Tsarin “Cashless” Da Hanyoyin Inganta Shi a Najeriya (3)

Tsarin "Cashless" a Wasu Ƙasashen Duniya

Daga cikin manufofin tsarin “Cashless”, akwai ƙoƙarin cika burin bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa wanda a lokacin (2011) ake sa ran zai yiwu zuwa shekara ta 2020. – Jaridar AMINIYA, Jumma’a 10 ga watan Maris, 2023.

61

Tsarin “Cashless” a Wasu Ƙasashe

A galibin ƙasashen duniya yanzu bankuna sun fara sauya tsarin ta’ammali da masu hulɗa dasu.  Sun koma ƙirƙirar manhajojin da za su taimaka wa mutane ta’ammali dasu cikin sauƙi.  Wannan yasa galibin cinikayya da sayayya da aikawa da karɓan kuɗaɗe ke sauyawa a duniyar yau.

Ƙasar da tafi kowace ƙasa yawan masu amfani da katin ATM a duniya ita ce ƙasar Ireland, wacce ke maƙotaka da ƙasar Burtaniya kenan.  Daga ita sai ƙasar Finland.  Ita ce ƙasa ta biyu a duniya wajen yawan waɗanda suka mallaki taskar ajiya a banki kuma katin ATM da suke amfani dashi wajen aiwatar da sayayya ko aikawa da karɓan kuɗaɗe a tsakaninsu.  A ƙasar Finland tsarin “Cashless” yayi nisa.  Sai ƙasar Suwidin, wacce ita ma a nahiyar turai take.  Ita ce ƙasar da ake sa ran za ta gama aiwatar da tsarin “Cashless” gaba ɗaya a wannan shekara ta 2023 da muke ciki.

Cikin ƙasashen da suka rungumi tsarin “Cashless” akwai ƙasar Sin, wacce tafi kowace ƙasa yawan jama’a kuma tafi kowace ƙasa yawan masu ta’ammali da na’urori da hanyoyin sadarwa na zamani.  Adadin masu amfani da Intanet a ƙasar Sin sun ninka adadin ‘yan Najeriya sau huɗu.  A taƙaice dai, akwai mutane sama da biliyan ɗaya dake ta’ammali da Intanet a ƙasar.  Kuma galibin cinikayyarsu da saye da sayarwarsu duk ta hanyar na’urorin da hanyoyin sadarwa na zamani suke yi.  Ita ce ƙasa ta huɗu cikin jerin ƙasar da ake sa ran za su kammala tsarin “Cashless” cikin wannan shekara ta 2023 ko 2024.  Bayan katin ATM, suna amfani da tsarin NFC dake wayar salula, da tsarin da ba ya buƙatar sai ka tsofa katinka a kan na’urar POS, wato: “Contactless Payment System”.

Bayan ƙasar Sin sai maƙociyarta ƙasar Koriya ta Kudu (South Korea), wacce cikin adadin rassan bankuna 1,600 da take dasu a ƙasar, kusan rabin su duk ba sa karɓar takardar kuɗin don ajiya.  Sai dai kayi tiransfa.  A wannan ƙasa ta Koriya ta Kudu, cikin kashi 100 na al’ummarta, kashi 13 ne kaɗai ke ta’ammali da takardun kuɗi.  Ragowan na aikawa da karɓan kuɗaɗe ne ta amfani da na’urori da hanyoyin sadarwa na zamani.  Tuni tsarin “Cashless” yayi nisa a can wajensu.

- Adv -

A ƙasashen Burtaniya da Ostraliya da Kanada da Holand kuwa, sama da kashi 75 ckin 100 na adadin jama’ar ƙasashen suna amfani da na’urori da hanyoyin sadarwa na zamani ne wajen aiwatar da cinikayya da kuma aikawa da karɓan kuɗaɗe.  A ƙasar Holand ma, kashi 99 cikin 100 ne na jama’arta.  Tuni sun kusa kammala tsarin “Cashless” a ƙasar.

Manufofin Samar da Tsarin “Cashless” a Najeriya

Bankin CBN bai samar da wannan tsari na “Cashless” don yayi ko a-bi-Yarima-a-sha-kiɗa ba.  Akwai manufofin da yake son cin mawa.  Daga ciki, akwai ƙoƙarin cika burin bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa wanda a lokacin (2011) ake sa ran zai yiwu zuwa shekara ta 2020.  Wannan shi zai haifar da abin da ake kira: “Cashless Economy”.  Manufa ta biyu ita ce don ingantawa tare da sabunta tsarin hada-hadar kuɗaɗe a Najeriya, musamman ta hanyar haɗa alaƙa mai ƙarfi tsakaninsa da fannin sadarwa na zamani.  Manufa ta uku ita ce don rage adadin takardun kuɗaɗe a tsakanin jama’a, wanda hakan zai rage yawan kuɗin da bankuna ke kashewa wajen zirya da waɗannan takardun kuɗaɗe – daga bugawa, da ɗaukawa, da aikawa, da ajiyewa ko taskancewa, zuwa baiwa mutane masu buƙata.

Manufa ta hudu, aiwatar da tsarin “Cashless” zai shigar da Najeriya gaba-gaɗi cikin tsarin banki, ta yadda za su iya mallakar taskar ajiya, da amfani da hanyoyin aikawa da karɓan kuɗaɗe ta amfani da na’urori da hanyoyin sadarwa na zamani.  Manufa ta biyar, hakan zai ƙara inganta tsaro a ƙasa.  Domin yawaitan takardun kuɗi a hannun mutane na sawwaƙe wa ‘yan ta’adda hanyar samunsu ta hanyar haramun; musamman masu garkuwa da mutane.  Manufa ta shida, don inganta tsari da ka’idojin tafiyar da hada-hadar kuɗaɗe a Najeriya.  Abin da wannan ke nufi shi ne, idan mafi rinjayen kuɗaɗe na taskokin bankuna ne, aiwatar da tsare-tsaren inganta tsarin hada-hadar kuɗi zai yi sauƙi ga hukuma.  Amma idan mafi rinjayen takardun kuɗaɗe na hannun jama’a ne, ba a ckin bankuna ba, hakan zai yi wahala, kamar irin halin da ake ciki gabanin a zo rana irin ta yau kenan.  A jawabin da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari yayi ranar Alhamis, 16 ga watan Fabrairu, 2023 ya tabbatar da cewa, ya zuwa watan Oktoba na shekarar da ta gabata, cikin adadin kuɗi Naira Tiriliyon uku da biliyon ɗari uku da bankin CBN ya samar a ƙasar nan, Naira biliyan ɗari biyar ne kaɗai ke kaikomo tsakanin bankuna.  Sauran na hannun jama’a; tsakanin waɗanda suka ajiye don kasuwanci, ko don ba su da taskar ajiya a banki, ko waɗanda suka taskance a gidaje don daman kuɗaɗen na sata ne, sai waɗanda suka taskance don sayen ƙuri’a, a ɓangaren ‘yan siyasa kena.  Amma zuwa ranar da yake jawabi, yace bankin CBN ya ƙarɓi kashi 80 cikin 100 na wancan adadi dake hannun mutane.

A taƙaice dai, waɗannan kaɗan ne cikin manufofin da suka sa aka samar da wannan tsari na “Cashless” tun a shekarar 2012 da aka fara aiwatar da wannan tsari.  Kuma waɗannan manufofi har yanzu suna da alaƙa da abinda ake aiwatarwa a aikace.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.