen Ingila da Amurka da sauran kasashen Turai, da ma hukumar kiwon lafiya ta duniya, wato: “World Health Organization” (WHO); duk babu bayani dake tabbatar da hakan. Wannan kenan.

Sannan shi kanshi wannan hayaki da ake magana fa, sai idan an kunna waya ana Magana ne sannan yake fita daga jikin wayar. Ba abu bane da gudanuwa daga jikin wayar a kowane lokaci ba. In kuwa haka ne, kenan ba wani bambanci tsakanin mai gyaran waya da wanda ke amfani da wayar. Don haka, shawarata ga masu gyaran wayar salula shi ne su dauki matakan kariya daga hadarin wutar lantarki da suke amfani da shi wajen yin waldan wayoyi, da wanda suke lika na’urar “IC” dashi. Sannan ya zama suna amfani da safar hannu don kariya daga dattin waya; domin baka san ina da ina aka kutsa da ita ba kafin kawo maka gyara. Bayan haka, idan akwai matattun wayoyin salula da aka daina amfani dasu, ko matattun batir, ko matattun gilashin waya da ake canzawa, duk bai kamata a rika zubar dasu a bolar da ake zubar da sauran shara ba. Kuskure ne wannan. Domin wadannan na’ukan karikitai suna dauke ne da sinadaran kimiyya kala-kala masu hadari ga rayuwa. Shi yasa a kasashen da aka ci gaba a fannin kimiyya da tattalin arziki, akwai hukuma ta musamman da ta tanadi wurare na musamman inda ake zubar da wadannan na’urori. Kuma ita ce ke kwashe su don yin abin da ya dace dasu.

- Adv -

Wannan shi ne dan abin da zan iya cewa. Ina maka fatan alheri. Allah sa a dace, amin. Na gode.

Assalamu alaikum Baban Sadik, na karanta bayaninka kan fasahar Artificial Intelligence (AI) wanda aka buga a cikin jaridan Aminiya, na kuma karu sosai. Baban Sadik Allah Ya kara ilimi. Na gode. Auwal Sulaiman daga Jihar Bauchi.

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Auwal. Hakika ina farin ciki da jin ka fa’idantu da abin da ka karanta. Daman manufar samar da shafin kenan don a ilmantar kuma a wayar da kan al’umma musamman kan fannonin ilimin da muke da karancin sani da fahimta a kansu. Allah mu dace baki daya, amin. Na gode.

Assalamu alaikum Baban Sadik, muna matukar godiya da wayar da kan jama’a da kake yi kan ilimin kwamfuta. Tambayata ita ce: kamfanin facebook na iya biyan masu amfani da shi ko shafinsa ne? In eh, sai ka samu adadin mabiya nawa ne kafin su fara biyanka? Daga Pada, Ibadan: 08032966986

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Padah. Shi kamfanin Facebook kamfani ne dake karban tallace-tallacen kamfanonin kasuwanci yana dorawa a shafinsa, don masu mu’amala da shafin su rika gani suna latsawa, shi kuma a biya shi ladan aikinsa. Idan ka lura, duk sadda ka hau shafinka, a daidai inda labaru ke bayyana (News Feed), za ka ga wasu bayanai na wasu kamfanoni da ba ka da alaka dasu; baka ma sansu ba. Idan ka lura sosai, daga saman hoton ko bidiyon za ka ga an rubuta: “Ad” ko kuma “Sponsored page” ko wani abu makamancin hakan. Idan ka matsa wadannan sakonni, wanda galibinsu hotuna ne ko bidiyo na wasu ‘yan dakiku, za a zarce da kai ne kai tsaye zuwa shafin kamfanin da ya bayar da tallan.

Amma kai da kake amfani da shafin Facebook, babu wani talla da kamfanin Facebook zai baka. Domin kai kanka, hajar kamfanin Facebook ne (yi hakuri ba aibantaka nake yi ba). Abin da nake nufi shi ne, kai kanka da ka bude shafi a dandalin Facebook, duk da cewa kana ganin kyauta ne, kamfanin Facebook ya fi ka riba. Ba ma haka ba, kai ne ke taimaka masa wajen samar da kudaden shiga. Don haka, kamfanin Facebook ba ya baiwa mutane talla, sai dai ma ya tallata musu hajar wasu kamfanonin.

Sannan akwai wasu dake amfani da mutane su sa ka bude shafi (Facebook Page) sannan sub aka wasu sakonni da zaka rika dorawa a duk Safiya, ko wani adadi na awanni, ta yadda duk mako ko karshen wata zasu baka kudi. Wannan ba kamfanin Facebook bane. Sannan abin da suke yi ma ya saba ma ka’idojin kamfanin. Da ace mutane ne ke lura da shafukan Facebook kai tsaye a madadin kamfanin, ba manhajoji ba, da ba wanda ya isa yayi irin wannan kasuwancin. A tare da cewa ma akwai cuwa-cuwa cikin yadda aiwatar dashi, hatta a shari’ance. Idan kaji wani yace maka an bashi talla a Facebook, to, ka sani ba kamfanin Facebook bane, watakila irin wannan nau’in kasuwancin ne me hadari.

Wannan shi ne jan hankali da karin bayanin da zan yi kan tambayarka. Da fatan ka gamsu. Allah sa a dace, amin. Na gode.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.