Asalin ‘Yan Dandatsa (Hackers) da Alakarsu da Kwayar Cutar Kwamfuta (1)

A makon da ya gabata mun fara kawo bayanai ne kan kwayoyin cutar kwamfuta da tsarin su da yadda suke yaduwa, da kuma tasirin su.  A karshe kuma sai muka kawo nau’ukan wadannan cututtuka da ke damun kwamfuta da hana ta sakewa.  A yau idan Allah Ya yarda za mu ci gaba da kwararo bayanai ne ; za mu san su waye ke da alhakin yada ire-iren wadannan kwayoyin cututtuka da kuma irin mummunan abin da suke haifarwa a duniya gaba daya.  Za mu san shahararren suna ko lakabin da aka san su dashi a duniyar fasahar sadarwa a yau, da kuma tarihin wannan sana’a tasu mai mummunan sakamako.  Idan Allah Ya bamu dama, za mu kawo bayani kan manufar wadannan mutane ; me  yasa suke wannan aiki?  

401

Computer Hacking ko Cracking

Hacking ko Cracking shi ne yin amfani da kwarewa wajen magance matsalolin kwamfuta da suka shafi dukkan sassanta, musamman bangarorin da ba kowa ke iya shigar su cikin masu amfani da wannan fasaha ba.  Har wa yau, wannan kalma ko kalmomi na iya nufin amfani da irin wannan kwarewa wajen cutar da kwamfuta a nesa ko kusa, ta hanyoyin da ba kowa ke iya ganin aukuwar su ba.  Kalmar Hacking ce ke nufin ma’anar farko.  Ita kuma Kalmar Cracking na daukan ma’ana ta biyu.  Sai dai saboda tasirin munin ma’ana ta biyu, an wayi gari Kalmar Hacking ce  ke daukan mummun ma’ana ta biyu.  Don haka a zamanin yau idan aka ce mutum Computer Hacker ne, to ana nufin yana amfani da kwarewar sa na ilimin kwamfuta wajen cutar da kwamfutocin mutane a nesa ko a kusa; ta dukkan hanyoyin da zai iya.  A takaice ka iya kiran sa dan ta’adda, ko kuma Dan Dandatsa, a cewar Farfesa Abdallah Uba Adam da ke Jami’ar Bayero a Kano.

Su Computer Hackers mutane ne masu ilimin gina manhajar kwamfuta, wato Programmers, kuma kwararru ne wajen sanin tsarin kwamfuta da yadda take aiki a dukkan lokuta.  Aikin su shi ne rubuta ma kwamfuta manhajoji ko masarrafan da take amfani dasu wajen aiwatar da ayyukan ta.  Sun san sirrin ta, da halayen ta, da dukkan abin da take so da wanda ba ta so.  Kamar yadda bayani ya gabata a sama, masu yin amfani da wannan kwarewa da iyawa nasu wajen gyaran kwamfuta da sawwake mata matsalolin da ke damun ta, su ake kira Hackers. Su kuma masu sarrafa wannan kwarewa tasu wajen cutarwa ga mutane su ake kira Crackers. Sai dai zamani tasa wannan tsari ya canza; masu mummunan halin ake kira Hackers.  A halin yanzu su ne masu rubuta ire-iren manhajoji ko bayanan da ke haddasa ma kwamfuta cututtuka masu tsananin wahalar da ita;  su rubuta manhaja ko bayanan da zasu sato musu sirrin wasu a wata duniya daban, duk ta amfani da kwarewan su na ilimin kwamfuta.  Idan suka ga dama, sai su gina manhajar kwamfuta guda, wacce zasu cillo ta cikin kwamfutar ka, ta hana ka aiki ko kuma sato musu dukkan bayanan sirrin da ka adana a cikin ta, ba tare da ka san abin da ma ke faruwa ba.

A duniyar kwamfuta irin ta yau, basu da wata kafa da zata gagare su shiga, muddin wannan kafa na damfare da wata hanyar fasahar sadarwa ce ta zamani.  Dukkan bayanan da suka gabata a makon jiya na abin da ya shafi al’adar cutar kwamfuta (Computer Virus), su ne masu rubuta su, su tsara su, su cillo su, tare da mummunar manufar su da suke kira ‘yan cin yada ilimin fasaha da hana boye shi.   Da wannan lakabi na Hackers aka fi sanin su, kuma da shi za mu ci gaba da kiran su har zuwa karshen wannan silsila da za mu yi ta kawowa insha’Allah.

- Adv -

Tarihinsu

Kamar sauran al’amura da ke faruwa a duniya, su ma suna da tarihi, wato mafarin da ta kai su ga fara wannan aiki.  Shekaru dari biyu da takwas da suka gabata, an samu wasu ‘yan ta’adda masana harkan injiniyancin lantarki da sadarwa na tarho (Electrical Engineers) da ke amfani da kwarewa ko dabararsu wajen waske injinan tarho da kamfanonin sadarwa suka kafa don sadarwa a wancan lokaci.  Wadannan mutane sun yadu a galibin biranen Turai da Amerika.  Idan dare yayi, sai su shiga cikin bukkar tarho (Telephone Booth), ba tare da ko sisin su ba, su shigar da kalmomin da suka saba ta’addancin su da su, sai tarho ta bude, su buga waya iya sa’o’in da ya musu suga.  A yayin da mutane ke sanya kwabbai na silalla don su daman buga waya, su ba ruwan su, sun san inda zasu sanya kalmomin da injin ke bukata, su waske don samun buga waya kyauta.

Da tafiya tayi nisa, aka fara kirkiran na’urar kwamfuta, sai masana ilimin kwamfuta suka ari wannan mummunan ta’ada wajen rubuta miyagun kalmomin da zasu cutar da kwamfutocin mutane ko sace musu bayanan sirrin da ke makare cikin kwamfutocin su.  Sun fara gwada wannan aiki nasu ne kan kwmfutocin asalin Intanet ta duniya, wato kwamfutocin ARPANET ; tsarin sadarwa ta Intanet na farko da aka fara kafawa, kafin yaduwar sa zuwa sauran kasashen duniya.  Amma asalin fasahar su ta samo asali ne daga makarantar da galibin masana kwamfuta suka fara a kasar Amurka, wato Massachussetts Institute of Techonology (MIT), babbar cibiyar koyar da ilimin fasaha da ke Massachussetts.  Daga nan suka ci gaba da wannan sana’a.

Daga Sha’awa zuwa Ta’addanci

Babban dalilin da ya fara motsa shaukin su ga wannan aiki shi ne sha’awan ganin sun gwada kwarewan da suka yi wajen sanayyar su ga fasahar sadarwa ta kwamfuta ; babban abin da suka koyo daga makaranta.  Dabi’ar dan Adam ce da zarar ya san wani ilimi ya ga cewa ya aikata shi a aikace, don samun natsuwa da wannan ilimi da ya koyo.  Da zarar sun gwada kwarewar su wajen sauya ma kwamfuta hankalin ta, sai su ga sun ci nasaa.  Daga nan suka fara shiga kwamfutocin makarantu don gano irin wainar da ake toyawa a cikin su.  Manufa ta fara canzawa kenan.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.