Sakonnin Masu Karatu (2019) (18)

Tsarin Sayen Wayar Salula

Ci gaban sakonnin masu karatu da na samu a wannan shekara. An buga wannan bayani ne a jaridar AMINIYA na ranar Jumma’a, 1 ga watan Nuwamba, 2019.

76

Assalamu alaikum Baban Sadik?  Muna maka godiya da wannan namijin kokari da kakeyi ga al’ummar kasar nan ta hanyar wayar da kanmu akan kimiyya da kere-kere.  Ni dai ban taba rike babbar waya ba, to wace shawara za ka bani?  Da irin wacce zan fara idan na tashi saya?  Ashiru Manyan gobe Mashi, Katsina: 09051512524

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Ashiru.  Sayan wayar salula yana rataye ne da abubuwa da dama.  Abu na farko shi ne yanayin hali na kuxi.  Nawa kayi niyyar kashewa wajen sayan waya, yana da alaka ne da irin wayar da za ka iya saya.  Sannan yanayinka.  Akwai wadanda masu kuxi ne, amma basa son rike babbar waya.  Ko dai saboda tsoron munana zato gare su daga jama’a, musamman barayi.  Ko kuma tsoron baza su iya yin tattalinta ba. Ta yiwu abubuwa na saurin kubucewa daga hannayensu, ko kuma suna aiki ne a wajen dake dauke da hadari ga na’urori irin wayar salaula.  Wannan ke sa kaga sun rike karamar waya, ba don baza su iya sayan babbar waya ba.  Bayan haka, ya danganci wayewar mutum.  Wasu suna da kuxin kuma suna son sayan waya, amma basu waye ba – wataqila ba sa jin turanci.  Wannan zai sa su takaitu da karamar waya. Saboda sayan babbar waya wajensu hasarar kuxi ne.  Sannan a qarshe, ya danganci me kake son yi da babbar waya.  Idan bukatarka bata wuce aiwatar da kira da karban kira ba, sayan babbar waya hasarar kuxi ne.  Amma idan akwai abubuwa da yawa da kake son yi, wadanda sai babbar waya kadai ta mallakesu ko take iya aiwatar dasu cikin sauki da sauri, a nan za a iya cewa ka sayi babbar waya.

Don haka, bazan iya ce maka ga irin wayar da zaka saya ba kai tsaye.  Kada ya zama waya ce mai tsada, alhali kai kuma ba ka da kuxin da zaka iya mallakarta.  Da ace ka min bayanin yanayinka da iya kimar kuxin da za ka iya sadaukarwa don sayan wayar, sai in baka shawarar irin wacce zaka saya.  Don haka, ka dai samu waya mai iya hawa intanet cikin sauki, mai dauke da babbar ma’adana, mai saurin budo shafuka kuma mai daukan caji na tsawon lokaci.  Ina maka fatan alheri da dacewa da wayar da ta dace da kai.  Na gode.

Assalamu alaikum Baban Sadik, gaisuwa mai yawa tare da fatan alkairi.  Ina da waya kirar Tecno K7, in ina aiki da ita sai kawai ta cije ta tsaya, har sai batir ya dauke. Ko meye matsalar?  Daga Faisal Usman Binkola, Mayo Belwa L.G.A., Adamawa.

- Adv -

Wa alaikumus salam, barka ka dai Malam Faisal.  Wannan alama ce dake nuna cewa wayar tana da matsala babba, ba karama ba.  Ko dai ta kamu da cuta (Virus) ne dake addabarta, ko kuma tana fama da karancin ma’adana.  Ita wayar salula kamar xan adam take; tana bukatar da sarari don numfasawa, da ma’adana isasshe don adana abubuwan da ake zuba mata, da kuma wata ma’adana ta wucin-gadi da ake kira: “RAM” – wato “Random Access Memory”.  Wannan ma’adana ta wucin-gadi ce ke daukan dukkan bayanan manhajojin da kake buxewa a wayarka, don samun damar ta’ammali dasu cikin sauki.  Idan misali ka budo manhajar karba da aika SAKOnni, wato: “Message”, kana latsawa, wayar za ta dauko bayanan manhajar daga ma’adanar wayar, wato “Internal Memory” zuwa wannan ma’adana.  Da zarar ka gama amfani da manhajar, sai wayar ta mayar dasu inda ta debo su.

Wannan ma’adana ta RAM tana zuwa ne mizani mizani.  Ba iri daya yake a kowace waya ba.  Manyan wayoyi masu tsada sun fi zuwa da RAM mai babban mizani, saboda samuwar tarin manhajoji da wayar ka iya zuwa dasu, ko damar saukar da bayanai masu yawa, saboda girman babbar ma’adanarta.  Idan aka yi rashin sa’a mizanin RAM din wayarka karami ne, kuma ka tara manhajoji masu yawa a kan wayar, sannan kana budo manhaja sama da daya ko biyu a lokaci daya don amfani dasu ba tare da ka rufe ta farko ba, wayar za ta shake, ta kasa numfasawa, saboda karancin ma’adanar RAM din.  Wannan ma daya ne daga cikin dalilan da ke sa waya ta zama haka.

Bayan nan, haka idan wayar tsohuwar waya ce mai dauke da tsofaffin manhajoji kuma ba a sabunta mata bayanan babbar manhajarta, wato “Update”, to, haka na iya faruwa da ita.  Don haka, hanya mafi sauki shi ne ka kai wajen masu gyara nagartattu don su duba maka ita.  Domin bai kamata waya ta rika dogon suma irin wannan ba.  Wannan shi ake kira: “Hanging”.

Wannan shi ne dan abin da zan iya cewa, tunda ba ganin wayar nayi ba kuma ba cikakken bayani kayi kan nau’inta da yanayin sabunta ko tsufanta ba.  Allah sa a dace, amin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.