Sakonnin Masu Karatu (2019) (1)

Bayani Kan Fasahar Sadarwa ta "Broadband"

Ga wasu daga cikin amsoshin sakonnin masu karatu na shekarar 2019. An buga wannan bayani ne a jaridar AMINIYA na watan Fabrairu. Asha karatu lafiya.

150

Assalamu alaikum Baban Sadik.  Don Allah ina son karin baynai game da na’urar sadarwa ta “Broadband”; ya take? Daga M. S. Babangida, Maraba.

 

Wa alaikumus salam Malam Babangida.  Kalmar “Broadband” dai tsari ne na aikawa da karban sakonni ta hanyar Intanet ta amfani da hanyoyi masu yawa, a lokaci daya.  Wannan shi ne tsari mafi inganci wajen aikawa da karban sakonni.  Kuma shi ne tsarin da ake amfani dashi a kusan dukkan kasashen da suka ci gaba, fiye da kowane tsari.  A ka’idar aikawa da karban sakonnin Intanet, idan ka hau wayarka ta salula ko kwamfutarka mai dauke da siginar Intanet, wayarka ko kwamfutarka za ta nemo wadannan bayanai ne daga asalin kwamfutar dake dauke dasu a ko ina take a duniya.  Da zarar wancan kwamfutar ta ingizo wa kwamfuta ko wayarka wadannan bayanai da ta nema, sai su biyo ta hanyoyin da aka tanada musu a yanayin haske, ta cikin wayoyin da aka tanada.  Daga nan sai su bayyana a shafin waya ko kwamfutarka.

Wannan titi da suke bi na dauke da tsarin aikawa da karban bayanai nau’i uku ne.  nau’in farko shi ake kira “Dial Up Connection”.  Wannan tsari ne da ya kunshi aika sakonnin shafukan Intanet a yanayin haske, ta amfani da wayar tarho.  Bayanan kan biyo wayoyi ne a matsayin haske, sai sun iso kwamfutarka sannan su harhade su bayyana a yanayinsu na asali.  Wannan tsari dai tsohon tsari ne, wanda a halin yanzu ba a cika amfani dashi ba saboda matsalolin da yake dauke dasu.  Matsalar farko ita ce: bayanan ba su isowa da wuri, domin titin da suke bi (wayar tarho kenan) ba a yi a asali don aika rubutattun sakonni ko hotuna ko bidiyo ba; an yi wayoyin ne don aika sakon sauti kadai, wato murya kenan.  Shi yasa da zarar sakonnin sun kamo hanya, sai sun dade kafin su iso.  Don dole a sarrafa su zuwa yanayin haske, daga nan a tunkudo su, idan sun iso kuma a sake sarrafa su a yanayin da suke na asali.  Matsala ta biyu kuma ita ce: titin da aka tanada don tunkudo sakonnin dai titi ne guda daya tal.  Da rubutu, da sauti, da bidiyo, da hotuna; duk ta hanya daya suke bi.  Wannan yasa tsarin ke dauke da nawa matuka.

- Adv -

Tsari na biyu da ake amfani dashi wajen aikawa da karban sakonni ta Intanet a tsakanin kayayyakin sadarwa shi ne tsarin: “Digital Subscriber Line” ko “DSL” a gajarce.  Wannan tsarin ya fi na farko inganci.  Domin yana amfani ne da hanya fiye da daya, amma wanda aka tanada don aika sakonnin talabijin.  Wato hoto mai motsi kenan da mara motsi, da rubutu.  Wannan tsarin yayi fice a kasashen da suka ci gaba matuka.  Domin gidajen talabijin masu yada shirye-shirye ta tauraron dana dam (Satellite TV Channels) ne suka yi amfani dashi wajen sada mutane da intanet.  Har wa yau akwai tsarin “Base Band”, wanda shi kuma kamfanonin sadarwa na wayar salula ke amfani dashi wajen sada masu layukansu da Intanet a ko ina suke.  Duk da cewa tsarin DSL bai shahara a Najeriya da sauran kasashen Afirka ba, amma tsarin “Base Band” ya shahara, musamman ganin cewa ba a samu yawaitar masu amfani da Intanet a wadannan kasashe ba sai da aka samu bunkasar tsarin sadarwar wayar salula.  Wannan tsari yafi na baya sauri wajen isar da sakonni, saboda amfani da hanya fiye da daya wajen aika sakonnin.  Kari a kan haka, yanayin titin ko tashar (Band) ya dace da yanayin sakonnin da ake aikawa, sabanin wancan titi ko tasha ta farko da aka tanade ta kawai don murya ko sauti.

Sai tsari na uku wanda shi ne ake yayi yanzu.  Wannan tsari shi ne tsarin da kake tambaya a kai, wato: “Broadband”.  Abin da Kalmar take nufi a zahirin fassara shi ne: “Tasha mai fadi, mai yalwa.”  Abin da wannan ke nufi kuwa shi ne, a tsarin “Broadband”, sakonnin da ake aikawa dasu ta wayar sadarwa, suna isowa ne ta hanyoyi masu yawa, masu fadi.  Misali, a tsarin “Broadband” kana iya sauke bayanin da mizaninsa yakai tiriliyon daya (1 Gigabyte) a tazarar lokacin da bai shige minti biyar ba!  Amma idan a tsarin “Dial-up”ne, kana iya daukan kusan awa guda baka sauke ba.  A tsarin “Base Band” kuwa ta yiwu ya dauke ka minti talatin zuwa arba’in da biyar.  Wannan muna kaddara cewa yanayin sadarwar ba matsala kenan a inda kake.

A takaice dai, tsarin “Broadband” tsari ne na aikawa da sakonnin Intanet ta amfani da tashoshin aika sakonni masu yawa, a lokaci daya, ta titi daya.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.