Sakonnin Masu Karatu (2020) (14)

Yadda Adireshin IP (IP Address) Yake Aiki

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 16 ga watan Oktoba, 2020.

347

Salaamun alaikum Baban Sadik, da fatan kana lafiya. A gaskiya muna jin dadin wannan dandali naka. Allah Ya karo basira, amin summa amin. Tambayata ta farko ita ce: yaya ake taskance hotuna da sauran bayanai a Gmail?  Tambaya ta biyu ita ce: shin, zan iya shiga akwatin Gmail dina ta hanyar Opera? Sannan ina bukatar shawara game da karatu  (burina in zama kwararren Software Engineer) ina son a taimaka mini da hanyoyin da zan bi domin in samu kaiwa ga matakin nasara.  Ko akwai wasu littafai da zan nema, domin yanzu nake aji shida a matakin Sakandare. Na gode. Daga Ibrahim Bishir S/Gini Malumfashi.

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Ibrahim.  Tambayarka ta kan yadda ake taskance bayanai da hotuna a Gmail.  Da farko dai yana da kyau ka san cewa Gmail manhaja ce da aka tanadeta don kirkira da aikawa da kuma karban sakonnin Imel.  Wannan ita ce manufar samar da Gmail, da ma dukkan manhajojin Imel na Intanet, irin su Yahoo!, da Hotmail da sauran makamantansu.  Idan kuwa kana bukatar ajiye ko adana wasu bayanai, sai dai ka rubuta su ta hanyar da ake kirkiran sakonni, wato: “Compose” kenan, sannan ka aiko wa kanka, ta hanyar sanya adireshin Imel dinka.  Da zarar sakon ya shigo, sai ka adana shi ta hanyar sa masa wata alama.  Wannan zai sa a duk sadda ka tashi bukata, sai ka bude.  Ko kuma idan ka gama rubuta sakon, maimakon ka aika wa kanka, kana iya matsa alamar : “Save as Draft”.  Wannan zai sa a adana maka shi, zallansa kamar yadda ka rubuta.  Idan kana nemansa sai kaje jakar “Draft”, can za ka ganshi.  Idan hoto ne kuma, kana bukatar Makala shi a jikin sakon ne, wato: “Attachment” kenan.  Yadda abin yake kuwa shi ne, da zarar ka budo allon rubuta sakon (Compose), a kasa za ka ga wasu alamomin rubutu da sarrafa sakonni.  Kana iya shafa dan yatsanka a kan konne, don sunayensu ya bayyana.  Idan kaga “Attach”, sai ka matsa.  Za a tambayeka inda kake son dauko hotunan a jikin wayarka, sai kaje ka dauko hotunan.  Nan take za a Makala su a jikin sakon.  Daga nan sai ka bi matakan da na zayyana a sama, don adanawa.

Sai dai kuma, a ganina ba ka bukatar amfani da Gmail wajen adana bayananka, musamman hotuna.  In dai kana amfani da waya ce mai dauke da babbar manhajar Android, ina sa ran kana da manhajojin Google tinjin a wayar; wadanda tazo dasu.  Idan ka budo jakar Google, za ka gansu.  Ciki har da manhajar “Google Drive”, da manhajar “Photos”.  Dukkan wadannan kana iya amfani dasu wajen adana sakonni da hotunanka cikin sauki.  Manhajar “Drive” ma’adana ce ta tafi-da-gidanka, wato: “Cloud Storage”, wacce za ka iya adana bayananka kai tsaye, kuma ka same su sadda kake so.  Ita kuma manhajar “Photo” daman manhaja ce ta kirkira da taskance hotuna na kamfanin Google. Ita kai tsaye ma take aiki.  Ma’ana, muddin kana da ita a kan wayarka, duk hotunan da ka dauka da wayarka, nan take take taskance maka su a ma’adanar tafi-da-gidanka na Google.  Don haka, ba ka bukatar amfani da Gmail wajen yin hakan.

Tambayarka ta biyu kuma kan yadda za ka iya amfani da manhajar Gmail da Opera, sai in ga ba ka bukatar hakan.  Hanya mafi sauki ita ce ka saukar da manhajar Gmail daga Play Store kawai, sai ka shigar da suna da kuma Kalmar sirrinka kawai, kai tsaye za ka rika samun sakonni ko aika su.  Ya ma fi sauki.

- Adv -

Tambayarka ta uku kuma kan batun “IP Address” ne, da yadda yake aiki ko tsarin gudanuwarsa.  Da farko dai, Kalmar “IP” na nufin “Internet Protocol” ne, wanda a dunkule nake kira da suna: “Ka’idojin dake taimaka wa kwamfuta aiwatar da sadarwa tsakaninta da wata kwamfuta ko na’urar sadarwa.”  Asalin IP dai wasu lambobi ne da kowace kwamfuta ko na’urar sadarwa ke dasu, wadanda ke bambanceta da sauran kwamfutoci.  Kamar dai lambar waya ce, wanda kowannenmu ke dashi.  Babu lambobi biyu iri daya; haka babu kwamfutoci biyu masu dauke da IP iri daya.  Aikin wadannan lambobi ga kwamfuta dai guda biyu ne.

Abu na farko shi ne samar da kafar da wata kwamfuta za ta iya ‘magana’ ko aiwatar da sadarwa da ita.  Misali, a duk sadda ka dauki wayarka ta salula ko wata kwamfuta, ka kunna siginar Intanet, ka budo shafin Facebook ko Instagram, ko kuma rariyar lilo, wato “Browser” don hawa Intanet da neman bayanai, wannan wayar taka kan aika da sakon neman sadarwa ne ga kwamfutar dake dauke da adireshin da ka shigar, ko yake dauke kan manhajar da kake amfani da ita, idan manhajar Facebook ce ko Instagarm, misali.  Da zarar wayarka da “kwankwasa” kofar kwamfutar dake dauke da shafin da kake nema, sai kwamfutar ta amsa mata, sai ita kuma tace gabatar da bukatarta.  Da zarar kwamfutar da ake neman bayanai daga gareta ta fahimci sakon bukatar da ake mata, sai ta tunkudo shafi ko bayanin da ake nema daga gareta nan take.  Bayan wayarka ta karbi sakon, sai ta rufe titin sadarwar.  Ita ma kwamfutar sai ta rufe nata kofar.  Wannan tsarin karba da aikawa da sako shi ake kira “The Two-way Handshake”, a ilimin kimiyyar sadarwa na zamani.

Abu na biyu kuma shi ne, wadannan lambobi na IP dais una taimakawa wajen gano inda kwamfutar dake dauke dasu take ne.  Misali, kamfanin Google na da kwamfutoci sama da 500,000 masu dauke da bayanan da shafin ke tarawa da adanawa don bukatar masu hulda dashi.  Wadannan kwamfutoci kowacce daga cikinsu tana da adireshinta, wanda ya sha bamban da na sauran.  Idan a misali kana Najeriya ne, ko nahiyar Afirka, kwamfutar dake dauke da bayanan da kamfanin Google ya tanada wa ‘yan nahiyar Afirka daban take.  Da zarar ka shigar da adireshin shafin da kake so, nan take zai zarce cikin Zangon Sadarwar kamfanin Google (Google Network), yana isa, nan take za a gane daga Afirka ko Najeriya kake, ta hanyar lambar IP din kwamfuta ko wayarka.  Wannan zai sa nan take a isar dakai ga kwamfutar dake dauke da bayanan da aka tanada don ‘yan nahiyar Afirka ko Najeriya.  Wannan abu ne mai sauki, wai cire wando ta ka.

Wannan dan abin da ya samu kenan. Na gode.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.