Ma’ana da Nau’ukan Makamin Nukiliya

Daga cikin abin da kasashen duniya ke rige-rige wajen mallaka akwai makamin nukiliya. Daga wannan mako za mu fara gudanar da bincike don kosar da masu karatu kan wannan makami, a kimiyyance. Wannan shi ne kashi na daya.

534

Gabatarwa

Cecekuce da ake ta yi kan kasashe irin su Koriya ta Arewa da kasar Iran ko Farisa a yau ya samo asali ne daga shirinsu na mallakar wani makamin tsare kasa da ake kira makamin nukiliya, ko kuma nuclear weapon, a harshen Turanci.  Wadannan kasashe, kamar sauran kasashe ‘yan uwansu, na da hakkin kare kasashensu da duk irin makamin da suka ga ya dace, musamman dangane da irin tsarin da duniya ke gudanuwa a kai a yau ; na yaudara da gilli da kinibibi da munafunci.  To amma saboda wasu tsare-tsare da ake ganin sun zama dole a yi, wai don duniya ta samu zama lafiya, ta fita daga halin zaman dardar da ta shiga lokacin yakin cacan-baki (cold war), ake ganin ya zama dole kowace kasa ta rattafa hannu kan yarjejeniyar hana yaduwar mallaka da kuma amfani da wannan makami mai suna makamin nukiliya.  Wai shin, me ke kunshe cikin wannan makami ne da har ake kokarin hana wasu mallakarsa?  Ya sha bamban ne da sauran makamai ta wajen barna, ko kuwa?  In haka ne, to me yasa wasu suka mallaka wasu kuma aka hana su mallaka?  Me yasa wasu suka bata nasu?  Kasashe nawa suka mallaki wannan makami?  Yaya tasirin wannan makami yake wajen murkushe rayuwa da lafiyar dan Adam da muhallinsa?  Wadannan, da ma sauran tambayoyin da masu karatu zasu karanta nan gaba, na kumshe cikin wannan silsila da za mu fara a yau in Allah ya yarda.  Da farko dai, ga ma’ana da nau’ukansa da kuma yadda aka yi wannan makami ya samo asali a duniya:

Ma’ana da Nau’ukan Makamin Nukiliya

Makamin Nukiliya, ko Nuclear Weapon a turance, wani irin makami ne mai karfi da saurin fashewa sanadiyyar wasu sinadaran kimiyya masu tarwatsewa ko harhadewa da junansu don haifar da makamashin madda (atomic energy) a yanayin hayaki ko haske mai dauke da tururin guba ga lafiya ko rayuwar dan Adam da muhallinsa.  Idan makamin nukiliya ya fashe a wuri  ko gari misali, dole a samu karar fashewa mai tsananin firgitarwa, wacce ke biye da hayaki mai guba ga dan Adam ko wasu halittu, tare da wuta mai ci balbal, a karshe kuma, akwai tururin haske mai cutarwa idan ya hadu da maddar muhalli.  Wannan tururin haske mai cutarwa da a ilimin kimiyya ake kira radioactive radiation, mai cikakken hadari ne ga fatar jiki da lafiya ko ran dan Adam, kuma yana iya kasancewa a dukkan ilahirin wurin da aka samu wannan fashewa na tsawon shekaru.  Da kasar wurin, da iskar wurin duk zasu gurbata.  Idan mizanin wannan makami ya kai tan miliyan a misali, karfin fashewarsa na iya haddasa ‘yar karamar girgizar kasa a ‘yan takaitattun taku daga wurin da fashewar ta auku.

- Adv -

Manyan sinadaran kimiyyar da ake amfani dasu wajen kera wannan makami a duniya su ne makamashin fulutoniyon (plutonium) da kuma yuraniyon (uranium).  Ana dafa su ne har su kai wani mizani na zafi wanda ke canza hakikaninsu zuwa wasu maddodin dabam, ya kuma basu tasirin fashewa ko hadewa da juna, sanadiyyar alakarsu ko kusancinsu da wasu makamashin haske ko maddodin dabam.  Saboda tsananin tasirinsa ga muhalli, tan guda na makamashin nukiliya da ke dauke cikin makami ko kwansonsa, idan aka harba shi, tasirin fashewa da kara da yawan sinadaran da zai fitar, daidai yake da tasirin fasa bam irin na zamani guda biliyan daya, a lokaci daya, kuma a wuri daya.  Idan kuma aka samu fashewar makamin nukiliya da mizaninsa ya kai tan dubu ko sama da haka, to yana iya Konawa da kuma tarwatsa birni mafi girma a duniyar yau.  Sanadiyyar wannan gamammiyar tasiri da wannan makami ya mallaka tasa ake masa lakabi da makamin kare-dangi, ko kuma weapon of mass destruction, a harshen Turanci.

A tarihin duniya sau biyu kadai aka taba amfani da wannan makami don kai hari tsakanin wata kasa da wata kasa.  Hakan ya faru ne lokacin yakin duniya na biyu, lokacin da kasar Amurka ta jefa wa kasar Jafan wani makaminta na nukilya mai dauke da nau’in makamashin yuraniyon, mai suna Little Boy”, a babban birnin kasar Jafan na wancan lokaci, wato birnin HiroshimaWannan ya faru ne ranar 6 ga watan Agusta, shekarar 1945.  Kwanaki uku da jefa wannan makami, sai Amurka ta sake dosan birni na biyu a girma, wato birnin Nagasaki, ta ajiye wa mutanen birnin wani makamin nukiliyanta mai dauke da makamashin fulutoniyon, mai suna “Fat Man”.  Wannan ya haddasa mutuwar mutane sama da dubu dari da ashirin nan take, tare da mutuwar wasu dubunnai akai-akai, sanadiyyar tururin haske mai dauke da guba da ke yawo a muhalli da sararin samaniyan biranen biyu.  Kawo yanzu, akwai kasashe a kalla takwas, wadanda aka tabbatar da suna da wannan makami na nukiliya a duniya, sanadiyyar gwaji da suka yi kowa ya gani don tabbaci.  Wadannan kasashe kuwa sune: Amurka, da Rasha, da Burtaniya, da Faransa, da Sin, da Indiya, da Pakistan, da kuma Koriya ta Arewa.

A yanzu akwai nau’ukan makamin nukiliya iri biyu, shahararru, wadanda dukkan  wasu nau’uka suka dogara dasu.  Nau’i na farko shi ne nau’in da ke dauke da makamashin madda mai karfi, masu tarwatsa juna ta hanyar warwatsuwar da suke yi yayin da aka harba su ta hanyar makamin da suke dauke cikinsa.  Akan jejjera wadannan makamai masu gaggawar tarwatsewa ne waje daya, cikin kwanso ko makami guda kenan, sannan a harba su zuwa inda ake hari.  Wannan tsari tsohon yayi kenan, kuma shi ake kira the gun method, domin akan harba makamin ne kamar yadda ake harba harsashi da ke cikin bindiga.  Ko kuma, a daya bangaren, a jera makamai masu dauke da makamashin fulutoniyon a wuri daya, cikin kwanso daya, da zarar an harba su, sai su harhade da juna, sannan su fashe.  Wannan tsari shi ake kira the implosion method.  Kuma su suka kunshi nau’in farko na makamin nukiliya mai suna Atomic Bomb, ko kuma A-Bomb a takaice.  Irin wannan nau’in ne kasar Amurka ta ajiye wa mutanen Jafan a manyan biranensu, lokacin yakin duniya na biyu, kamar yadda bayanai suka gabata a sama.

Sai nau’i na biyu kuma, wanda ke haifar da makamashin guba mai dimbin yawa sanadiyyar hadewar sinadaran madda masu tarwatsewa irin wanda ke dauke cikin nau’in farko, da kuma wasu sinadaran madda masu hadewa kafin su tarwatse.  Yadda ake kera wannan nau’in shi ne, za a shigar da sinadaran madda masu tarwatsewa cikin ma’adana daya mai dauke da makamashin tururin haske, a gefensu kuma a jejjera sinadaran makamashi masu gamewa da juna lokacin fashewarsu (irin su tritium da kuma deuterium, ko kuma lithium denteride), duk cikin kwanso ko ma’adana guda.  Da zarar an jefa wannan makami a wurin da ake hari, sai wadancan sinadarai masu saurin tarwatsewa su tarwatse cikin ma’adanar. Tarwatsewarsu ke haifar da haske mai tsanani nau’in Gamma-ray da kuma X-ray, nan take sai wannan haske ya narka sinadaran lithium denteride, ya tafasa su matukar tafasawa.  Suna gama tafasuwa sai kawai su haifar da sinadarai nau’in neutron, masu gamewa da makamashin yuraniyon don haddasa fashewa da kara mai tsanani.  Wannan nau’i kuma shi ake kira Hydrogen Bomb, ko H-Bomb, ko Fusion Bomb, ko kuma Thermonuclear Bomb, a turance.  Kuma shi ne har wa yau Hausawa ke kira “makami mai guba”!

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.