Sakonnin Masu Karatu (2014) (2)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

51

Assalamu alaikum Allah gafarta malam.  Don Allah ayi mini bayanin matakan da zanbi don aiki da “Whatsapp a kan kwamfuta.  Allah ya kara ilmi mai albarka da takawa. – Abdulqadir Muhammad Bello

Wa alaikumus salaam Malam Abdulkadir, barka da warhaka. Wannan ai abu ne mai sauki.  Da farko sadda manhajar “Whatsapp” ta fara bayyana, babu wani tsari da za ka iya amfani da ita a kan wata na’ura idan ba wayar salula ba.  Amma daga baya, da masana harkar gina manhajar kwamfuta suka yi nazarinta, sai suka samar mata da “mazauni” da za ta iya gudanar da aiki a kan kwamfuta; ya Allah kwamfutar tafi-da-gidanka ce ko ta kan tebur.  Kamfanin da yayi wannan kuwa shi ne kamfanin “Bluetstacks,” kuma sunan masarrafar da ya kirkira shi ne: “Bluestacks App Player.”

Wannan masarrafa dai ba don manhajar “Whatsapp” kadai aka gina ta ba.  A a.  Duk wata masarrafa da ka san ba a iya gudanar da ita a kan kwamfuta sai wayar salula, to kana iya saukar da ita a kan wannan masarrafa ta “Bluestacks App Player” don gundanar da ita, cikin sauki.  Wani abin sha’awa ma shi ne, wannan masarrafa kyauta ake bayar da ita, duk da cewa kana iya biyan kudin layi na tsawon shekara don samun karin damar amfani da masarrafar idan kana so.  Wannan masarrafa na amfani da manhajar “Play Store” ko “Google Store” ne, don saukarwa da kuma samun manhajoji, kamar yadda za ka iya a wayarka mai dauke da babbar manhajar Android.  Kai, a takaice ma dai, tana bayar da damar iya amfani da masarrafan da aka gina su don babbar manhajar Android ne a kan kwamfuta mai dauke da babbar manhajar Windows ko OS X na kamfanin Apple.

Don iya amfani da manhajar “Whatsapp” a kan kwamfutarka, sai ka je shafin Bluestacks dake: www.bluestacks.com ka saukar da manhajar zuwa kwamfutarka.  Idan kaje shafin, a kasa daga bangaren hagu za ka ci kawo da tambarin “Download for Windows,” nan za ka shiga.  Idan ka gama saukar da masarrafar, sai ka loda wa kwamfutarka, wato “Install” kenan.  Akwai matakai guda biyu da take bi; a farko masarrafar za ta loda kanta kan kwamfutarka.  Daga nan kuma za a ce maka: “ka dakata” don ta lodo wasu jakunkunan bayanai masu taimaka mata aiwatar da aikin cikin sauki.  Wadannan jakunkunan bayanai tana kiransu: “Library files.”  Hakan zai dan dauki lokaci, duk kada ka damu.  Ka dai tabbata kana da “Data” isasshe a kan makalutun sadarwarka (Modem), domin masarrafar za ta koma kwamfutocin kamfanin Bluestacks ne dake Intanet, don loda wadannan jakunkunan bayanai.

- Adv -

Idan ta gama, za ta bude maka masarrafar “Play Store” irin wannan da ka sani na Android, amma ba za ka iya komai ba sai ka sa sunanka (username) da kalmar iznin shiga (password) na manhajar Imel din Gmail kenan.  Idan ba ka dashi, akwai inda za ka matsa don yin rajista nan take, babu matsala.  Matakan ba su da wahala.  Idan ka gama rajista, sai kaje wajen “Applications” ka matsa tambarin “Search” dake bangaren hagu daga sama, ka rubuta “Whatsapp” ko duk manhajar da kake son amfani da ita a kan kwamfutarka, ka matsa “Enter” a allon shigar da bayananka, nan take za a budo maka su yarbatsai, ka zabi wanda kake so, sai ka loda.

Idan ka gama loda manhajar, sai ka bude, daga nan kuma za ta bukaci kayi rajistar layinka kamar dai yadda ka san ake yi a wayar salula.


Salam, barka da yau.  Ina da wata tambaya ce. Nina kasance ina mai amfani ne da wayar hannu wajen shiga facebook. Ina ganin wasu in sun rubuta sako a shafinsu sai sunan wayar ya bayyana. Ni kuma waya ta Samsung ce, amma na kamfanin at&t. Shin, zai yiwu ni ma in na rubuta sako sunan wayar ya bayyana ga abokai na kuwa? Ka huta lafiya.  – Hashim Yusuf

Wa alaikumus salaam Malam Hashim. Wannan abu da kake gani ba na tunanin masu rubuta sakonnin ne ko kuma wayar, sai dai irin masarrafar Dandalin Facebook da suke amfani ita wajen shiga shafinsu, wanda ko dai da wannan masarrafar ne wayar tazo da ita, ko kuma saukar da masarrafar suka yi daga baya.  Akwai masarrafai (Apps) na shiga facebook (Facebook Apps) da wayoyin salula ke zuwa dasu da yawa, sannan akwai wadanda wasu suka gina suka zuba a cibiyoyin kasuwanci da wayoyin salula ke zuwa dasu, irinsu “Store” a wayoyi masu babbar manhajar “Windows Phone,” da “Play Store” ko “Google Store” ga wayoyi masu dauke da babbar manhajar “Android” da dai sauransu.  Ba wai wani abu bane da masu wayar keyi wajen shigarwa.  Misali da zan baka shi ne nau’in masarrafar shiga Dandalin Facebook da wayoyin Blackberry ke zuwa da ita.

Galibi, idan ka shiga Dandalin Facebook da ita, har kayi rubutu a shafinka (wato “Wall” kenan) nan take masarrafar za ta nuna sunanta a karkashin rubutunka, misali: “Using my Blackberry 9700.”  Wannan rubutu da kake gani, wanda ya kirkiri masarrafar ne da kanshi ya tsara mata, cewa: “A duk sadda aka yi rubutu a shafi, ki rubutua: ‘Using my Blackberry 9700’ a kasan sakon.”  Wannan, a ilimin gina manhajar kwamfuta ana kiransa “Automated message.”  Mai wayar ko ita kanta wayar salular ba su da hakkin sanya wannan rubutu sai dai masarrafar da aka yi amfani da ita wajen rubuta sakon da zuba shi a inda aka zuba shi.  Masarrafar ce ke dauke da sakon ba wayar ba.  Ita wayar kawai aikinta shi ne ta baiwa masarrafar damar aiki kamar yadda aka gina ta.  Don haka ba zan iya ce maka ga irin nau’in wayar da za kayi amfani da ita wajen yin wannan ba, domin ya danganci wace irin masarrafa ce: mai dauke da wannan tsarin ne, ko wata ce daban.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.