Tashoshin Sashen Hausa na DW Radio da BBC ta Tauraron NileSat

Kasidarmu ta yau dai fadakarwa ce kan samuwar tashoshin tauraron dan adam na gidan rediyon BBC Hasau da DW. A sha karatu lafiya.

792

Ga masu sha’awar sauraron tashoshin BBC Hausa da Muryar Jamus na rediyo, wato Deustwelle Hausa ko DW Hausa, yanzu nesa ta zo kusa.  Cikin shekarar da ta gabata ne wadannan tashoshi suka hau tauraron adan adam mai suna NileSat, inda duk mai kallon tashoshin tauraron dan adam ta wannan tauraro na NileSat zai iya kamo su, ya kuma saurari shirye-shiryensu cikin lokutan da suke yadawa, garau radau, ba tare da wata matsala ba.

Idan kana da tauraron adan adam na NileSat wanda kake kallo kyauta ba tare da ka biya ko ahu ba, kana iya samun tashar shashen Hausa na BBC a TP 11.843, a bigiren Horizontal, wacce ke dauke a Symbol Rate (SR): 27.500. Da zarar ka shigar da wadannan kalmomin nema, za ka samo tashar ba tare da bata lokaci ba.  Bayan haka, muddin kana iya kama sashen BBC World na harshen turanci a bangaren talabijin, to, kana da wannan tasha ta Hausa.  Idan kana son ganewa, sai ka je bangaren tashoshin rediyo – ka matsa maballar da aka rubuta TV/Radio a jikin rimot dinka, za a zarce da kai tashoshin rediyo nan take.  Sai ka budo tashoshin, ka nemi wannan tasha.  Sunan tashar dai shi ne BBC Hausa Radio. 

- Adv -

Ga wadanda ke amfani da karamar dish ta NileSat mai girman 1.8, samun wannan tasha zai musu wahala idan a birnin Abuja suke, sai sun sanya babbar dish mai girman 2.4. Amma idan a Arewacin Najeriya suke, za su samu.  Saboda an fi samun yanayi mai kyau a can.

Ga masu neman tashar DW Hausa Radio kuma, sai su neme te a TP 11.900, a bigiren Vertical, a Symbol Rate (SR): 27.500, kuma sunan tashar shi ne DW2. Da zarar an shigar da bayanan nema za a samu.  Kuma idan ma kana iya kama tashar DW ta Turanci ko DW Arabic, to, ina kyautata zaton za a samu wannan tasha, ba sai an bincika ba.  Bayan haka, duk wanda ya dubi tashoshinsa na rediyo bai samu ba, to, yana iya kiran masu sanya tauraron dan adam su binciko masa, in har ba zai iya bincikowa da kansa ba.

A tashoshin tauraron dan adam na Multichoice kuwa, wato DSTV, wannan tasha ta BBC Hausa na nan tun fil azal.  Idan kana amfani da DSTV amma baka taba sanin wannan ba, ka je bangaren tashoshin rediyo daga rimot dinka (ka matsa “Shift”, ka rike, da zarar koren haske ya bayyana, sai ka saki ka matsa maballin “TV” nan take).  Sai ka nemi tasha mai suna BBC 2, ko BBC 3, za ka saurari shirye-shiryensu.  Idan ma tashar sashen turanci kake so, ita ce BBC 1.  Allah sa a dace.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.